Thursday, December 20, 2018

TARIHIN HAUSA


Tarihin Hausa: Daura, Rijiyar
Kusugu Da Labarin Bayajidda
Tarihin Hausa ya nuna cewa sama da
shekaru 2000 da suka wuce, al’ummar
Hausawa na zanne a tsakiyar kasashen
bakaken fata wanda ya kasance a Arewacin
Najeriya da wani sashen Nijar a yanzu.
Daura na daya daga cikin manya manyan
kasashen Hausa a lokacin. Tana da mata a
matsayin Sarauniya, Wadanda suke mulki a
wancan lokaci.
A lokacin Sarauniya Daurama, akwai wata
rijiya mai suna Kusugu, wadda itace babbar
rijiya dake ba garin Daura ruwa a wancan
lokacin. Amma mutane basu samun bar
ruwan saboda akwai wata Macijiya a cikin
rijiyar.
Haka mutanen garin suka cigaba da zama
har shaida wata rana wani mutum wanda
ake tsammanin Dan Sarkin Bagadaza, Abu
Yazid ya zo Daura bayan da ya kasa samun
Sarki bayan mutuwar baban shi.
Jarumin Dan Sarkin bayan daya sauka gidan
wata tsohuwa mai suna Ayyana, sai ya
bukaci a bashi ruwa ya sha. Ruwan da aka
bashi bai ishe shi ba, shi da mutanen shi. Sai
ya roki tsohuwar data nuna mashi inda rijiyar
garin take domin ya ibo ruwan. Tsohuwar sai
ta gargade shi akan Macijiyar amma bai ji
ba. Bayan da yaje ibo ruwan sai sukayi
artabu da Macijiyar inda ya kashe ta.
Ganin haka ya sanya Sarauniyar ta aure shi
inda ya zama Sarki. Saboda baya jin Hausa
ada ne ya sanya mutane ke ce mashi
Bayajidda. Watau, Bayajjida.
Ya haifi yara bakwai wadanda sune sukayi
mulkin kasashen Hausa guda bakwai.
Shugaban kasar Najeriya mai ci,
Muhammadu Buhari dan asalin Daura ne,
kuma yana da gida a can. Kuma yana da
sarautar Bayajidda Na Biyu a masarutar
Daura.
Allah yasa mU dace

No comments:

Post a Comment