Friday, December 21, 2018

TARIHIN SHEHU SHAGARI

TARIHIN ALH SHEHU SHAGARI
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
An haifi Alh Shehu Usman Shagari a shekarar 1925 cikin kauyen Shagari garin da kakan-kakansa Ahmadu Rufai ya kafa. Sunan mahaifinsa Aliyu, mahaifiyarsa kuwa sunanta Maryamu.
Mahaifin Shehu Shagari ke rike da mukamin Magajin Shagari, watau kamar dagacin kauyen kenan, sai dai Allah yayi masa rasuwa shekaru kafin a haifi Shehu Shagari, wanda hakan yasa ɗan uwansa Bello yaci gaba da zamowa magajin shagari.
Shagari yayi karatun alkurani a gida, sannan ya fara fita waje neman ilimin zamani. A shekarar 1931 zuwa ta 1935 ya kammala karatun elementarensa a Yabo. Sannan ya tafi midil dake sokoto a shekarar 1936 ya kammala a shekarar 1940, daga nan sai ya tafi kwalejin kaduna yayi karatunsa daga shekarar 1941 zuwa shekara ta 1944.
Bayan ya kammala kwalejin kaduna sai kuma ya samu gurbin karatu a kwalejin horas da malamai ta zaria inda ya kammala a shekarar 1952 tare da zamowa malami jihar sa ta Sokoto.
Shehu Shagari ya soma siyasa ne da zamowa akawun jamiyyar NPC, Northern Progressive Party reshen jihar sa ta Sokoto a shekarar 1951 sai kuma a shekarar 1954 aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yammacin sokoto.
A shekarar 1958, Shagari ya zamo akawun majalisar tarayya, amma a shekarar 1959 sai ya barwa Tafawa Balewa wannan gurbi saboda martabawa. A wannan shekarar kuwa sai aka naɗa shi ministan tarayya mai kula da kasuwanci da masana'antu.
Shagari ya rinka samun sauye sauyen hukumomi a matsayin sa na minista tun da aka karɓi yancin kai a shekarar 1960 har lokacin da akayi juyin mulki a shekarar 1966, haka kuma bayan Janar Yakubu Gawon ya zama shugaban kasa, an sake baiwa Shehu Shagari mukamin ministan kasa a shekarar 1970
Baya da haka, a shekarar 1971-75 a lokacin yakin basasar kasa, Shehu Shagari ya zama ministan kuɗin Nigeria, wannan kujera ce ta bashi damar ya rike mukamin gwamna na bankin duniya, ya kuma zama ɗaya daga cikin mutane ashirin 'yan kwamitin bankin lamuni na duniya watau IMF.
Shehu Shagari na daga cikin waɗanda suka kafa jamiyyar 'National People’s Party' a shekarar 1978 bayan an kashe Janar Murtala, a lokacin da shugaban kasa na lokacin Janar Obasanjo Olusegun ya bada izinin kafa jamiyyun siyasa don mikawa farar hula mulkin kasa. Haka kuma a shekarar 1979 Shagari ya zama ɗan takarar shugaban kasa a tutar jamiyyar tasu, kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana shi a matsayin wanda ya cinye zaɓe a wannan shekara.
Shehu Shagari yayi shekaru huɗu yana mulkar Nigeria, sannan ya sake neman takara kuma yaci a shekarar 1983, to amma jim kaɗan da zaɓen, sai sojoji sukayi masa juyin mulki a ranar 31 ga watan disambar 1983, a lokacin da aka naɗa Shugaba Muhammadu Buhari shugaban kasa Nigeria kenan da kakin soja.
Hakika za'a jima ana tunawa da Shehu Shagari a matsayinsa na Shugaban kasar Nigeria duba da kokarin sa wajen haɓaka samar da Man fetur, da inganta masana'antu, da samar da Injinan aikin gona a shirin sa na 'Green Revolution', da gina tituna da suka sadar da manyan jihohi don inganta zirga zirga gami da samar da gidaje masu saukin kuɗi a birane da karkarar Nigeria.
Da rarar kuɗin man fetur Shagari ya kammala ginin matatar man fetur ta Kaduna a shekarar, sannan ya kammala ma'aikatun sarrafa karafuna na Ajaokuta da wani irinsa a Delta a shekarar 1982.
A shekarar 1983, Shagari ya samar da kamfanin sarrafa Alminiyon a Ikot Abasi duk kuwa da talaucin da kasar ke ciki saboda karyewar farashin mai a shekarar 1981.
A lokacin sai ya maida kasar izuwa dogaro da noma ta hanyar bada taki da iri mai kyau kyauta ga manoma, sanna ya rage kuɗaɗen da gwamnatinsa ke kashewa tare da kara samar da kuɗaɗen shiga daga jamian hana fasa kwauri na kasa watau Custom.
Sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shagari sun zargi gwamnatinsa da rashawa gami da maguɗi a zaɓen 1983. Sannan sunyiwa 'yan kasa alkawarin fitar dasu kangin talaucin da suka shiga biyo bayan karyewar farashin mai a kasuwar duniya
Shehu Shagari yayi rayuwa mai kyau a iya shekarunsa cassa'in da biyu da haiuwa, ya janye jikinsa daga mafi akasarin lamurorin gwamnati dana siyasa don tsira da mutumcinsa, sannan ya auri mataye uku, sune Amina, Aishatu, Hadiza, Allah kuma ya albarkace shi da 'ya'yaye da dama, acikin su akwai Captain Muhammad Bala Shagari Rtd. da Aminu Shehu Shagari.
Shine Alhaji Shehu Shagari, tsohon shugaban Nigeria, Tsohon ɗan siyasa, turakin sokoto, Ochiebuzo of Ogbaland, the Ezediale of Aboucha, the Baba Korede of Ado Ekiti, sannan kuma mai lambar girma ta Grand commander a tarayyar Nigeria watau GCFR.
Dafatan Allah ya inganta lafiya, yasa kuma agama lafiya Amin.

No comments:

Post a Comment