Saturday, December 8, 2018

TARIHIN ANNABI YUSUF A.S

TAKAITACCEN TARIHIN ANNABI YUSIF (a.s)
*****ALLAH YA JARRABA ANNABI
YA'AKUB A.S*****
=========================
=========================
=========================
Bayan Rahilu (mahaifiyar Annabi
Yusif) ta haife shi, sai Annabi
Ya'akub ya karbe shi ya mai da
rainonsa a hannun babbar yarsu
ya'yan Ishak A.S. To dama akwai
dan Annabi Ishak wanda ta gada
saboda babban da shi ne yake
gadonsa a al'adarsu. Bayan Annabi
Yusif ya dan tashi a wajenta sai
Annabi Ya'akub ya nemi ya karbe
shi. To ta kasance tana matukar son
Annabi Yusif. Don haka sai tace ba
za ta iya rabuwa da shi ba. Sai shi
ma Annabi Ya'akub AS yace ai kuwa
shi ma ba zai iya barin mata shi ba.
Don haka sai ta lallabe shi a kan ya
yi hakuri nan da dan wani lokaci za
ta ba shi shi. Sai ya yarda ya tafi ya
bar mata shi. Sai ta kira Yusif ta
shigar da shi dakin ta. Sai ta sa
masa wannan a karkashin kayansa.
Bayan ya fita yana wasa a cikin
yara sai ta tura a nemo mata a
tsakanin yara. Ana dubawa kuwa
sai aka sameta a wajen Yusif. To
dama a shari'ar wadannan
mutunen duk wanda aka kama
yayi sata, to ya zama bawan wanda
yayiwa satar don haka sai ta rike
Yusif. Annabi Ya'akub bai sami
damar daukar Annabi Yusif ba har
sai bayan rasuwarta. Don haka ne
ma a lokacin da aka samu kwanon
awon sarkin Misra a kayan
Binyaminu sai yan'uwansa suka ce
idan ma yayi sata, ta ai dama
dan'uwansa ma ya taba yin sata,
kamar yadda Allah (S W T) ya ba
mu labarin a cikin Alkur'ani a
Suratu Yusif:77.

No comments:

Post a Comment