Friday, December 21, 2018

ZUWAN TURAWA 5

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.

Kashi na Biyar

Sadiq Tukur Gwarzo

Amma dangane da Sarkin Kano Ali ɗan Abdullahi (maje karofi) Alfallati, munji cewar a zamanin da yake mulkinsa, sai watarana wani manzo yazo masa wanda ake kira Baban Kano.
Wannan Manzo ya zone daga Lokoja, a haɓnunsa kuma akwai wasika daga wani Attajiri Ba'agale mai hurɗa da turawa, mai suna Adamu Jakada.
Koda manzo yazo fada, sai akai masa iso ga sarki ya shiga gareshi ana fadanci, yayi gaisuwa tare da mika masa wannan wasika dake tare dashi.
Nan take sarki ya karɓi wasikar, ya shiga karantawa a zuci ba a bayyane ba.
Ance ga abinda ke cikin rubutun:
Daga Adamu Jakadan Kiristoci. Aminci ga sarkin kano Ali ɗan Abdullahi.
Bayan gaisuwa, wannan manzo Baba Kano na aiko shine domin ya shaida maka da baki cewar Turawa na zuwa gareka.
Hakika, kayi sanin cewa babu makawa sai sunzo. Babu kuma abinda zai tunkuɗe zuwan nasu. Don haka sai kayi taka tsan-tsan, ka kuma lura da sha'anoninka.
Idan kanaganin ba zaka iya yakar suba, to zaifi kyau ka mika wuya a garesu. Kayi musu kyawawan zantuka, gami da kyaututtuka, ni kuma nasan da sannu zaka tsira daga garesu dakai da mutanenka.
Ina mai maka nasiha a bisa haka, don Allah indai ka aminta da nasihata to godiya ga Allah domin babu abinda zai faru.
Amma idan baka ɗauketaba, to ina kara jan hankalinka abisa abinda zai auku mummuna.

Koda sarki Ali ya kammala karantawa, sai bai cewa fadawansa komi ba, amma ya mayarda martani da baki ga Baba kano, yana maicewa
"Kayi sani yakai Baba Kano, bazan mika wuya ga kiristoci ba, ba kuma zan nemi tsira daga wurin suba.
A maimakon haka, zan yakesu matsawar suka zo kasata."
Ya faɗi haka a gaban fadawansa, amma fa a zuciyarsa ba haka abin yake ba domin ya tsorata har ma yayi shirin tserewa.
Daga wannan rana ne kuwa ya soma shirin tafiya sokoto domin neman mafaka.
To kuma bayan lokacin tashi yayi ga Sarki Ali har ma ya fita daga garinsa, ya riski sokoto, kwanaki kaɗan yayi a garin sai ya baroshi da niyyar komowa Kano.
Koda suka riski kasar zamfara, suka shiga wani gari mai suna Gidan Goga (Ko Birnin Goga) sai suka sauka anan da niyyar hutawa. Aka baiwa sarki Ali wani gida ya shige.
Ance Sarki Ali yana zaune a kofar ɗaki sai kwatsam yaga matarsa mai suna kubura ta shigo gidan a fusace tare da jama'arta.
Koda sarki ya kaleta ya ganeta, sai yace mata "yake kubura, menene damuwarki?"
Sai kubura tace "Ya kai wannan sarki, kiristoci sun shiga turakar ka, sun kuma karɓe iko da birninka, sun ruguza daular ka."
Sarki Ali yace "Babu sarki sai Allah, yaushe haka ta faru?"
Kubura ta amsa masa da cewa "kwanaki talatin kenan bayan barowarka birni."
Sarki Ali yayi jim cikin takaici sannan yace mata "yanzu menene abinyi?"
Kubura tace "masa idan dai kana son tsira, dole ka gudu. Komawa kano ba naka bane. Domin bayan fitowar mu daga kano, munji ance suma sun fito nemanka.
Don haka tun barowar mu kano muke ta azama ba dare ba rana domin mu riskeka mu sanar maka da wannan labari. Kayi sani, wanda duk ya tsere, to ya kuɓuta."
Da sarki Ali yaji wannan jawabi nata, sai kuma ya nemi shawararta game da tserewar. Ta kuwa ce masa lallai ya tsere a wannan dare domin hakan shine kaɗai mafita.
Ai kuwa da tsakar dare Sarki Ali tare da iyalinsa da wasu zaɓaɓɓu a tawagarsa suka tsere suka nufi kusurwar birnin Gobir.
Koda gari ya waye, sai ragowar mutanen sa suka nemeshi sama ko kasa basu ganshiba, sai daga baya suka gane cewa da dare ya tsere.
Da aka sanar da ɗan uwansa kuma mai taimaka masa Waziri Amadu cewar Yayansa ya tsere, sai yace ina hujjar haka? Sai aka ce masa ai jiya kubura matarsa ta riskeshi da yammaci.
Waziri Amadu yace "daga Allah muke, kuma gareshi zamu koma, lallai wannan mutum ya ja mana abin kunya, yanzu ina ya shiga, kuma menene dalilin gudunsa?"
Daga nan sai waziri Amadu ya tara sauran mutane ya sanar musu da abinda ɗan uwansa yayi. Dajin haka Sai kuwa sukace yanzu suna karkashin sane, don haka sai ya jagorancesu izuwa duk inda yaso.
Waziri Amadu kuwa sai yace to indai haka ne, kowa yahau dokinsa mu nufi kano (domin bashi da labarin turawa)
Kunji yadda ta faru har waziri Amadu da tawagarsa sukayi kichiɓus da turawa a dajin Rubin, wanda akace yana nan kusa da garin kwatarkwashi ta kasar zamfara, inda har kuma waziri Amadun ya rasa ransa a fafatawar, yayinda kaninsa ya tsere da wasu mutanen, yaje ya mika wuya ga turawa dake kano daga baya kuma suka naɗa shi sarkin kano.
Ance a yammacin wata ranar jumua aka naɗa sarki Abbas (maje Nasarawa) sarkin kano. Kuma sai da kanawa suka shafe sati guda cur suna kaɗe-kaɗen tambura da ganguna da wasanni don murna.
Daga bisani Gwamna Lugga ya aika suje Dungurum ta zungeru don su haɗu dashi.
Ai kuwa haka sarki Abbas yayi hawa da tawagarsa ya tafi Zungeru.
Gwamna Lugga kuwa ya tarbeshi, yayi masa godiya gami da kara masa matsayi. Daga bisani Sarki Abbas ya komo kano lafiyaaaa.
Anan labarin Abdullahi Alghadamasi yazo karshe.
Sai dai daga bisani, an jiyo cewar watanni huɗu zuwa biyar da tserewar Sarki Alu, sai turawan faransa suka kameshi, suka kuma mika shi ga turawan Burtaniya dake nemansa. Kuma a hannunsu ya rasu yana tsare a garin Lokoja.

No comments:

Post a Comment