Friday, December 7, 2018

KUNAN WUTA



KO KASAN WARKEWAR FATA BA SHI NE WARKEWAR ƘUNA KAWAI BA?
kunar wuta ciwo ne da ke raunata fata da sauran abubuwan da fata ta rufe sakamakon ƙuna daga zazzafan ruwa ko mai, wutar makamashi, lantarki da sauran sinadaran da ka iya ƙona jiki.
Waɗanda suke da haɗarin gamuwa da ƙunar wuta sun haɗa da:
1) Ƙananan yara, musamman ‘yan ƙasa da shekaru biyar.
2) Tsofaffi ko waɗanda shekarunsu suka miƙa.
3) Marassa kiyaye ƙa’idojin hulɗa da wuta.
4) Da kuma wanda azal ta faɗawa.
A duk lokacin da mutum ya ƙone kafin zuwa asibiti ana buƙatar:
1) A ɗauke mutum daga wurin wutar.
2) A Kashe wutar.
3) A cire tufafin da ya ƙone a jikin mutum.
4) A zuba tsabtataccen ruwa a ƙunar.
5) A rufe ƙunar da tsabtatacciyar tufa.
6) Sannan a garzaya da wanda ya ƙone zuwa asibiti.
Don haka a guji sa ƙanƙara, man-shafawa, man-shanu da sauran mayuka a wurin ƙuna, amma ana iya amfani da man-kifi ko man-kaɗanya musamman domin lausasa fatar da ta fara warkewa.
Idan ƙuna ta shafi gaɓoɓin jiki, ƙagewa ko maƙalewar gaɓɓai yana daga cikin matsalolin da ke biyo bayan ƙuna musamman in ba’a samu kulawar likitocin Fisiyo (Physiotherapists) ba tun da farko ba. Domin waɗannan likitoci su ke da ƙwarewar kula da lafiyar gaɓoɓi a yayin warkewar ƙuna domin su tabbatar kowacce gaɓa tana lanƙwashewa ta miƙe, sannan tai aikinta yadda ya kamata don magance ƙagewar gaɓoɓi tun da wuri.
Bayan nan waɗannan likitoci suna da kayan aiki da suke amfani da su domin temakawa fata ta warke sumul ba tare da haifar da mummunan tabo a kan fatar ba.
Bugu da ƙari idan aka sami matsala mai-ƙuna bai samu cikakkiyar kulawa daga likitocin wannan sashi ba, mai-ƙuna ka iya naƙasa, ya rasa aikin gaɓɓansa, domin gaɓoɓin za su janye, kuma su riƙe, sannan su ƙi yin aiki yadda ya kamata. Hakan na iya janyo yin tiyata domin sakin jijiyoyin da suka ƙage.
Don haka muna kira ga sauran likitoci abokan aiki da su ƙara ƙoƙari wajen gayyato likitocin wannan sashi da zarar an kwantar da mai-ƙuna a asibiti domin kaucewa faruwar wannan matsala. Sannan ga masu jinyar ƙuna a gida da lalle su zo asibiti domin gujewa faruwar wannan matsala.
Daga ƙarshe, ya kamata duk mai-ƙuna ko mai zaman jinyar mai-ƙuna ya sani cewa warkewar ƙuna ba a iya fata ba ne kawai. Saboda haka duk gaɓar da ba ta lanƙwaskewa ta miƙe sannan tai aikinta yadda ya kamata to wannan ƙuna ba ta warkewa yadda ya kamata, kuma alamace cewa akwai matsala.
Allah ya kiyaye mu, ya kuma bada lafiya.
#BurnInjury
#Contractures
#StubbornScar
#RuleOfNine
#TendonRelease
Copied From Physio Hausa
Posted by Adam M. Adam

No comments:

Post a Comment