TARIHIN WASU UNGUWANNI DA KE CIKIN BIRNIN
KATSINA
1. Makudawa asalin unguwar daga Buzaye ne
naAgalawa wadanda suka zo don fatauci. Cikin
wadanda suka zauna har da wani hamshakin
Attajiri mai suna Alhaji Basari, wanda a zamanin
Sarki Dikko ba mai kudinsa.
2. Darma an kafa ta shekarun 1452 ko
1475.Unguwa ce ta attajirai da Malamai wadanda
sukashahara a zamanin baya, kuma zuriyarsu har
yanzu na tashe.
3. Gafai unguwar Gafai, ana jin cewa, asalinta
daga Larabawan kasar Spain ne (watau
Andalusia kenan), wanda wani Malami mai suna
Malam Buhari da dansa MalamYahaya suka baro
Andalus lokacin tana daular Musulunci, ba su yi
zangon dindindin a ko’ina ba sai Gafai. Wata
ruwayar kuma ta ce a’a mutanenkasar Maroko ne
suka kafa ta.
4. Tsohuwar Kasuwa. Asalinta daga kaya ne da
mutanen Tunisiya, Moroko kan kawo , a rika
musaya ta ba ni gishiri in ba ka manda. Amma
wurin ya zama birni da gari a lokacin Sarkin
Katsina Ummarun Dallaje, lokacin da wani Malami
daga kasar Barno mai suna Malam Usman ya zo
da almajiransa ya zauna a wajen. Rafindadi.
Unguwar ta samo asali ne daga waniAttajiri da
ya gina rijiyoyi guda 12, don a rikadibar ruwa
kyauta. Daga mutanen da suka rayasunan
unguwar shi ne zuriyar Waziri Zayyana, wadanda
su kuma asalinsu Larabawan Madinane. Unguwar
kuma tana da Sharifai. Daga cikinsu akwai zuriyar
Abba Abu (Allah ya kara masarahama).
5. Unguwar Alkali, unguwa ce da mafi yawansu
Alkalai ne. Asalinsu zuriyar Malam Muhammadu
Chomo ne, wanda are hasashen ya Frito daga
Futo-jallon ta kasar Mali. Suna da zuriyarsu
yanzu wadda suke kira zuriyar gidan Hambali.
6. Masanawa. Tsohuwar unguwa ce, wadda
asalin tadaga Waliyyai ne guda biyu - Wali Dan
Masani dakuma Wali Dan Marina. Wali Dan
Marina asalinsa Balarabe, shi kuma Wali Dan
masani asalinsa daga kasar Barno ya fito.
Unguwar tana da fitattun Malamai, da Attajirai.
Wani marubuci maisuna Malam Abdullahi Kasim,
ma’aikaci a dakin karatu na Katsina ya rubuta
littafi cikakke a kan tarihin unguwar. An kuma
buga littafin Bambadawa, asalinsu daga Sarki
Bambadawan Sarkin Katsina Umarun Dallaje,
wanda ake kira da Ummaru Kilaga. Wasu kuma
sun ce asalin su mutanen Sakkwato ne. Unguwar
kuma akwai wanzamai.
7. Gambarawa. Unguwa ce da ake kaulanin yadda
aka kafa ta. Wasu sun ce mutanen Barno ne,
wasu kuma sun ce mutanen Mali ne. Unguwa ce
wadda akwai shahararrun Malamai a cikinta,
irinsu Malam Babangida Abbas.
8. Albaba. Zuriyar wani Malami ne mai suna Abul
Gaisu, suka kafa Albaba. Sai kuma wasu
Larabawa da ake jin Sharifai ne. Daga cikin su ne
aka samu su Abba Jaye da Abba Dayyabu.
9. Kofar Sauri da makwabtanta. Asalin su nan
daga wani Sarkin samari ne. Asalin wadanda
suka zauna wajen kuma zuriyarsu ita tkea wajen
haryanzu Bare-bari ne daga kasar
Barno.Babarbaren da ya fara zama har yau akwai
zuriyarsa shi ne Malam Yunusa. Ya zo a 1754.
Sai kuma kakan Attajirin nan Abu Kyahi, wanda
ake kira Malam Umaru, wanda shi ma daga kasar
Kukawa ya zo ta kasar Barno.
10. Unguwannin Rafukka, Nasarawa da
Makera.Wadannan unguwanni sun dade. Rafukka
tananan tun zamanin Sarkin Katsina
MuhammaduBello. Wuri ne mai dausayi da
albarkar noma.Sarkin Katsina Dikko shi ne ya
kara raya wajen.Nasarawa, ita kusan tarihinta da
tasirinta dayada na Rafukka.
11. Yammawa. Yammawa, asalinta unguwa ce ta
mazauna aikin lambu da noma a Rafukka. Ta rika
canza mazauni kafin ta tsaya inda take, kuma
takafu. An kafa unguwar tun karni na 15. A shafi
na 164 Farfesa Munnir ya fara bayanin Kofofin
Katsina, inda ya fara da Kofar Guga, wanda a
tarihi sunan matar Sarkin Gobir ce Bawa Jan
Gwarzo, wanda ya hana Katsina sakat. Sai
matarsa mai suna Guga ta gudo, ta tona asirin
mijinta na sihirce-sihirce ga Sarkin Katsina. Da
wannan asirin ne da aka samu aka ci Gobirawa
dayaki. Wannan ya sa Sarkin Katsina,
Muhammadu Jan Hazo ya sanya ma Kofar suna
kofar Guga,domin ta nan Guga ta shigo Katsina.
12. Sararin Tsako. Sunan unguwar ya samo asali
ne daga kalmar Buzayen Agadas, wanda a lokacin
fili ne fayau Buzaye kadai a wurin in sun zo
fatauci ke zama. Sullubawa. Asalin, wanda ya
kafa unguwar, wani Malami ne mai suna Malam
Umaru Dunyana daga Zamdam ta kasar Maradi
jamhuriyar Nijar. Da shi aka yi jihadin Shehu
Usman Danfodiyo a Katsina.
13. Filin masallacin Idi da unguwar Tudun
’yanLihidda. Masallacin Idi a nan ake sallar Idi
tunkarni na 16 kafin jihadin Shehu Usman
Danfodiyo.
14. Tudun ’yan Lihidda kuwa, asalinsa mayakan
da ke raka Sarki ne masallaci ke tsayawa suna
kare masallata daga yiwuwar kawo masu hari.
Wani lokaci kuma a nan dakaru kan yi hawa don
tsare garin Katsina daga harin mahaya a
tabarayin.
15. Kofar Durbi. Sunan kofar ya samo asali ne
daga Hakimin Mani. Shi kuma daga Durbi ta
Kusheyi, wadanda sune gidan sarautar Durbawa.
16. Filin Samji. Asalin wajen daji ne mai namun
daji kala-kala. Sai wani Baturen Ingila D.O mai
suna Samuel J. ya mai da wajen wurin sukuwar
dawaki. Daga nan ne, sai wurin ya koma Filin
Samuel J. A hankali, a hankali sai kiran sunan
wajen ya canza zuwa Filin Samji.
17. Rimin Badawa. Asalin wajen wasu mutanen
Barno ne daga wani yanki da yanzu yake jihar
Yobe mai suna Bedde. Sune bayan sun dawo
daga Sakkwato sun amso tuta suka yadda zango
suka kafa unguwar, daga Bedde aka koma kiran
su Badawa.
18. Kofar Marusa. Sunan ya samo asali ne daga
wani Basaraken Habe mai suna Marusa Umaru.
19. Kofar Kaura ta samo asali ne daga wani
mayaki daya mai suna Kaura Gumari. Daga nan
ta cigaba da jan sunan duk wani Kaura da ya
shahara a Katsina. Kaura Gumari daga baya ya yi
hijira, ya koma Tasawa ta kasar Maradi a can ya
rasu.
20. Dan Dagoro. Sunan da kafuwar garin ya
samoasali ne daga wani Malami mai suna
Abubakar da ya zo daga kasar Damagaram. Sai
ya samu wata itaciya ya yi bukkarsa a sama. Sai
jama’a suna zuwa kallon wannan abin mamaki. A
dokar daji kuma mutum ya yi daki saman itace?!
Sai aka rika kiran abin Dan Dagwam. Daga nan
sai takoma Dan Dagoro.
21. Kofar Kwaya. Sunan ya samo asali daga wani
Sarkin Habe mai suna Sarkin Kwaya. Wali Jodoma
ya taba tsine ma kofar ya ce, ba za ta cigaba ba,
sai bayan shekaru dari biyar. Kuma bata fara
bunkasa ba, sai da aka yi shekaru dari biyar da
doriya da waccan tsinuwar.
22. Kofar ’Yan Daka. Ita ma asalinta daga
Basaraken Habe ne na garin ’Yan Daka. Kofar
tana hade daunguwar ’Yan taba. Wanda a nan ne
gidan ’Yan Daka yake. Akwai kuma Marinar
Kadabo wadda masu sana’ar Rini suka kafa
wajen. A unguwar akwai rijiyoyin Rini.
23. Babbar Ruga, Fulani makiyaya suka kafa
wajen,amma Turawan Mishan su suka bunkasa
wajenda gina asibitinsu na maganin cututtukan
da ake dauka ko ake kyama.
24. Filin Polo, wanda asalinsa filin wasan Polo ne,
shine na farko da aka kafa a Najeriya.
SarkinKatsina Muhammadu Dikko ne ya kawo
wasan akasar nan bayan dawowarsa daga Ingila.
Anshata filin a 1921. Yanzu wajen yananan.
DAGA ADAM MOHD ADAM GAYA.
Monday, April 30, 2018
Sunday, April 29, 2018
KALAMAN SOYAYYA 02
KALAMAN SOYAYYA 02
NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya.
NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shud’ewa soyayyar ki na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina k’aunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. NA
TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
DAGA ADAMU MAHADI ADAM.

Saturday, April 28, 2018
HIKAYAR ANNABI HUDU
Hikayar Annabi Hudu
Annabi Hudu {a.s} ne da ya
kasance daga cikin Annabawan Allah
Madaukaki da aka aiko domin shiryar da
al’umma zuwa ga kadaita Allah da gudanar da
bauta a gare shi, kuma Annabi Hudu {a.s} ya
zo ne bayan da al'umma suka sake komawa
kan tafarkin shirka bayan tsawon shekaru
masu yawa da barin Annabi Nuhu {a.s}
duniya, kuma an aiko Annabi Hudu {a.s} ne ga
mutanensa da ake kira da Adawa. Sai a biyo
mu don jin abin da shirin ya kunsa:-
A cikin suratu-Hudu an ambaci hikayoyin
Annabawa mafi girman daukaka guda biyar da
irin matsalolin da suka fuskanta wajen isar da
sakon shiriyar da aka aiko su da shi zuwa ga
al’umma, gami da irin azabar da aka saukar
ga wadanda suka kafirta daga mutanensu,
kuma aka ambaci surar da suratu-Hudu, to a
cikin surar zamu saurari hikayar Annabi Hudu
{a.s} ne kan irin matakin da ya dauka wajen
kiran mutanensa zuwa ga bautan Allah
Madaukaki tare da kokarin shiryar da su zuwa
ga yin amfani da hankulansu wajen tantance
tsakanin gaskiya da bata, musamman sanin
cewa; gumakan da suke bauta musu, ba su
amfanarwa kuma ba su cutarwa, don haka
wace ƙarya ce suke ƙirƙirowa a tsakaninsu ta
hanyar danganta faruwan ayyuka daga
wadannan gumaka?.
Alkur’ani mai girma a cikin Suratu –Hudu
daga aya ta 50 zuwa 53 yana fayyace mana
hakikanin hikayar da cewa:-
"Kuma zuwa ga Ãdãwa {Mun aiko} ɗan'uwansu
Hũdu. Ya ce: Yã kũ mutãnena, Ku bauta wa
Allah, ba ku da wani abin bautãwa {da gaskiya}
sai Shi, babu abin da kuka kasance kuna
aikatawa sai ƙirƙirãr {ƙarya} kawai".
"Yã ku mutãnena, bã na tambayarku wata lada
a kansa {shi wannan saƙo}, lalle lada ta ba ta
zama ba fãce a wajen wannan da Ya halicce ni,
shin bã zaku hankalta ba?"
"Kuma ya mutãnena, Ku nẽmi gãfarar
Ubangijinku, sannan ku tũba zuwa gare Shi,
zai sakar muku sama ta kwararo muku da
ruwa, kuma Ya ƙãra muku wani ƙarfi a kan
ƙarfinku, Kuma kada ku jũya baya kunã mãsu
laifi".
Yanzu kuma zamu ambaci hikayar ta Annabi
Hudu {a.s} ce kamar yadda ta zo cikin
littattafan tarihi kamar haka;-
Bayan da ruwan dufana ya halakar da
mutanen da suka kafircewa sakon Annabi
Nuhu {a.s}, sannan mutane 'yan kadan da
suka tsira daga wadanda suka yi imani suka
dauki matakin sake gina kasa, a wannan
lokaci dukkanin mutanen da suke kan bayan
kasa muminai ne da suke kadaita Allah
Madaukaki. Sannan bayan shudewar shekaru
masu yawa, inda har mutanen da suka rayu
da Annabi Nuhu {a.s} suka bar duniya, sai ya
zame jikokinsu ne suke ci gaba da rayuwa a
duniya, sai kuma aka sake samun bullar
gurbatar tunani bayan mutane sun mance da
wasiyar Annabi Nuhu {a.s} tare da komawa
kan mummunar dabi'ar bautar gumaka.
Hakaki bautar gumaka ta samo asali ne a
tsakanin mutane sakamakon matakin da
wasu daga cikin jikokin mutanen Nuhu {a.s}
suka dauka na sassaka gumakan mahaifansu
da suka tsira daga ruwan dufana da nufin
kada a mance da su, inda mutane suke
girmama gumakan fiye da kima, kuma hakan
ya ci gaba da gudana har ya kai ga matakin
da girmamawar ta rikide zuwa bautar gumaka.
Hakika makircin shaidan ya yi galaba a kan
hankulan mutane inda suke riya cewa
wadannan gumakan da suke girmamawa sune
tsaninsu zuwa ga Allah Madaukaki, kuma
suna matsayin Ubangiji ne, don haka suka
koma suna shirka wa Allah wajen bauta, inda
duhun bata da rudun rayuwa suka sake
dawowa kan doron kasa, sakamakon haka
Allah cikin jin kansa da rahamarsa ga talikai
ya aiko musu Annabi Hudu {a.s} domin shiryar
da su hanya madaidaiciya.
Annabi Hudu {a.s} ya kasance daga kabilar da
ake kira A'da, kuma wannan kabilar tana
zaune ne a wani waje da ake kira da Ahqa'f,
kuma waje ne mai sahara da yawan yashi
kusa da bakin teku. Kabilar Adawa tana
rayuwa ce cikin haimomi masu girma da suke
da ginshikai masu karfi da tsayi, kuma Adawa
sun kasance sun fi sauran mutanen da suke
rayuwa da su a bayan kasa girman jiki da
karfi gami da tsayi kamar yadda suka
kasance suna alfahari da karfinsu, saboda
babu wani jinsin bil-Adama da ya kai su karfi
a wannan zamani, kuma duk da tarin
ni'imomin da Allah ya yi a gare su, amma suna
rayuwa ce cikin duhun bata da rudun rayuwa
ta hanyar bautar gumaka, sannan suna kare
wadannan gumaka da dukkanin karfinsu tare
da yaki dominsu.
Hakika Adawa sun kasance suna cutar da
Annabinsu tare da gudanar da izgili a gare shi
da cewa; "Lalle ne mũ, haƙĩƙka, Munã ganin ka
a cikin wata wauta! Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa,
Munã zaton ka daga maƙaryata. Kuma
kasancewar Adawa mutane ne masu alfahari
da irin karfin jikin da aka ba su, maimakon su
yi tunanin cewa; lalle Allah da ya halicce su
shi ne mafi karfi da girman iko a kansu, kuma
tabbas zasu koma zuwa gare shi, amma sai
suka zabi yin riko da gumaka a matsayin abin
bautansu. Annabi Hudu {a.s} ya dauki
matakin fadakar da su tare da kokarin mai da
su kan fidirarsu ta dan Adamtaka da cewa:
"Ya mutãnena! Ku bautã wa Allah! Bã ku da
wani abin bautã wa, koma bayansa . Shin bã
zã ku ji tsoron Allah ba?".
Haka nan Adawa sun dauki matakin gabatar
da zargi da kokarin muzantawa ga Annabi
Hudu {a.s} da cewa: Shin kana son zama
shugaba ne a kanmu ta wannan kira naka?
Shin kana son wata lada ce daga gare mu,
inda zamu dinga tattara maka dukiya? Amma
sai Annabi Hudu {a.s} yana mayar musu da
martanin cewa: Baya neman wata lada daga
gare su, sai a wajen Allah Madaukaki, iyakan
abin da ke bukatar gani shi ne su 'yantar da
tunaninsu tare da sanya hankalinsu a gaba
domin ganin hakikanin hasken rayuwa, inda
ya ambata musu tarin ni'imomin da Allah ya yi
musu a rayuwa tare da sanya su a matsayin
magada ga mutanen Annabi Nuhu {a.s}, kuma
ga tsananin karfin jiki da Allah ya huwace
musu tare da zaunar da su a waje mai tarin
arziki da wadatar amfanin gona ta hanyar
saukar musu da ruwan sama da ke rayar da
kasa, amma mutanen Hudu {a.s} suka
butulce tare da yaudaruwa da karfin jikin da
aka ba su, suna jin cewa babu wani abin da
zai fuskance su, ba tare da sun kare kansu da
karfi ba, don haka suka kara girman kai da
dagawa a bayan kasa.
A karshen shirin namu zamu ambaci wani abu
ne daga cikin taskar iyalan gidan manzon
Allah tsarkaka {a.s} dangane da hikayar ta
Annabi Hudu {a.s} kamar haka:-
Allamah Muhammad Husain Tabataba'i
ma'abucin tafsirin Al-Mizan ya nakalto
ruwayar iyalan gidan manzon Allah tsarkaka
{a.s} cewa: Hakika Adawa sun kasance suna
rayuwa ce a wata kauye mai dauke da
amfanin gona da yawan dabino, kuma sun
kawata kauyen da tarin gine-gine ga kuma
karfin jiki da aka huwace musu, amma sai
suka wofantar da hankulansu wajen gudanar
da bautar gumaka, don haka Allah Madaukaki
ya aiko musu Annabi Hudu {a.s} domin ya kira
su zuwa ga addinin Musulunci tare da
kauracewa gumakan da suke bauta musu,
amma sai suka kafirce tare da daukan
matakin cutar da Annabi Hudu {a.s}, don haka
aka aiko musu da fari na tsawon shekaru
bakwai.

Friday, April 27, 2018
AMFANIN TSA-TSA A RAYUWARMU TA YANZU
BAYANI GAMEDA YADDA TSATSA YAKEDA AMFANI ADUNIYA.
Turkashi!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
Ka dauka cewa tsatsan dake fitowa ajikin kwano ko karfe bayada amfani ko?.
To barikaji, duk wata camera a duniya to da tsatsa ake sarrafawa ahada camera na waya, da duk wata camera na daukan hoto, tsatsan daka sani dashi ake hadawa, duk haduwar camera din wayarka babu shakka da tsatsa aka hada, sunan camera din ana ce masa CMOS camera. C =yana nufin complementary, M =yana nufin metal, O = yana nufin oxide, S= kuwa yana... nufin semiconductor, Lafazin complementary ainihin kalmar daga complement ne, idan akace complement ana nufin some thing which is farfect or complete, shi kuwa lafazin metal ma bama sai anfassara shi ba kowa san cewa karfe ne, lafazin oxide kuwa ainihin kalmar daga oxygen ne wato iskan damuke shaka kenan, Babu shakka yau nazo da abinda ba kowane zai yadda sai wanda ya yarda da irin research din danakeyi, dakuma wanda yasan chemistry zai iya yadda da bayanin da zanyi yanzu, idan akace metal oxide to ana nufin karfe da oxygen sunyi reaction dajuna wato sunhadu, wato aduk lokacin da ruwa yataba jikin wani karfe zakaga tsatsa tafito, saboda acikin ruwa akwai oxygen, wannan oxygen din shi zaiyi reaction da wannan karfen. Bayan dan kwanaki kadan sai kaga tsatsa yafara fitowa, shiyasa idan ruwa yataba karfe idan iska ya hura wannan karfen to daga zaran iska yahura to tsatsa zai biyo baya, shiyasa akeso ayi maza asaka wani mai ko abinda zai hanashi tsatsan fitowa, shi tsatsa idan yafito yana hana karfe karban wutan lantarki, koda ya karbi wannan wutan kuwa to zai karba ne amma bawai dakyau ba kamar yadda karfen da baida tsatsa zaikarba ba. To sai karfen da yakeda tsatsan yarikide yazama semi conductor, wato semi ana nufin matsakaici, shi ba good conductor ba kuma shi ba bad conductor ba wato yana tsaka tsaki ne, shiyasa ake ce masa semi conductor, to itakuwa na,uran computer shi yakeso wajen designed na sarrafa kwakwalwar camera na waya da sauran cameras dake jikin wasu na,uran.
shiyasa ake kiran wannan cameran da ake hadawa da tsatsan dasuna complementary metal oxide semi conductor.
Ina fatan masu karatu sungane sirrin yadda abin yake.
Bama cameran waya ne ake hadawa da tsatsa ba, even RAM na computer duk tsatsane yake wannan aiki. amma akan sarrafa tsatsan yadawo normal one bawai yadda yaken nan ba, shiysa suke cewa complementary wato perfect rusted metal wato karfe mai tsatsa amma tsatsan tacaccene .
Ga hoton daya daga cikin kwakwalwan camera wanda aka hadashi da tsatsa. Inka kalli hoton zaga alamanun tsatsan acikin glass .
Ashe dai tsatsama yanada amfani wa dan adam.
For further reading
aduba littafin the circuit design and simulation third edition shafina 770,
dakuma littafin The introduction to vlsi system shafina 840.
DAGA ADAM MOHD ADAM GAYA
Thursday, April 26, 2018
MATHS KASHIN BAYAN KIMIYYA DA FASAHA
MATHEMATICS KASHIN BAYAN KIMIYYA DA FASAHA
1. Sau da yawa za ka ga mutane su na kokawa da wahalar
lissafi da kuma yawan faduwa jarrabawar sa. Kuma za ka ji Dalibai su na
tambayar wai mai ya sa a ke tilasta su sai sunyi lissafi? Kuma a ina ne za su
yi amfani da shi? Ko kuma mene amfanin sa?. Wadannan tambayoyi sun biyo bayan
rashin sanin gudun-mawar da lissafi ya ke bayarwa a duk wata harka da ta shafi
kimiyya da fasaha. A yanzu babu wani ilimin kimiyya da fasaha mai zurfi wanda
ba ya bukatar ilmin lissafi. Hatta ilmin kasuwanci, banki, da sauransu, babu
wanda mutum zai iya yi da kyau ba tare da lissafi ba. Duba tun daga haluntun
ubangiji: sammai, da kassai, rana da wata, dare da rana, safiya da
maraice. Duk wadannan abubuwane da mutane ma su tunani suke shan mamaki wajen
yadda su ke gudana bisa tsari. Haka, idan mutum ya duba irin baiwar da Allah Ta’ala
ya yi wa dan Adam ta kere-kere: Radio, Talabijin, Mota, Jirgin ruwa da na sama,
Inji mai kwakwalwa, da dai sauransu. Mutum ya kan sha mamaki yadda wadannan
abubuwa duka su ke aiki bisa tsari. To duk wadannan abubuwa su na gudanane bisa
tsarin ilimin lissafi. Wannan shi ya sa, mutum ba ya iya samun shiga kowace
jama’i a duniya domin karantun kimiyya ko fasaha sai da shaidar lissafi mai
kwari. Haka kuma, ba ka iya samun aiki mai kyau da ya shafi kimiyya da fasaha,
sai ka na da shaidar lissafi mai kwari. Wannan shi ne ya sa wasu sukan yiwa
lissafi kirari: Rariya matatar dalibai. AHA MUJE ZUWA.
2. Mutane sun sha banban
Malaman sanin
yanayin dan Adam tuni su ka gano cewa mutane sun sha banban wajen yadda su ke
fahimta da zartar da abubuwa. Kuma ita fasaha iri-iri ce. Wasu mutane akwai su
da saurin gane abubuwa da su ka shafi lissafi, wasu kuma sun fi saurin gane
abubuwa da su ka shafi yare. Wasu sun fi so su yi abu da hannunsu, wasu kuma
sun fi so su karanta, haka kuma wasu sun fi son sauraro. Dangane da lissafi,
ina ganin mutane sun kasu kashi uku: Kashin farko su ne mutanen da Allah Ta’ala
ya yi mu su baiwa mai yawa ta fahimtar lissafi. Wadannan mutane, da zaran an
dan yi musu bayani nan take sai ka ga sun gane abin da a ke nufi. Wani lokacin
su kan gane abu fiye da wanda ya yi mu su bayanin, ko da kuwa malamin su ne.
Kai wasu ma suna da basirar gane abubuwa ba tare da an koyar da su ba. To
wadannan mutane ba su da yawa a cikin jama’a. Kashi na biyu su ne kishiyar na
farko. Su kuma mutanene da ke shan wuya kwarai wajen gane duk wani abu da ya
hada da lissafi. Kuma a kan sha wuya wajen koya musu lissafi. Ko da kuwa an yi
bayani sosai sun yi kamar sun gane, da zaran an yi musu tambaya, sai ka ga ashe
sanin Damisar Bunu su ka yi. To su ma wannan kashin ba su da yawa sosai cikin
jama’a. Kashi na uku su ne wadanda su na gane lissafi idan an yi musu cikakken
bayani, amma sukan sha wuya kafin su gano wasu abubuwa masu zurfi. Amma da
zaran sun tara hankali gu daya sun dage, sai ka ga sun gane abin da ake nufi. Wadannan
mutane su ne su ka fi yawa a alumma.
Manyan
matsaloli guda biyu da ke damun dukkan dalibai sune: Na daya mafiya yawa
dalibai tun tuni an cusa musu ra’ayin cewar lissafi abune mai wahalar gaske kuma
sun amince; to wadannan mutanen, da wuya su koyi lissafin koda kuwa suna da
basirar yin lissafin. Matsala ta biyu itce, mafiya yawan malamai masu koyar da
lissafi su kan su basu iya lissafin ba, musamman a primary da secondary; lalle
kuwa idan dalibi bai sami tushen lissafi mai kyau ba, to fa da wuya dalibin nan
yayi wani katabus a gaba. Hmmm.
3. Yadda ya kamata
dalibi ya koyi lissafi
Ga dukkanin
dalilbi mai sha’awar karatun kimiyya da fasaha kamar su: Mathematics,
Chemistry, Physics, Geology and Mining, Computer Science, ko Engineering,
kamar: Chemeical, Electirical, Mechanical, Civil, Computer da dai sauransu. Ko
kuma karatun zane-zane, kamar su Archintecture, Planning, Survey, Construction
da dai sauran su. Ko karatun Likitanci, ko karatun harkar kasuwanci, kamar su:
Accounting, Finance, Economics, Banking da dai sauran su. To babu shakka
ba zai iya yin fice a wadannnan fagagen ba sai ya na da kyakkyawar fahimtar
lisafi.
Kamar yadda mu
ka sani, mutane da yawa su kan samu matsala wajen koyon lissafi, ba don komai
ba sai dai kawai don ba su san yadda ya kamata su koyeshi ba, ko kuma basu sami
malamai da su ka san yadda ya kamata a koyar da shi ba. Tambaya
itace, yaya dalibi zai yi domin ya dinga samun lissafi da dan sauki. Ga wasu
‘yan shawarwari da za su iya taimakawa in Allah ya so. Sune:
- Lallene ya kamata dalibi ya fahimci cewa ba’a koyon kowane irin karatu da sauki. Kaji abin da Annabi Musa AS yace: Lalle mun sha bakar wuya wajen wannan tafiya ta mu ta neman karatu. Dubi Suratul Kahfi ka sha karin bayani.
- Ya kamata kuma dalibi ya fahimci a wane ajin mutane uku ya ke da mu ka yi bayani baya. Wannan zai taimakawa kowa yasan matsayin sa. Domin idan mutanen ajin farko su na bukatar karatun awa daya, to mutanen aji na biyu zasu bukaci awa biyar ko fiye. Su kuma ‘yan aji na uku zasu bukaci awa biyu zuwa uku. Sabo da haka ka da kowa ya hada kan sa da wani.
- Sannan ya dace dalibi ya zamanto ya na shaawar lissafi. Duk da cewa akan samu masu basirar abu amma basa sonsa, bincike ya nuna cewa Idan mutum yana sha’awar abu, ya kan bashi lokaci. Hausawa suna ce wai So yafi bauta ciwo. Haka kuma wanda bai son abu, to, babu shakka da wuya ya bada hankali akan abun sosai balle ma ya fahimce shi.
- Kuma ya zama yana halartar aji akan kari ba latti. Sannan a aji ya zama mai tara hankali gu daya yayin duk da malami ke koyarwa. Shi lissafi abu ne mai bukatar natsuwa da tunani. Yayin duk da malami ke bayani idan hankalin ka ya na wani abu da ban, to da wuya ka gane abin da ya koyar.
- Lalle ne mutum kuma ya zanto mai naci. Da zaran an gama karatu a aji to mutum nan take ya je ya yi tishi a gida ko dakin karatu (library). Idan za ka fara karatu, to ka fara karanta misalai da malami ya bayar a aji, idan ka gane su, sai kaje gaba. Wato daga mai sauki zuwa mai wuya.
- Duk tambayoyin da malami ya bayar a yi a gida, to lalle ka dunga yi a kan kari. Idan da sauran lokaci, ka kwatanta yin sauran da malami bai ce a yi ba. Yin haka, zai tabbatar ma ka cewa ka gane ko ba ka gane ba. Abin da ba ka gane, sai ka kara dagewa da tunani har sai ka gano shi. Amma idan abin ya faskara, to sai ka nemi taimako wajan malamin ka ko abokin ka da kasan ya fi gane karatu. Lissafi bai yiwuwa sai da tunani da naci.
- Kafin aji na gaba, ka tabbatar da cewa ka gane karatun baya. Sannan idan da hali ka yi kokari kasan karatun da za ku yi nan gaba, kuma ka dan duba kadan kafin malami ya zo aji. Amma kar ka kuskura ka bar karatu ya taru sai lokacin jarrabwa ta kusa. Wannan baban kuskure ne, domin ita kwakwalwa ta na da iyaka. Ba ta son a takura ta da yawa cikin kankanin lokaci. Nan ta ke za ka ga mutum ya rikice.
- Zai kyau kuma mutum ya zanto ya hada kai da mutane ma su basirar lissafi domin su dinga yin karatu tare. Wannan ya kan taimakawa kwarai ga mutanen duka. Shi wanda ya yi bayani ya kan kan kara ganewa, shi kuma da akayi wa bayani, ya kan samu karuwa so sai.
- Banda Hadda: Shi lissafi ya na bukatar fahimta ne kawai. Kar ka kuskura ka yi haddar abin da baka fahimta ba. Lalle ka yi iyakacin kokarin ka ka ga cewa ka gane sakon da kyau. Da zaran wani abu ya sha ma kai, to ka je ka tamabaya. Allah ya ce ku tambayi masana idan ba ku sani ba. Su kuma Hasusawa su kance tsugunawa Wada ba gajiyawa ba ne.
- Sannan ka natsu ka gano hanyoyin da idan ka bi su to ka fi saurin gane karatu. To sai ka dage akan su.
- Haka kuma ka yi kokari ka gane lokutan da kafi jin dadin yin karatu a cikin su. Sai ka lizimce su da kyau, banda hira a wadannan lokutan.
- Bayan kuma ka gama duk abin da ya kamata ka yi to sai ka mikawa Allah sauran. A yi ta addu’a Allah ya buda ma ka basira ka dinga gane karatun da sauri. Saboda haka dalibi ya dage da addu’a Allah ya buda ma sa basira ya kara gane karatu.
4. Karkarewa da fatan
alheri
To kamar yadda Na nuna a baya, duk wani ci gaba da a ka samu na
kimiyya da fasaha, to lallai sirrin abin ya na cikin lissafi ne. Wannan shi ne
ya sa babu Jami’a a duniya da za ta dauki wani dalibi domin karatun
kimiyya ko fasaha sai ya na da shahadar lissafi mai kwari. Haka kuma ko da
mutum ya gama karatu, samun aiki na da wuya idan ba ka da kwarewa wajen
lissafi. Saboda haka na ke baiwa dalibai shawara, cewa su dage so sai
wajen karatunsu, su kuma tara hanlinsu gu daya. Allah Ya yi alkawarin cewa duk
mutumin da ya dage kan al’amari, to zai samu gudammawa daga gurin ubangiji.
Allah ya yi ma na jagora baki daya, amin.
DAGA ADAMU MAHADI ADAM GAYA
Tuesday, April 24, 2018
TARHIN REAL MADRID
TAKAITACCEN TARIHIN REAL MADRID
Real Madrid Club de Futbol ko Los Blancos. (The White)
Kwararriyar kungiyar kwallon kafa ce dake birnin Madrid na kasar Spain.
Itace kungiyar da FIFA ta zaba a matsayin kungiyar da tafi samun nasara a karni na 20, domin ta lashe kofin rukuni-rukuni na kasar Spain (La-liga) sau 31, Spanish Cup sau 17 da kofin zakarun nahiyar turai sau 9 da kuma kofin UEFA sau biyu.
An kafa kungiyar Real Madrid a shekarar 1902 (6 March 1902). A shekarar 1900 aka kafa kungiyar Club Espanol de Madrid. A 1902 kungiyar ta rabu biyu hakan ya kawo kafuwar Madrid Fooball Club.
A shekarar 1905 Madrid FC ta fara yin nasarar daukar kofi, bayan ta doke Athletic Bilbao a kofin Spanish Cup.
Madrid FC na daya daga cikin wakilan hukumar FIFA na farko kuma wakiliyar rushasshiyar kungiyar G-14 na manyan kungiyoyin da ake ji dasu a nahiyar turai.
A 1920 ne aka canja sunan kungiyar zuwa Real Madrid bayan da sarki Alfonso ya amince a yi amfani da lakabi Real da ake nufin Royal ga kungiyar.
A shekarar 1929 ne aka fara gasar La-liga inda Real Madrid ta jagoranci gasar har zuwa wasan karshe inda tayi rashin sa'a a hannun Athletic Bilbao. Ta zama ta biyu bayan Barcelona. Real Madrid ta fara lashe gasar La-liga ne a 1931/1932, sannan shekarar gaba ma ta sake lashewa.
A 1940 Santiago Bernabeu Yeste ya zama shugaban kungiyar, kuma a mulkinsa ne Real Madrid ta sake gina filayen wasanninta na Santiago Bernabeu da Ciudad Deportiva, bayan yakin basasar kasar Spain.
Santiago Bernabeu a shekarar 1953 ne ya fara dakko kwararrun yan wasa daga kasashen waje. Fitacce daga cikinsu shine Alfredo di Stefano, wannan ya bashi damar kafa tarihin kungiyar da ta fara tattara yan wasa daga sassan duniya a tarihin kwallon kafa. A karkashin Bernabeu ne Real Madrid ta zama gagabadau a fagen kwallon kafa a kasashen turai.
Real Madrid ta lashe kofin kasashen turai (Uefa Champions League) sau biyar a lokaci daga a tsakanin 1956 zuwa 1961 wanda ya hada da ci 7-3 da tayiwa kungiyar Eintracht Frankfurt a filin wasa na Hampden Park a wasan karshe a 1960. Cin kofin sau biyar a jere yasa kungiyar ta samu mallakin kofin na ainihi tare da bata damar sanya tambarin girmamawa na UEFA.
Real Madrid ta lashe Uefa Champion League karo na shida a 1966 bayan ta doke FK Partizan da ci 2-1 a wasan karshe.
Ranar 2 July 1978 shugaban Real Madrid Santiago Bernabeu ya rasu. A shekarar 1996 shugaban Real Madrid na lokacin Lorenzo Sanz ya kulla yarjejeniyar daukar Fabio Capello a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar na tsayon shekara daya.
A 1998 Real Madrid ta sake yin nasarar daukar kofin Uefa Champions League karo na bakwai bayan ta samu nasara akan Juventus da ci 1-0 a wasan karshe.
A watan bakwai na shekarar 2000 aka zabi Florentino Perez a matsayin shugaban kungiyar, a mulkinsa ya samu nasarar kawo shahararrun yan wasa kungiyar, wanda suka hada da Zinedine Zidane, Ronaldo, Luis Figo, Roberto Carlos, Raul da David Beckham. A shekarar ne kungiyar ta sake cin kofin Uefa Champions League karo na takwas. Sannan kuma ta samu nasarar daukar na tara a shekarar 2002 da kuma kofin La-liga a 2003 duk a lokacin mulkin Perez.
Ramon Calderon ya zama shugaban Real Madrid ranar 02 July 2006 da zuwansa ya sake dakko Fabio Capello a karo na biyu a matsayin mai horar da yan wasan kungiyar, da kuma tsohon dan wasan kungiyar Predrag Mijatovic a matsayin manajan kungiyar.
Real Madrid tayi nasarar cin kofin La-liga karo na 30 a shekarar 2007. Sannan ta sake cinye kofin a 2008. Ranar 01 June 2009 Florentino Perez aka sake zabarsa shugaban kungiyar karo na biyu. Da zuwansa ya sayo shahararren dan wasan AC Milan da Kasar Brazil wato Ricardo Kaka akan kudi £60m. Sannan kuma sai dan wasan duniya na lokacin Cristiano Ronaldo daga kungiyar Manchester United ta kasar England, akan kudi £80m. Wannan sayayyar itace tafi kowacce tsada a tarihin kwallon kafa bayan dan wasar kasar France Zinedine Zidane.
Duk da Real Madrid tafi kusa da kungiyar Athletic Madrid. Amma babbar abokiyar adawarta itace kungiyar Barcelona.
Real Madrid itace kungiyar kwallon kafa da tafi kowacce kungiya samun nasarar daukar kofuna. Ga jerin wasu kofuna da kungiyar ta dauka:
9 Uefa Champions League.
31 Spanish La-liga.
19 Spanish Cup.
18 Regional Cup.
3 Intercontenatal Cup.
8 Spanish Super Cup.
5 Community Cup.
2 Uefa Cup.
2 Spanish League Cup.
2 Latin Cup.
2 Little Cup.
1 European Super Cup.

DAGA ADAM M. ADAM GAYA
Monday, April 23, 2018
YADDA AKA KASHE SIR AHAMADU BELLO SARDAUNA SOKOTO A GABAN DIREBANSA:
YADDA
AKA KASHE SIR AHAMADU BELLO SARDAUNA SOKOTO A GABAN DIREBANSA:
DIREBAN
NASA YAKE FADA KAMAR HAKA:
Alhaji Ali Sarkin Mota shi ne ya zan ta
da Wakili Jaridar Leadership yadda aka kashe Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto
Firimiyan Jihar Arewa akan idonsa. Ya shaidawa Midat Joseph dan Jaridar cewar
zan iya mantawa da komai, amma banda yadda sojoji suka kashe Sardaun da iyalin
sa a gaban ido na a 15 ga watan Janairun 1966.
Leadership: Kana gidan Firimiya a ranar
15 ga watan Janairun 1966. Me zaka iya tunawa da ya faru a wannan ranar?
Sarkin-Mota: Ga wadan da suke zaune a
Kaduna zasu shaida yadda sojoji suke yin atisaye a makarantar Kafital dake
unguwar Malali a garin Kaduna, duk lokacin da za ayi wani biki a hukumance.
Amma a lokacin da ake shirin yiwa Sir Abubakar Tafawa Balewa Prime minister da
Firimiya juyin mulki a 15 ga Janairun 1966 mun ga sojoji suna yin atisaye ba
tare da wani biki ya gabata ba na hukuma.
A ranar Juma'a 14 ga watan Janairun
1966, wani abokin aikina ya sanar da ni cewar, muna sa ran yin bakin alfarma a
wannan rana daga Yammacin Najeriya zasu kawowa Firimiya ziyarar bangirma. Sai
daga baya aka tabbatar min da cewar Cif Samuel Akintola, shi ne zai kawo ziyara
Kaduna, a wannan rana, an shaida mana cewar zai sauka a filin jirgin sama na
Kaduna da Misalin 11:30 na safe, dan haka ne muka shirya na tuka Sardauna zuwa
filin jirgi shi da 'yan tawagarsa da Ministocinsa domin taryen Samuel Akintola.
Mun isa filin jirgi, muna zaune a zauren
manyan baki, muna jiran saukar jirgin da ke dauke da su Akintola, sai Firimiya
ya duba agogonsa yaga lokaci ya nuna 12:00 na rana, daga nan ne Firimiyan ya
aiki daya daga cikin Ministocinsa akan, yaje ya samu masu lura da sauka da
tashin jirage ya tambaye su, me ya faru aka samu jinkirin saukar jirgin su
Akintola, dan aiken yana zuwa suka shaida masa cewar, rashin kyawun yanayi ne
ya hana jirgin sauka a kan lokaci, amma zai iso nan da 12:30. Muka cigaba da
zama muna jira har 12:30 tayi babu alamun saukar wani jirgi, Firimiya ya kuma
aikawa a tambayi ma'aikatan, shin ya akai har yanzu jirgin bai sauka ba, suka
sake shaida masa cewar rashin kyawun yanayi ne ya janyo tsaiko, amma jirgin zai
iso nan da 1:00, muna zaune har agogo ya nuna, karfe daya babu alamun saukar
wani jirgi, aka kuma cewa, muyi hakuri Jirgin zai sauka karfe 1: 30.
Daga nan ne, Firimiya ya tashi zai fita
tunda yake Juma'a ce ranar dan zuwa Masallaci, sai ya gayawa mataimakinsa,
Aliyu Makaman Bidda, cewar ya tsaya a filin jirgi ya taryi Akintola idan ya
karaso, domin shi zai wuce Masallaci. Cikin raha da kakaci, sai Makaman Bidda
yace masa, ranka ya dade, shin ka maida ni arne kenan ni ba zan je Sallah ba?
Firimiya ya mayar masa da amsa, cewar bana nufin haka ko kadan, illa kawai ina
nuna maka matsayin ka na mataimaki, a lokacin da bana nan ka tsaya ka wakilce
ni. Nan dai Makaman Bidda ya nunawa Firimiya muhimmancin ya tsaya da kansa ya
taryi Akintola din, idan ya so yayi Sallar azahar a filin jirgin, nan dai
Firimiya ya gamsu, suna cikin yin Sallar Azahar ne sai jirgin su Akintola ya
sauka.
Bayan su Firimiya sun idar da Sallah ne,
aka ďanyi kade kade da bushe bushe na taryen manyan baki kamar yadda aka saba
ana taren baki na alfarma. Daga nan Firimiya ya gabatar da Ministocinsa ga
Samuel Akintola, a lokacin da muke kokarin fita daga zauren karbar baki, sai
muka hangi Gilmawar Mejo Chukwuma Nzeagwu a cikin kakin soja, sai Firimiya ya
tambaya me Nzeogwu yake yi a cikin filin jirgin sama sanye da kaki? Sai
Akintola ya tambayi Firimiya ko da matsala ne? Sai Firimiya yace, abun mamaki
ne naga Soja da kaki yanzu yana zirga zirga, daga nan su duka biyu sukai dariya
suka wuce muka fita dan hawa mota.
Na wuce gaba na tuka su, zuwa gidan
saukar baki na Gwamnati, inda Firimiya ya shiryawa bakin liyafar cin abincin
rana shi da 'yan tawagarsa, sannan kuma su yi tattaunawa a kebe. Akintola ya
dan yi min hasafi (inji Direban sardauna) Har ma dogarinsa yake cewa nai masa
wani abu shima. A lokacin naji mutane suna fadin cewar, Akintola ya gayawa
Sardauna cewar, a yanayin yadda abubuwa suke faruwa, Gara su nemi mafaka a wata
kasar su bar Najeriya, amma dai ni banji wannan magana daga bakin su ba, a
wajen jama’a naji. Bayan sun gama tattaunawa, bakin sun gama cin abinci, muka
dauko su dan raka su filin jirgi, domin komawa. Anan ne, muka sake ganin Mejo
Chukwuma Nzeagwu, wannan karon yana sauri yana bin Kwambar motocin mu, kamar
akwai wani abu da yake son fadawa shugabannin guda biyu.
Bayan da Akintola ya hau jirginsa ya
koma, suka yi Sallama da Firimiya. Muka kama hanya dan komawa gidan Gwamnati,
sai Firimiya ya lura Nzeogwu yana biye da shi a baya. Da yaga haka, sai yace,
maza yi kwana ka kaini cikin gari na dan motsa jik a otal din Hamdala, anan ne
galibi Firimiya kan tsaya ya shakata a lokacin da yake hutu baya aikin komai,
kafun mu isa wajen, sai Firimiya yace, na kaishi gidan kwamashinan 'yan sanda
na lokacin, MD Yusufu, muna isa gidan sai muka tarar Kwamashina baya nan, mun
iske wani dan sanda yana gadi a bakin Kofa, dan sandan dake gadi ya tambayi
Firimiya, idan ya dawo wa za a ce masa ya zo? Sai Firimiya yace masa, ka gayawa
oganka, wani dogon mutum me gashin baki yazo bai same shi ba. Sannan Firimiya
ya zaro Fan daya ko biyu a aljihunsa ya baiwa dan sandan.
Da muka fito daga gidan MD Yusufu, sai
na tambaye shi, ina kuma zamu je? Sai yace na kai shi unguwar Kakuri, muna zuwa
Kakuri sai ya shaida min cewar yana son zai kai ziyara DIC (Defence Industry
Cooperation), muna gab da isa bakin kofar shiga, sai muka ga an rubuta baro
baro, 'No Enter By Order' ma'ana ba wanda zai shiga sai wanda aka yiwa izni.
Sai na gayawa Firimiya cikin raha cewar, Mubi fa a hankali sojojin nan zasu iya
harbi, ba hankali gare su ba, Firimiya bai ce komai ba, da yake da Azumi a
bakinsa, sai na kalle shi ta madubi muka hada ido, sai yace mun, kana zaton ko
bacci nake? Sai nace masa, ranka ya dade naga kayi tagumi ko akwai wani abu da
yake faruwa ne? Sai yace, kawai ina tunanin wannan rayuwar ne, sai na sake
tambayarsa, ko da akwai wata matsala ne? Sai yace mun, bai san me zai faru da
shi ba idan ya mutu, sa ya kara da cewar "bana fatan na kara shekaru biyar
nan gaba" yace gaskiya shi ya gaji da wannan rayuwar. Sai nace masa, haba
ranka ya dade ya zaka dinga irin wannan tunani, ai kullum addu'ar mu Allah ya
baka lafiya da yawan rai. Nace masa, Yallabai, idan ka mutu yanzu, akan idon mu
komai zai jagwalgwale a kasarnan, sai ya kara cewa, ni dai wannan rayuwa ta
ishe ni. Daga nan sai yace, na maida shi gidan Gwamnati. A lokacin biyar na
Yamma ta kusa, an kusa Shan Ruwa, muna isa gida har ya bude Kofa zai shiga sai
ya kira daya daga cikin hadimansa, Mamman Bakura, ya shaida masa cewar, idan an
kira Sallah kusha ruwa Kada ku jirani, shi kansa Bakura yayi mamaki domin mun
saba da Firimiya muke buda baki tun farkonsa Azumi.
Leadership: ka bayyana mana abubuwa na
karshe da suka faru da Sardauna a gaban idonka?
Sarkin-Mota: Bayan da aka yi Sallar
Asham, sai Firimiya ya sauko daga sama ya shaida mana cewar kowa yana iya
tafiya ya kwana cikin iyalansa, sai daya daga cikin hadimansa da ake kira
Jarumi, yace shi yana nan ko bukatar gaggawa zata taso. Ni kuma ina tare da a
iyalina a gidan Gwamnati a bangare na, da Misalin karfe daya na dare, ina wanke
mota a lokacin, sai Firimiya ya sauko yana kwalawa me askinsa kira, yazo da
sauri, da yazo sai ya gaya masa yana son yayi masa asiki a daren. Sai ya
tambayeni da su wa yaga in magana dazu? Sai nace masa da 'yan sandan da suke
gadin gidan Gwamnati muke magana.
Ashe ban sani ba, nayi kuskure, mutanan
da na zata masu gadi ne, ashe sojoji ne, tuni sun shigo gidan a sace, sun
rarraba kansu kusfa kusfa. Daga nan Firimiya ya aiki Bakura ya sayo masa
kilishi da balangu, daga nan Firimiya yace na zo, na hau sama na daukowa masu
gadin Lemo su sha, na shiga na dauko musu 'Tango'. A wannan lokacin bamu sani
ba ashe, tuni wadannan sojojin sun kashe masu gadin gidan Gwamnati, suna gani na,
suka kirani suka ce nai maza maza na bar gidan, kafun na tafi sai daya daga
cikinsu yace mun 'ina Sardauna yake' Sai na nuna masa ban san wa yake tambaya
ba, a lokacin wajen karfe daya da rabi na dare, sai ya sake tambaya ta, ina
Sardauna yake, nace musu, tun da yamma da muka dawo daga Hamdala ban mu sake
haduwa ba.
Su uku ne, sojojin, sai daya daga
cikinsu yace, sun bani dakika biyar na fada musu inda Sardauna yake ko su kashe
ni. Sai nayi karfin hali, nace musu, kuna iya kashe ni idan kun so, sai suka kyale
ni suka shiga cikin gidan suna neman dakin da yake, a lokacin nan sun duba ko
ina basu ganshi ba, daga nan suka shiga sashin da iyalansa suke, suka fito da
su waje, suna tambayarsu ina Sardauna yake, ana haka, sai iyalan Firimiya suka
garzayo inda nake suka hadu da iyalina. Sai kawai muka fara jin sojojin suna
harbi ratata, na kirga harbi yakai sau goma, daga nan suka budewa dakina wuta a
zaton su Firimiya yana ciki, suka karya Kofa suka shiga, suka farfasa gilasai,
suka birkita dakin amma basu ga Firimiya ba. Daga nan sojojin suka shiga harbin
kan mai uwa da wabi, anan ne fa, iyalin Firimiya suka shiga kururuwa, Inno
matarsa, tana ta cewa, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, daga nan, sai daya
matar tasa Hafsatu ta hango Firimiya sanye da doguwar Jallabiya kansa babu hula
yana tsaye, sai tayi sauri ta mika masa mayafinta, ta ce ya lulluba yayi basaja
ya gudu. Sai Firimiya yace mata, ba zai saka ba, ai shi suke nema kuma gashi.
Nima na tashi da sauri na karasa inda Firimiya yake, na kamo hannunsa, amma ina
ya dage.
A lokacin nufi na shi ne, na kamo shi,
na jashi zuwa dakina na b'oye shi, tunda sun tabbatar baya ciki, amma ina da
wani yayo harbi sai na wuntsula na bar Firimiya a tsaye. A lokacin sojojin suka
kashe wutar gidan gaba daya, sai Inno ta taso a guje dan ta zo inda Firimiya
yake, ashe wani soja ya hango ta, kawai sai ya biyo ta a baya, yana fadin, Ina
Sardauna yake, jin haka sai Firimiya yayi magana yace gani nan, Allahu akbar!
Anan wajen Ajalinsa ya sauka, Firimiya yana tsaye kusa da wani makewayi,
matarsa Hafsatu ta rukunkumeshi, sojan kuwa, fadi yake ta sake shi ko ya bude
musu wuta gaba daya, amma ina Ajali yayi kira, bata ko saurare shi ba. Ta
gayawa sojan ka kashe ni tare da shi, daga na kuwa bai yi wata wata ba ya bude
musu wuta su biyun, akan idona, Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto aka kashe shi
tare da matarsa Hafsatu a lokacin. Karfe 4 na asubahi tayi, na suma da ganin
gawar Firimiya tare da matarsa a gabana. Kun ji yadda sojoji suka kashe Sir
Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa a Kaduna ranar 15 ga watan
Janairun 1966. Allah ya jikansa yaji gafarta masa.
DAGA ADAM M. ADAM
Sunday, April 22, 2018
KALAMAN SOYAYYA 01
KARANTA KAJI YADDA ZAKA TSARA BUDURWARKA
Zuciyarki ta zama takarda, tawa ta zama
biro in rubata miki shafin kauna !
Kizama kofa na zamao
makulli, mu hadu mu bude kofar soyyar lambun zuciyata!
Na kasa tsaye na kasa
zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro , kin fita daban
kaman wata a daren sha biyar!
Ya madarar zuciyata,
ki zamo ciminti in zamo bulo mu gina gidan quana a filin soyayya.
Watau yau da na tashi, sai
na ga rana ta taso ta haske garin nan, amma duk hasken ta ba kai hasken fuskar
da haske zuciyata,domin ni a zuciyata Hasken fuskar abun quana ta yafi duk
hasken raina
Ki zama petur na zama inji
mu hadu mu taa da lantarkin qauna
ya shiba ta na baki filin
zuciya ta ki shuka a duk wani lungun da sako bushiyar so a kauna don mu sami
inuwar da zamu zauna muyi soyayya.
Kece madubi abar dubawata
duk safiya, kin zamo min tamkar fetur a mota, rayuwat ba ke lami ce ya rabin
raina.
Ke ce makwarariyar madarar
zuciyata, wadda da na sha za ta haska ka zuciyata ta yi fari.
Rayuwata babu ke tamkar
wayar da ba wayar shaji ce, kuma babu layi, a mace ba amfani.
Kunne ya kurmance saboda
rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya daina magana dai dai saboda
rashin begen zumar rayuwata kullum.
Ta tsagwaron zallar tsabar
kwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda rashin ganinki a yau da kullum
Ya gangariyar madarar zumar
da bata da gauraye, ya tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske zuciyar
masoyinta.
Idona ya bude ya ga haske
irin na walkiya don ya gan ki. Ziciyata na shan lawgadar zuma da madarar kauna
Idon basira lafazin
rayuwata
Alfijir na quana ya keto,
tsuntsayen soyayya sun tashi su na yayo a sararin samaniyar zuciyata
Ya fankar da ke juya
zuciyata, zan zamo kwale kwale ki shigo bu hau kan kogin so, in zamo katifa ki
zamo gado a cikin dakin kauna.
Hadarin begen ki ya hado,
guguwar sonki ta taso, sai ruwa mai karfi ake yi na kaunar ki a filin zuciyata.
Gaisuwa daga kamfanin so,
harabar kauna, gida mai lambar zuciyata layin begen ki, zuwa ga rabin rayuwata.
ya zare da allurar da ta
dinken zuciya ta, bazan taba daina sonki ba har sai wutar lantarki ta zauna a
nijeriya.
ya majaujawar zuciya ta,
zan zama guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu cikin rijiyar soyayya
Ya tsokar zuciya ta, zan so
ace ki zama fura in zama nono mu hadu a kwaryar soyayya
Ya sahiba ta ki zama
fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu ta da tsuntsun soyayya.
Ya masoyiyata, ki zamo
bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar
da ke.
Ya masoyiyata, ki zamo
hanta in zamo jini, muga mai raba mu.
Ludayin kaunar ki ya mamaye
min kokon zuciyata.
Ya masoyiyata, ki zamo mai
in zamo alabasa mu hadu mu soye juna.'.
a masoyiyata, ki zama
candir in zamo ashana, ku zamo itace in zamo makamaci mu hadu mu hura wutar so,
domin mu mu tafasa tukunyar kauna.
HMM, DAGA ADAM M. ADAM GAYA
Saturday, April 21, 2018
SHAWARWARI 60 GA MAZA
SHAWARWARI 60 GA
MAZA MASU AURE
Shawarwari guda 60, ga masu gida domin
samun zamantakewa mai inganci, da zama miji na gari.
1.ciyarwa gwargwadon iko.
2.tufatarwa daidai iko.
3.shayarwa.
4.kayan kwalliya.
5.kayan tsafta.
6.gurin kwana.
7.kula da lafiya.
8.hakkin saduwa.
9.ilmantarwa.
10.girmamawa.
11.mutuntawa.
12.tausasawa.
13.yabawa ga abinci ko kwalliya ko tsafta.
14.nuna damuwa da ita.
15.sakar mata fuska da murmushi.
16.gaya mata kalmomi masu dadi na yabo.
17.zama hira da tattaunawa da ita.
18.kiranta da suna mai dadi.
19.yawan yi mata kyautar ba zato ba tsammani.
20.fita unguwa ko taro ko ko tafiya da ita.
21.taimaka mata aikin gida ko dan kadan.
22.bata damar zabin abincin gida a wasu lokuta.
23.bata damar zabin tufafin da zata sauya.
24.mutunta iyayenta da danginta.
25.A bata hakuri idan anyi mata ba dai dai ba.
26.A yaba mata idan tayi daidai.
27. kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.
28.banda duka.
29.banda zagi.
30.banda saurin fushi.
31.ka zama miji mai tsafta.
32.ka zama miji mai kula da goge baki.
33.miji mai kwalliya.
34.miji bamai almubazzaranci ba.
35.miji bamai mai kwauro ba.
36.miji bamai shan taba ba.
37.miji bamai mai shan giya ba.
38.miji bamai yawon dare ba.
39.miji bamai neman mata ba.
40 Kada ka zama miji mai hira da wasu mata a gaban iyalansa.
41.miji mai yawan fada.
42.kada ka zama miji mai kauracewa shimfidar iyali.
43.kada ka zama miji mai nuna rashin damuwa da halin da iyalansa suke ciki.
44.kada ka zama miji mai tsananin kishi.
45.kada ka zama miji mai yawan zagi.
46.ka nuna wa matarka cewa gamsu da yanayinta.
47.ka bata dama ta fadi raayinta.
48.kayi shawara da ita akan harkokin gida da wajen cikinta.
49.ka dinga sumbatar ta daga lokaci zuwa lokaci.
50.yin wanka tare a wasu lokuta.
51.rera mata waka da kirari.
52.yin wasa da guje-guje.
53.kada ya zama miji mai zargi.
54.kada miji ya zama mai mugunta.
55.kada miji ya zama mai kushe.
56.kada miji ya zama mai bakin ciki da abinda iyalansa suke dashi.
57.kada miji ya zama mai ragwanci.
58.mijin ya zama mai lafiya wajen biyan bukatar aure.
59.miji ya zama mai kaunar yayansa.
60.miji ya zama mai girmama kawaye da aminan matarsa

MU duba abubuwan nan 60 wanda muke yi na
kirki mu kara ,wanda mukeyi na rashin kirki mu dena,
Allah ya bamu ikon rike iyalan mu da kirki da alkhairi. Ameen, Daga Adam M. Adam Gaya.
Allah ya bamu ikon rike iyalan mu da kirki da alkhairi. Ameen, Daga Adam M. Adam Gaya.
Thursday, April 19, 2018
TAKALMI MAI NA'URA NEW TECHNOLOGY
TAKALMI
MAI NAURAR ZAMANI
Yanzu muna karni na 21 karni mai dauki da abubuwan mamaki da dama, da Allah s.w.t yakaddaremu da gani,
Kamfanin 'Virgin America' sun kir_kiri takalmi (shoes) na zamani, a karon farko a cikin duniyar kamfunan fasahar kere_kere,
Takalmin ankerashine da farar fata mai kyau ta zamani kuma yana dauki da abubuwa, ga kadan.
A iya bincikenmu da mukayi mun gano abubuwa kadan daga cikin abubuwan da takalmin ya kunsa:- hmmm kuna tare da Adam M. Adam Gaya. AHA zakuci karshen zancen.
'
=Yana dauki da TV
=Wurin cajin waya (U.S.B)
=Harda yanar gizo (INTERNET)
=Kai hardama wifi (WIRELAN)
'
A cewar su kimanin kudin takalmin yakai $4,950, a yanzu kwatancin miliyan daya da dubu dari biyar na naira a kudin kasarmu ta gado wato........NIGERIA. N1,500,000.00.
'
Daya daga cikin masu zanin takalmin wato 'mr mike mckay' yace "suna ganin wanan fasahar zata samu karbuwa ganin babu kamfanin da yataba yin wanan fasaha,
by Adam. M. Adam Gaya.

MALICIOUS SOFTWARE
MALICICIOUS SOFTWARE
Wannan suna ne da ake bayar wa ga duk wani
irin manhaja (software) wanda ba'a buƙatar
kasancewar sa a cikin Na'urar komfiwta ko wayar
salula ko makamantan su, sannan kuma irin
waɗannan manajojin sun kasance sun kasance
suna da ikon da zasu lalata Na'urar tare da
dakatar da gudanar Na'urar ko kuma dai ya
samar da wani yanayi mara ɗaɗi ga Na'urar.
Irin Manhajojin akan iya sanya su cikin Na'urar
ka ta hanyar yardarka ko kuma ba da yardarka
ba, (wato ta hanyar yi ma ka Basaja), sannan
kuma irin waɗannan manhajojin zasu iya yaɗa
kansu daga wata Na'urar zuwa wata Na'ura
daban ko kuwa dai a'a. Hmm kuci gaba da sauraro dai

kuna tare da Adamu Mahadi adam Gaya
MALWARE: wannan kuwa suna ne wanda ake
faɗawa kowacce irin manhajar da ba'a buƙatar
kasancewar su a Na'ura. Wannan kuwa ya shafi
irinsu; Virus, spyware, worms, Trojan da dai
sauransu.
MALWARE: wannan kuwa suna ne wanda ake
faɗawa kowacce irin manhajar da ba'a buƙatar
kasancewar su a Na'ura. Wannan kuwa ya shafi
irinsu; Virus, spyware, worms, Trojan da dai
sauransu.
AHA
IRE-IREN MALICICIOUS SOFTWARE.
:::VIRUS: wasu nau'in rubutu ne iri-iri wadda
suke yaɗa kansu daga wata Na'urar zuwa wata
ta hanyar sajewa da wata fail (file) domin ya
samu damar shiga Na'urar ka a ɓoye.
Su waɗannan nau'ikan rubutun da suke a
matsayin VIRUS sukan lalata fail ne (file) da yake
Na'urar komfiwtar duk wanda aka turawa, ko
kuma su hargitsa waɗannan fail (file) ɗin domin
amfanin wanda ya tura.
MENE NE AMFANIN SU IRIN WAƊANNAN VIRUS
ƊIN GA MASU ƘIRƘỊRANSU, MA'ANA WANI AMFANI
MAƘIRƘIRIN YAKE SAMU IDAN YA KIRKIRE SU ?
A Duk lokacin da mai kirkirar irin waɗannan
VIRUS ɗin ya ƙirƙire su to sai ya watsa su a kan
iska wato NETWORK (WIRELESS MEDIUMS), idan
wani ya buɗe Bluetooth nashi ko kuma ya sauƙe
(DOWNLOADING) wani fail (file) to sai su irin
waɗannan VIRUS ɗin su saje da waɗannan fail
ɗin domin su samu damar shiga Na'urar
komfiwta ko wayar ka don lalata ta.
To su kuwa waɗanda suke ƙirƙiro su sai su kirkiri
wata Manhaja wadda zata iya goge wannan
VIRUS ɗin sannan su kai shi kasuwa domin
sayarwa (COMPUTER WAREHOUSE) to a lokacin
mutane su rinƙa zuwa suna sayo wa.
To kaga wannan shine ribar da suke samu. Daga Adam Mohd Adam Gaya.

Wednesday, April 18, 2018
WITH US
ASSALAMU ALAIKUM
ALHAMDULILLAHI
Sunana Adamu Mahadi Adam Gaya, Ina Godiya Ga Allah S.W.T da yabani damar kirkirar wannan website mai albarka ayau ranar laraba 18th April, 2018.
Sannan kuma ina yiwa dukkan mabiya wannan shafi barka da zuwa da kuma fatan Alkahiri. Nagode.
Ina Mika godiya ga "yan uwa da abokan arziki akan shawarwari da aka bayar akan wannan shafi, irinsu:
Yeemi Solomon, , Aisha Abdullahi, Abdulkadir Ali Amin, Muhammad Hassan, Umar Bello sunusi, Umar Auwalu, Adamu Umar Maitama, Umar Asheer Bala, Ibrahim Mustapha, Abdurrashid Abdulmumin, Rufa'ee Mustapha.
Subscribe to:
Posts (Atom)