TARIHIN HAUSAWA: DAGA ADMIN: Adam M. Adam
Addinin Gargajiya da Hanyoyin Yada Labarai da
Kayan Sawa da Al’adu da Sana’o’i da Muhalli da
kuma Tattalin Arzikinsu
Asalin Hausawa abu ne da aka sha kuma ake
kan tambaya a kullum, sai dai abin takaici har
yanzu ba a sami wata cikakkiyar amsa mai
gamsarwa ba. Kafin mu yi nisa ya kamata mu
san ko su wane ne Hausawa. Hausawa dai su
ne mutane wadanda harshensu shi ne Hausa
sannan dukkan al’adunsu na Hausa ne. Haka
kuma addinin musulunci ya yi cikakken tasiri a
kansu.
Mutane dabam-daban sun yi bincike sosai a kan
ilmin harsuna da abubuwan da aka kattaba da
kuma zantukan baka. Ta hanyar irin wannan
bincike ne aka gane cewa wadansu harsuna suna
da kama da juna ainun, wanda ya haifar da kara
zurfafa nazarce-nazarce. Sakamakon haka ne
kuwa aka karkasa harsunan Afrika ta yadda
kowane kaso ya kunshi harsuna wadanda bisa
dukan alamu tushensu guda. Ma’ana a asali su
wadannan harsuna harshe ne guda daya wanda
wasu dalilai irin su bambancin wurin zama,
sanadin kaurace-kaurace da yake-yake da dai
wadansu dalilai suka sanya ya karkasu ya
kasance harsuna iri-iri a halin yanzu.
Akwai dangunan harsuna da dama a cikin Afrika.
Misali akwai dangin Bantu a can wajen tsakiyar
Afrika wadanda tushensu duka daga wani tsohon
harshe ne wai shi Bantu; akwai kuma dangin
Kwa wanda ya kunshi Yarabanci da Ibo da
Nupanci da dai sauransu. Ita kuwa Hausa tana
cikin harsunan iyalin Cadi. Ko da yake shi
wannan harshe babu shi a yanzu, wannan suna
na Cadi suna ne kawai da masana ilmin harsuna
suka kirkiro. Dalili kuwa shi ne yawancin iyalin
wannan harshe ana samunsu a farfajiyar tafkin
Cadi. To saboda rashin sanin ainihin sunansa sai
aka kira shi da sunan Cadi. Harsunan iyalan Cadi
suna da yawa. Akwai Angas da Bacama da Bade
da Bolanci da Bura da Hausa da Kanakuru da
Karekare da Mandara da Margi da Miya da
Ngizim da Tera da dai sauransu. A sakamakon
kamanni da wadannan harsuna suke yi da juna
ya sanya aka danganta su ga tushe guda.
A bisa wannan dan bayani muna iya cewa
Hausawa da harshensu sun fito ne daga cibiya
daya da sauran harsunan iyalin Cadi. Wannan
kuwa zai ba mu damar cewa mutanen da suka
zama Hausawa sun fito ne daga Gabas ko arewa
maso gabas da wurin da suke a yanzu
Daga nan sai mu duba abubuwan da aka
kattaba. A nan an samu mutane dabam-daban
sun yi rubuce-rubuce a kan asalin Hausawa da
harshensu. A wani littafi da ya wallafa a kan
Daular Usmaniyya, Johnston ya bayyana cewa a
tsakanin shekarar 1050 zuwa 1100 ta Miladiyya
wadansu, Berbers, (Buzaye) sun ratso sahara
suka zauna cikin Tukururu kuma suka yi
auratayya da su. Wai a sanadin wannan cudanya
ne aka sami Hausa da harshen Hausa.
Shi ma wani marubucin dangane da tarihin
Hausawa da harshensu, M.G. Smith, yana da
ra’ayi kusan iri daya da na Johnston. Wato ya
amince da cewa akwai kaura da ta auku daga
gabas zuwa kasar Tukururu, wanda ya yi
sanadin samuwar Hausawa da harshensu. Ya
kare da cewa wannan kaura ta auku ne wajajen
shekarar 1350 ta Miladiyya.
Shi kuwa Abdullahi Smith nuna rashin
amincewarsa ya yi da wannan bayani da aka yi
dangane da asalin Hausawa da harshensu.
Musamman ma cewa wai nan da shekara dubu
da suka wuce babu Hausawa. Shi yana ganin
cewa kasa rarrabewa tsakanin asalin Hausawa
da harshensu da kuma asalin daular mulkin da
suka kafa shi ne dalilin rashin fahimtar. Haka
kuma bai amince ba da cewa Hausawa sun samu
a sakamakon auratayya tsakanin Berbers
(Buzaye?) da kuma Tukururu da suka taras a
wurin. Hasali ma ra’ayinsa ya fi karkata ga cewa
Hausa tana da alaka da harsunan iyalin Cadi, har
hakan ma kuwa yana ganin cewa sun raba hanya
shekaru dubbai da suka wuce.Ya kuma kara da
cewa mai yiwuwa da can akwai dangantaka
tsakanin harshen Berber da na Cadi, wato tun
kafin Sahara ta zamo hamada.
Babu shakka ba abu ne mai karbuwa ba a ce
nan da shekaru 950 da suka wuce babu
Hausawa da harshensu, musamman idan aka
dubi tarihin garuruwan Hausa da jerin sarakunan
da suka mulke su. Misali an ce tun karshen
karni na 9 na Miladiyya wadansu maharba suka
zo suka zauna a duwatsun da ke kewaye da
sararin da ake kira Kano yanzu. Idan haka ne
wannan ya nuna cewa akwai Hausawa a wannan
wuri fiye da shekaru 1,000 da suka wuce.
Addinin Gargajiya na Bahaushe
Adinin gargajiya wata hanya ce ta bautar da
mutane dabam-daban kan sama wa kansu.
Babu wata kabila da za ta bugi kirji cewa ita ta
koya wa wata bauta wa (Ubangiji). Kusan
kowace kabila nan take take ta kago hanyoyin
bautarta. Wadannan hanyoyin bauta ana ganin
sun samu tun farkon samuwar dan’adam. Masu
binciken tarihi na ganin cewa makasudin bautar
gumaka shi ne ganin cewa wasu abubuwa kamar
rana da wata da kogi ko duwatsu suna yi dabi’a
irin ta mutum wato in an faranta musu rai su ji
dadi in kuma an bakanta musu su yi fushi. Masu
bauta wa kogi ana ganin sun yi imani da shi ne
saboda ganin cewa wani lokaci sai ya yi
ambaliya su sami amfani mai yawa, wani lokaci
kuma ya bushe. Daga ya bushe sai masu bautar
su dauka cewa sun yi wani laifi ne, sai a sami
wani babbansu ya kasance mai yin magana da
gunkin, shi kuma zai rika gaya musu sakon
gunki. Makasudi na biyu da ake zaton ya sa
mutane yin bautar gunki shi ne ta wajen ciwo.
Wani lokaci ciwo kan kama mutum a yi ta
magani a rasa yadda za a yi ciwon ya warke.
To, in aka yi katari wani ya zo ya ba da magani
majinyacin ya warke, sai a dauka cewa wannan
mutumin yana da wata daraja ta musamman.
Saboda haka duk abin da ya faru, shi za a dosa,
shi kuma ya rika dangana cuce-cucen da iskoki.
Ta nan ne sai mutane su yi imani da iskoki.
Tun da yake za a yi magana ne a kan addinin
gargajiya na Bahaushe, ya kamata a dan
bayyana wasu misalai na tsafe-tsafen Hausawa
a lokacin da suke yin Maguzanci da kuma
barbashin tsafe-tsafen har zuwa yau. Amma tun
da ba Bahaushe ne kadai yake yin irin wadannan
tsafe-tsafe ba, za a bayar da takaitaccen misalin
bautar gumaka a wasu kasashen. Misali a kasar
Masar suna da nasu gumakan kafin zuwan
musulinci, sanannu daga cikin gumakan su ne
Ra da Osiris. Ra shi ne gunkin rana shi kuma
Osiris shi ne mai kula da kogin Nil, kogin da shi
ne kashin bayan rayuwar mutanen Masar. Idan
muka matso wajen makwabtanmu za mu ga
cewa Ashanti na kasar Ghana su ma suna da
sanannen gunkin da suke kira Abosomi.
Yarabawa kuma suna da Orisha. Orisha din nan
shahararren gunki ne wanda Yarabawa ke wa
bauta sosai. A duk lokacin da suka ga wani abu
ba ya tafiya daidai, sai manyansu su kai
kukansu ga wannan gunki. Daga nan sai a yi
yanke-yanken dabbobi don Orisha ya sha jini. Da
an ga wani canji sai a dauka cewa Orisha ya
yarda. Mutanen Jukun ma suna da nasu gunkin
da suke kira Jo. Barebari kuma na da nasu
gunkin da suke kira Sanama. Kabilar Tangale da
ke Bauchi ma ba a bar su a baya ba wajen
bautar gumaka, suna da babban gunkinsu da
suke kira Yeku. Ban da babban gunki Yeku akwai
kuma kananan gumaka a kowane gida da ake
bautawa, haka kuma a kowace unguwa.
Daga wadannan bayanai da aka yi za a fahimci
cewa addnin gargajiya ya mamaye kasashe da
yawa kafin zuwan addinin Almasihu da na
musulunci. Kuma kusan kowane irin addinin
gargajiya, sai an sami wani mutum wanda shi ne
mai wucewa gaba don nemo bayani daga gunkin
sa’annan ya sanar wa da mabiya.
Tun da yake an dan ji bayanan addinan gargaji
na wasu mutane, sai kuma mu tsunduma ga na
Hausawa. Hausawa ma kamar sauran mutane
suna da addininsu na gargajiya tun kafin zuwan
addinin musulunci. A gaskiya ba wanda zai ce ga
lokacin da Hausawa suka fara bautar gumaka da
tsafe-tsafe. Tarihi ya nuna cewa tun da aka
halicci dan’adam, bautar iskoki ta cusu a
zuciyarsa. Wannan shi ya sa yake da wuya a
bayyana tun sa’ad da abin ya fara. Dalilai na
biyu da ake jin su suka haifar da addinin
gargajiya, ba kuma ga Hausawa kadai ba har ma
da sauran jinsi iri-iri na duniya. Dalili na farko
shi ne, shi dai dan’adam ya dauka cewa kowane
abu a duniya yana dabi’a irin tasa, wato wani
lokaci zai ji dadi musamman in an faranta masa
rai, ya kuma ji zafi in an bakanta masa, har ya
kai ga ramuwar gayya. Alal misali, lokacin da
Kanawa ke bautar Tsumburbura a gindin Dala,
zamanin Barbushe, duk shekarar da ta zo da
wani bala’i sai mutane su dauka cewa lallai an
saba wa Tsumburbura. Saboda haka sai a yi
yanke-yanken awaki da karnuka don dodon ya
sha jini wai ko ya huce. To wasu lokutan kuwa
sai a yi sa’a abin ya yi sauki shi ke nan sai a
dauka wannan sauki ya faru ne saboda yanke-
yanken da aka yi wa gunkin ne.
Dalili na biyu da ake zaton shi ma ya taimaka
wajen kago bautar gumaka shi ne ciwo. Sau da
yawa akan sami ciwo ya ki ci ya ki cinyewa ga
mutum, a yi ta neman magani, amma a banza,
sai a dauka ba mai warkar da majinyacin sai dai
mutumin da Allah ya yi wa wata daraja ta
musamman. Ana nan har a sami wani boka ya
nuna cewa iska kaza ce ta taba mutum amma
shi zai warkar da shi. Idan aka yi katari sai
kuwa mutumin ya warke. Da zarar haka ta faru
fa sai mutane su yi imani da wannan iska da
boka ya ambata, shi kuma boka kasuwa ta bude
ke nan.
Ana yin bauta ta hanyoyi dabam-daban. Wasu
sukan sassaka gunkinsu da kansu, su yi wani
mutum-mutumi su rika bauta masa. Wasu kuma
sukan bauta wa iskokai.
Dangane da bautar gumaka wajen Hausawa, su
ba sa sassaka gunki don yi masa bauta, a’a, sai
dai bautar iskokai ta hanyar bori. Kanawa suna
bautar Tsumburbura a dutsen Dala.
Akwai wasu gumaka makamantan wadannan a
wasu wurarae a kasar Hausa. A kasar Katsina,
akwai mutanen Kainafara, arnan Birci a kasar
Dutsin ma, masu bautar wani gunki mai suna
Dan talle. Sunan mai kula da wannan gunki shi
ne Sarkin Noma. Kamar Barbushe Sarkin Noma
shi ne mai ba da labarin sakon da Dan talle ya
yi ga mabiyansa. Su ma mabiyan Dan talle
kabilar Kainafara na yin bikinsu ne shekara-
shekara kuma suna yin yanke-yake kamar dai
mutanen Barbushe.
Akwai kuma wasu maguzawa masu bautar wani
gunki mai suna Magiro a dutsen Kwatarkwashi a
cikin jihar Sakkwato. Mai kula da tsafin shi ne
Magajin Ranau. Shi ma ana yi masa yanke-
yanke kamar yadda ake yi wa Tsumburbura sai
dai su bakin sa ake yanka masa ko bakar akuya.
Bayan wadannan gumaka kuma, Hausawa
Maguzawa kan yi tsafe-tsafe na gida. Misali shi
ne, kusan kowane Bamaguje ya ajiye wata
halitta wadda ya dauka ita ce kan gidansa. Wasu
sukan dauki dabbobi kamar damisa, kura ko
zomo ya zama kan gidansu. Duk abin da aka
dauka ya zama kan gida to ba hali wani dan
gidan ya ci namansa, ko ya kashe shi ko kuma
ya cuce shi ko ta wace hanya.
Tasirin Addinin Gargajiya
A halin da ake ciki yanzu, ko da yake mafi
yawan Hausawa sun karbi addinin musulunci
hannu bibiyu, har ma ta kai fagen da an ambaci
sunan Bahaushe sai a kawo addinin musulunci
ciki, don ganin cewa Hausa da musulunci sun
kusa zama abu daya duk da haka akwai
Hausawa wadanda har yanzu tasirin addinin
gargajiya bai bar su ba. Sanin kowa ne cewa har
yanzu akwai Maguzawa a kasashen Kano da
Katsina wadanda ba su daina yin tsafi da bautar
gumaka ba. Wadannan Maguzawa har yanzu
sukan yi bukukuwa da tsafe-tsafe iri-iri. Ta
hanyarsu ne wasu Hausawan musulmi kan nemi
taimako wajen dodo don neman biyan bukata.
Irin wannan da’awa ta sa na sami wani tsohon
Bamaguje a Jammawa ta kasar Dawakin Tofa
wanda ake kira Zuga don ya tabbatar min ko
Hausawa musulmi sukan nemi taimako a
wurinsu, Zuga ya bayya min cewa a matsayinsa
na makeri, ya sha karbar ziyarar makera
Hausawa kuma musulmi wadanda suke zuwa
wajensa don neman taimako kan yadda za su
sarrafa wuta. Ya ce yakan fayyace musu fa lallai
sai an kauce kuma sun yarda suna kuma bin
dukan abin da ya nuna musu na game da tsafi.
Haka kuma na sadu da wani dattijo a wani
kauye mai suna Katsardawa ita ma a kasar
Dawakin Tofa take. Shi wannan Bamaguje
sunansa Girbau kuma gawurtaccen manomi ne,
ya bayyana min cewa ya ba mutane da yawa
Hausawa kuma musulmi asirin dodo don kawai
su tara hatsi da yawa.
Idan muka juyo ta fannin bori (wanda al’ada ce
ta Maguzawa masu bin addinin gargajiya), za
mu ga cewa har kwanan gobe Hausawa musulmi
suna yi kuma duk mai yi ya ba da gaskiya.
Hanyoyin Yada Labarai Na Hausawa
Hanyoyin yada labarai abubuwa ne da suke
tattare da kowacce al’umma, kamar yadda
Hausawa kan ce ‘tun ran gini tun ran zane’.
Hanyar yada labarai hanya ce tsararriya da ake
bi domin isar da sako ga daidaiku ko kuma
jumlar mutane ba tare da wani tarnaki ba. Babu
shakka hanyar yada labarai ta dade a cikin
al’umma amma, tun tuni, mun dade a kasar
Hausa muna da tsarin isar da sako ta hanyar
yekuwa ko shela da sankira yake yi domin
fadakarwa ko sanarwa ko kuma nusarwa ga
mutane ko ilmantar da su dangane da wani
muhimmin abu da ya shafi rayuwarsu. Irin
wannan yekuwar (shela) tana daga cikin tushen
kafafin yada labarai a kasashen Afrika,
musamma ma kasar Hausa.
Kayan Sawar Hausawa
Hausawa a da can ba su da wata sutura da ta
zarce warki sai kuma ganye, amma zuwan
addinin musulunci kasar Hausa ya canza
rayuwarsu ta hanyoyi da dama, misali, ko wajen
sutura ma musulunci ya canza tsarin adon
Hausawa, zuwan Larabawa da wasu kabilun
Masar suka kawo wa Hausawa suturu masu rufe
al’aura, kamar su riga ’yar Tambutu da jabba da
Kaftani da Kubta da wanduna iri-iri da hular
dara. Aka kuma tanadar wa mata zane (gyauto)
da mayafi (gyale) da dankwali da riga. Saboda
samun irin wadannan suturu su ma Hausawa
suka kago irin nasu suturun don maza da mata
kamar ’yar-shara da taguwa da aganiya da
fatari da bante. Wasu sun ce bante Hausawa sun
aro shi daga wajen Nufawa ne.
Ire-iren Suturun Da Hausawa Suke Amfani Da Su
Luru, Gwado-babbar kwarya da karamar kwarya
Babbar riga da ’yar ciki-gari
Shakwara da jamfa da wando
Doguwar riga
Launukan Babbar Riga
Gari da Sace da Shakwara da Aganiya- akwai
wadanda ake yi musu ado a ba su wasu sunaye:
Kamar Aska tara mai cibiya da Aska takwas
malummalun da Aska biyu mai wau da Girke da
Girken Zazzau da Girken Nufe da Sace mai adda
da Sace mai gafiya.
’Yar Tambutu da Doguwar riga da Fanjama da
Hartin da Jallabiyya da Zuleka da Kaftani
’Yar ciki dahariya da ’Yar shara da Zuhuni da
kuma Falmaran
Wanduna
Tsala da Fanyama da Bulus da Dan itori da
Dantunis mai kamun kafa da kuma Kwarjalle.
Huluna
Dankwara da Bakwala da Damanga da Habar
kada da Facima da Zanna da Kube da kuma Zita
Rawani
Harasa da Bakin fara da Dankura da kuma
Mubarrashi
Takalma
Dangarafai da Sambatsai da Fade da Mai gashin
jimina da Dan Maroko da kuma Huffi.
Zanin Mata
Saki da Bunu da Bakurde da Gam Sarki da
Tsamiya da Dantofi da Fatari da Saro da kuma
Mukuru
Sana’o’in Hausawa
Kasuwaci da Fatauci da Saka da Rini da Farauta
da Jima da Noma da Kiwo da Kira da Sassaka
da Dukanci da Gini da Fawa da kuma Wanzanci.
Muhalli
Bukka da Tsangaya da Dakin Hayi da Shigifa ko
Soro da Kudandan ko Rudu da kuma Kago.
Al’adun Hausawa
Hausawa mutane ne musu tsananin rikon
al’adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi
da abinci da al’amuran da suka shafi aure ko
haihuwa ko mutuwa da sha’aninmu’amala
tsakanin dangi da abokai da shugabanni da
sauransu, da kuma al’amuran sana’a ko
kasuwanci ko neman ilmi.
Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna
cikin al’ummomin da ba su saki tufafinsu na
gargajiya sun ari na baki ba. Galibin adon namiji
a Hausa ba ya wuce riga gari da wando
musamman tsala, da takalmi fade ko kafa-cik,
da hula kube, ko dankwara, ko dara. In kuma
saraki ne ko malami ko dattijo, yakan sa rawani.
Adon mata kuwa, zane ne da gyauton yafawa,
wato gyale da kallabi da taguwa da ’yan kunne
da duwatsen wuya wato tsakiya.
Yawancin abincin Hausawa kuwa, ana yin sa da
gero ko dawa ne. Sai kuma sauran abubuwan
hadawa, da na marmari, kamar su wake da
shinkafa da alkama da kayan rafi da sauransu.
Yawancin Hausawa Musulmi ne saboda haka
yawancin al’adunsu da suka shafi aure da
haihuwa da mutuwa duk sun ta’allaka ne da
wannan addni, sai dan abin da ba a rasawa na
daga al’adun gargajiya musamman a wajen
Maguzawa.
Haka kuma wajen mu’amala da iyaye ko dangi
ko abokai ko shugabanni ko makwabta ko wanin
wadannan, yawanci na Musulunci ne. Haka nan
sha’anin sana’a da kasuwanci da neman ilmi duk
a jikin Musulunci suka rataya..
Da can, sana’a da kusuwanci da neman ilmi suna
bin gado ne, wato kowa yana bin wadda ya gada
kaka da kakanni. Kuma idan mai sana’a ya shiga
bakon gari zai je ya sauka a gidan abokan
sana’arsa ne. In ma koyo ya zo yi, zai je gidan
masu sana’ar gidansu ne. Saboda haka kusan
kowace sana’a akwai sarkinta da makadanta da
mawakanta, kai har ma da wasu al’adu na musa
yinta da suka sha bamban da na sauran jama’a.
Tattalin Arzikin Hausawa
Kalmar tattali tana nufin kula ko ririta ko tanadi
da kula ko adana wani abu, wato tsiminsa. Ita
kuwa kalmar arziki a nan tana nufin tajirci ko
dukiya ko samu ko hali ko gafi ko kudi ko sukuni
ko daula ko wadata ko abin hannu wato mllakar
dukiya mai yawa fiye da sauran abubuwan
bukata.
Daga wadannan bayanai za a ga, a ma’ana ta
gama-gari, tattalin arziki yana nufin kula da
dukiya. A fagen nazari kuwa, tsari ne na sarrafa
al’barkatun kasa da sauran ni’imomin da Allah
ya yi wa mutum, yadda za a samar da
muhimman abubuwa da dan’adam yake bukata
a kuma sarrafa su ga jama’a.
Dangane da haka, dan’adam tilas ne ya yi aiki
ya sarrafa wasu abubuwa don ya kai ga biyan
wadannan bukatu, amma kuma mutum bai iya
wadatar da kansa da dukkan bukatunsa, don
haka dole ya dogara da ’yan’uwansa wajen
samun wadannan abubuwa, kamar yadda su ma
suka dogara da shi.
Tattalin arzikin Hausawa na gargajiya abu ne
kara zube inda ake barin abubuwa kara zube,
ma’ana kowa yana ba da gudummawa
gwargwadon karfinsa kuma yana samun
abubuwa gwargwadon irin sana’arsa da
kwazonsa da kuma sa’arsa. Ita kuma hukuma ta
sa ido don tsaron mutunci da dukiyar al’aumma.
Sana’o’i su ne mafi girman tafarkin da Hausawa
suke bi don samar da abubuwan bukata. Ta
hanyar sana’o’i suke sarrafa albarkatun kasa da
sauran ni’imomin kuma rarar da suka samu suke
musanyawa su mallaki abubuwan da ba za su
iya samar wa kansu ba. A takaice dai sana’o’i
su ne kashin bayan tattalin arzikin Hausawa na
gargajiya wadanda suka hada da noma da kira
da wanzanci da fawa da saka da jima da
dukanci da sassaka da rini da dillanci da bokanci
da dibbu da dinki da magori da tuggu da
kwarami da banbadanci da kuma koli da dai
sauran su.
Daga cikin wadannan sana’o’i noma shi gidan
kowa da shi, a gargajiyance duk Bahaushe
manomi ne amma kuma yakan kara da wata
sana’ar don tallafawa. Dangane da haka ne ake
karkasa mazauna gari bisa tsarin sana’o’in
kowane gida ko unguwa, don haka ne ma a Kano
aka sami unguwannin Makera da Dukawa da
Mahauta da unguwar gini da makamantansu.
C.E.O: A.M.A Gaya