Tuesday, April 28, 2020

ABUBUWA GUDA (10) WADANDA ZA SU TAIMAKA WAJEN ZAMA DA MACE LAFIYA.




ABUBUWA GUDA (10) WADANDA ZA SU TAIMAKA WAJEN ZAMA DA MACE LAFIYA.
Imamu Ahmad (RA) ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za su taimaka wajen zama da mace lafiya.
Yace ya kai da Na, hakika ba zaka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da zaka mu'amalanci matarka dasu don haka ka kiyaye su
NA DAYA DA NA BIYU:
Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da kauna
NA UKU: Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakaninku
NA HUDU: Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayinka
NA BIYAR: Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkinsa
NA SHIDA: Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bats zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su
NA BAKWAI: Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankali

BAMBANCI SO DA KAUNA







BAMBANCI TSAKANIN SO
DA KAUNA
Sau dayawa munayin kuskure
muna hada so,da kauna a waje
guda.wanda hakan a wjan
malaman soyayya kuskurene
mai girma.
Ita kalmar ‘SO‘bakaken
hausane guda 2.wato‘S‘da‘O‘
Turawa sukace‘love‘su kuma
haduwar bakake guda 4.
Da yarabanci kuma‘IFE‘
Wannan wata kalmace wadda
ake dafifi akanta,ake iya
mutuwa akanta.
In akace ana sonka to baya
daukar ma'anar cewa ana
kaunarka.dmin shi so ana
furtashi ne akan abinda ya
baka sha'awa.kuma da wanna
abinda ya baka sha'awa zai
zama babu shi,to da aka iya
daina sonshi.
Ma'ana in budurwa tace tana
sonka sboda kudi.to aranar da
baka dashi,wannan kalmar so
din ta kau daga gareka.
amma mutane sun fiya anfani
da ita.
Ita kuma ‘KAUNA‘kalma ce
wadda tafi ‘SO‘wajan yawa da
anfani da juriya.
Domin it kauna duk halin da ya
shiga kaunar nan bazata gushe
ba.
Wato ba yaudara a cikinta.
misali:wanda yake na gaskene.
wanine ana cemar
Abdul~wahab,sun hadu da
wata yarinya a makarantar
scondary,sunanta
maryam.maryam tana bala'in
kaunarsa.duk da cewa halinsa
bamai kyau bane,kuma ba dan
gdan me kudi bane.
sau dayawa akan kamashi da
laifin sata da
makamantansu,amma duk da
haka bata daina kaunarsa
ba.illama kaunar sa ce take
kara shiga jikinta.kaga wannan
kaunace zalla.
Wanda yake kaunar abu baya
ganin bakin abun koda yakai
duhun dare baki.
Don haka mu ringa lura yayin
da muke soyayya,wajan
bam~bam cewa wai kaunarka
ake kokuma sonka ake don
abin hannunka.