Friday, December 28, 2018

TARIHIN ALKAWARIZM


TARIHIN MASANI IMAM MUHAMMAD ALKAWARIZM

Sadiq Tukur Gwarzo

Daga sahun masana da wannan duniyar ta amfana dasu, waɗanda har karsheɓlnta kuma ba za'a iya mancewa da gudunmuwarsu a fagen ilimi ba, akwai Imam Muhammad alkhwarizm.
Cikakken sunansa shine Abu Abdullahi, Muhammad Bn Musa Alkhawarizm AlMajusiyy Al Quɗrubbuliy.
Shi haifaffen tsohuwar daular farisa ne, domin kuwa an haife shine a garin Khiva wanda a yanzu yake cikin kasar Uzbekistan, a shekara ta 780 miladiyyah.
Muhammad Alkawarizm cikakken masani ne a fannin Islama. Yayi karatun sa na addini, daga nan sai ya tsunduma binciken iliman lissalafi, falasifa dana kimiyya. Haka kuma ya shafe tsawon rayuwarsa yana koyarwa a cibiyar ilimin nan data shahara aduk duniya dake birnin Bagadaza, watau Darul Hikmah.
Da yake bayyana kaɗan daga tarihin Alkawarizm, Ibn Naɗim a littafinsa Kitab Al-Fihrist, cewa yayi "Alkawarizm yayi mafi yawan ayyukan sane na ilimi a wuraren shekara ta 813-831, a sa'ar da musulunci ya mamaye daular Farisa, Bagadaza kuma ta zamo cibiyar ilimi wadda har daga birnin Sin ana zuwa gareta neman sani".
Marubucin tarihi Rosen ya faɗa cewar " Al khawarizm ya rayu ne a zamanin Halifancin Al Mamun, kuma shine wanda ya soma warware badak'alar lissafin Algebra a larabce."
Imam Ibn Khaldun ya faɗa a littafinsa shahararee mai suna Muqaddimah cewar "wanda ya fara rubutu akan lissafin Aljabra shine Abu Abdullahi Alkhawarizm, daga baya ne Kamil Shoja ibn Aslam yazo."
Da yake anfi sanin rayuwar ilimi da rubututyukan Imam Muhmmad Alkhawarizm sama da inihin rayuwarsa, amma tarihi ya nuna cewa lokacin da Halifa Harun AlRashid ya zamo khalifa a Farisa a ranar 14 ga watan satumbar shekara ta 786, Alkhawarizm yana yaro kankane ne.
Ance Halifa Harun AlRashid yana da 'ya'yaye guda biyu. Babbansu shine Al'amin, sai kaninsa mai suna Al'Mamun. Da hawan mulkinsa sai ya fara kokarin cika daular musulunci da ilimi, inda ya rinka gayyato masana suna zuwa bagadaza suna koyar da ilimi, sannan ya rinka biya domin kawo tulin littattafan kimiyya dana sauran fannoni daga kasashen girka dana Hindu izuwa daular tasa.
ƁBayan mutuwarsa kuwa sai akace rigimar mulki ta kaure a tsakanin 'ya'yayen nan nasa, inda daga bisani sojojin Al'Mamun suka hallaka Al'amin, suka ɗorashi bisa gadon Halifanci.
Da hawan Al'Mamun, sai ya ɗora akan inda mahaifins ya tsaya, inda ya kammala ginin Darul Hikmah wanda mahaifinsa ya soma, sannan ya cigaba da bautawa ilimi shima.
A wannn lokacin ne kuma gawurtar Alkhawarizm ta fara Fagen ilimi, inda har aka ɗaukeshi a sahun Malumman wannan taska ta ilimi ta Darul Hikmah.
Da yake Alkhawarizm masanin falsafa ne, sai yake kalon ilimi saɓanin yadda wasu ke kallonsa, inda ya jajirce wajen fassara wasu littattafan ilimai daga harshen girkawa izuwa larabci, sannan ya dukufa bincike gami da rubuce-rubuce a fannonin lissafi, ilimin fahimtar alkibla, ilimin kimiyyar sararin samaniya da yanayin kasa dama wasunsu.
Daga abinda har yau ake tunawa dashi shine littafinsa mai suna 'Kitabul Mukhtassar fiy Hisabul Jabr wal Muqabala', wanda daga sunan littafin aka maida Jabr izuwa Algebra, aka kuma ɗauki Lissafin Algorithm duk aciki.
A littafin, masani Al khawarithm ya nunawa musulmai muhimmancin dake akwai wajen koyon ilamai musamman na hisabi (lissafi), tunda acewarsa musulmai na matukar bukatar ilimin a wajen maganar rabon gado, alkalanci, auna alkibla da auna tazarar fili da kasuwanci, kai harma da raba husuma a cewarsa.
Imam Alkawarizm yayi rayuwa mai sauki, cikin koyo da koyarwa. Sannan yayi rubututtuka gawurtattu domin koyar da ɗalibansa.
Shine fa marubucin littafin da yake bada fasali da kwatancen yadda za'a gane inda garin makkah yake daga ko ina a sassan duniya, sannan shine marubucin littafin daya zayyano fasalin birane kimanin 2402 na wannan duniyar. Aannan yayi aiki tukuru wajen zanawa duniya kalandar shekara da gyaran kura-kuran wasu masana. Ance kullum cikin nazarin ilimi yake, kuma yana da saukin kai gashi gwani wajen fahimtar da mai ɗaukar darasi.
Alkawarizm ya rasu a shekara ta 850 miladiyya, yana da shejarau saba'in a duniya. Amman kafin rasuwarsa ya rubuta tulin littattafai, waɗansu sun ɓace, yayinda waɗansu kuma har yau ana amfani dasu.
Daga cikin littattafansa da akwai:-
-Kitaburr Rukhamah
-Ma'arifatu sa'at al mashriq fi kulli balad
-Ma'arifat Al samt min qibal al irtifa'i
-Risalati fi Istikraji Ta'arikhil yahud
-Kitabu Surat Al Ard
-Zinj Al sindihid
-Kitab Al jam wat tafriq bi Hisab Al Hind
-Kitabul Mukhtassar fi Hisabil Jabr wal Muqabalah.
Da wasunsu.
Dafatan Allah yayi rahama a gareshi amin

Sunday, December 23, 2018

KARANTA KAJI

SUNAYEN MATAN MANZON ALLAH (S.A.W)
1.Khadija 'yar khuwailid
2.Saudatu 'yar Zam'atu
3. Hafsah 'yar Umar
4. Aisha 'yar Abubakar
5. Zainab 'yar Khuzaimah
6. Zainab 'yar Jahshin
7. Juwairiyya 'yar Haris
8. Ummu Salama (HINDU)'yar Abu Umayyah
9. Safiyya 'yar Huyayyu
10. Ramlatu 'yar Abu Sufyan
11. Maimunah 'yar Haris
SUNAYEN 'YA'YAYEN ANNABI (S.A.W)
1. Ibrahim
2. Alkasim
3. Abdullahi
4. Zainab
5. Rukayyah
6. Ummukulsum
7. Fadimatu
SAHABBAI GOMA DA AKA YI WA BUSHARA DA ALJANNAH
1. Abubakar Assiddik.
2. Umar Dan Khaddab.
3. Usman Dan Affan.
4. Aliyu Dan Abi Dalib.
5. Dalha Dan Abaidullahi.
6. Zubairu Dan Awwam.
7. Abu Ubaida Dan Jarrah.
8. Abdurrahman Dan Aufu.
9. Sa'adu Dan Abi Wakkas.
10. Sa'idu Dan Zaid.
SHIKA SHIKAN MUSULUNCI GUDA BIYAR
1. Tauhidi.
2. Sallah.
3. Azumi.
4. Zakkah.
5. Hajji.

SUNAYEN WATANNIN MUSULUNCI:
1. Almuharram.
2. Safar.
3. Rabi'ul Awwal.
4. Rabi'ul Sani.
5. Jumada Awwal.
6. Jumada Sani.
7. Rajab.
8. Sha'aban.
9. Ramadhan.
10. Shawwal.
11. Zulkidah.
12. Zulhijji.
.NAFILOLIN DA MANZON ALLAH YAYI KUMA YACE AYI.
Duk wanda ya dabbakasu za'a gina masa gida a ALJANNA.
1) Raka'a 2 kafin sallar asuba
2) Raka'a 4 kafin sallar azahar
3) Raka'a 2 bayan sallar azahar
4)Raka'a 2 bayan magariba
5) Raka'a 2 bayan sallar insha,
Abin ban sha'awa cikin lamarin musulunci shine, duk wanda yatura wannan zuwaga jama'a shima za'a bashi ladar duk wanda
yagani yayi wannan nafilolin.


Friday, December 21, 2018

SARKI SIBANA

 HIKAYAR SARKI SIBANA DA GIMBIYARSA SULBANIYA

Tare da Sadiq Tukur Gwarzo

Ance Sarki sibana wani shahararren sarki ne kuma qasaitacce daga cikin rukunin sarakunan da suka mulki Birnin Andaluz, dadaddiyar masarautar da a wani zamani can daya gabata mulkinta ya kusan game ko ina a sassan duniya.
Shidai wannan sarki, tarihi ya nuna asalinsa baiyi gadon sarauta ba, ba kuma wani Kakkarfan jarumi bane, wannan ne babban abin mamaki alokacin jahiliyya har ace wani wanda bai hada wadancan biyun ba ya zamo sarki, alhali lokacin rayuwa ce kwatankwacin ta dabbobi, mai qarfi shine a sama, sarauta da shugabanci ko wanne iri ne gida ko ace zuriya yake bi, wato idan akace wane shine shugaba kaza, tofa shekaru aru-aru masu zuwa zaka samu cewar zuriyarsa ce ke riqe wannan kambun.
Sibana dai kafin zamowarsa Sarki, ance masani ne amma fa matalauci naqin qarawa tun alokacin da sani bai wadata ba kuma arziki bai zamo ruwan dare ba, masanin dalasumai ne; wasu kalmomi da ake ta'allaqa su da wasu halittu wadanda ido baya iya gani, masanin hukunci ne, mai kamanta adalci ne, kuma gwanin tsara magana ne. Sannan kuma an haqqaqe cewar yana cikin sahun wasu mutane da akewa kallon gida-dawa a wancan lokacin, wadanda suke neman buqatunsu a wurin Allah. Idan zasuyi alqawari, bada shaida ko tawassali don samun wata buqata, sunayi ne da Allah wanda sukayi imanin al'arshinsa yana sama, duk da cewa a lokacin akwai qarancin ilimin wanene Allah.
Wata rana sibana yayi mafarki ana masa magana da wata sassanyar murya, ana cewa "ya kai wannan mutum, haqiqa Allah yayi maka baiwar ilimi da hikima, abinda tsiraru acikin bayinsa ne suke dashi. Allah ya fifita taka fiye da yawa-yawan mutanen wannan alqarya. Don haka lokaci ya gabato wanda Allah zai daukaka ka da ilimin ka, ba bisa ga abinda kayi gado ba, ba kuma bisa ga wata bajinta da kayiwa al'umma ba, sannan zai qasqantar da jahilai bisa ga abinda suka dade suna aikatawa na munanci ga Allah.
Ya kai wannan mutum, kayi shiga irin ta qasqantattun mutane kanufi Fada gobe, kasanar da sarki cewar zaka bashi amsar tambayar sa, zaka sanar dashi aikin da Allah yake aiwatarwa da hannunsa tare da qwararan hujjoji matsawar ya yarda da sharadin zai baka kayansa na sarauta, zai sanya naka, zaka hau kan karagarsa kuma dole kowa yayi maka biyayya sannan zaka fadi amsar.
Ya kai wannan mutum, kayi sani cewa daga nan mulki ya dawo gareka. Ka sanar da mutane hukuncin Allah da ikonsa wajen daukaka qasqantacce da qasqantar da daukakakke yafi ga haka, kayi mulki kuma da gaskiya da adalci. Haqiqa zaka dauwama acikib mulki, zaka samu duk cikar burikanka matsawar baka fara gaggawar yanke hukunci acikin lamurorin kaba, sannan matsawar fushi bai zamo yana tunkudaka aikata munanan aiyuka ba.." Yana zuwa nan ne ya farga afujajan.
Farkawar sa keda wuya ya samu kansa yana maimaita maganganun da aka sanar dashi. Babu abinda ya mance kai kace gar-da-gar aka sanar dashi wadannan zantuka. Tunani ya mamaye shi, ya rasa abinyi. Anan ne ma yake fahimtar ashe gari ya waye, rana ta take.
Yana cikin wannan hali ne kuma ya jiyo San kira yana shela a gari yana cewa "yaku mutanen wannan alqarya, Sarki Alkandaruz yana sanya muku albarka, yace asanar daku, bai daukewa kowa ba halartar taron daurin aurensa gobe a fada da gimbiya Sulbaniya ba, sannan yace asanar daku ya tanaji babban muqami da tarin dukiya ga duk wanda yazo masa da amsar da daddiyar tambayarsa gagara amso. Abinda kawai akeso shine, kafadi aikin da Allah yake aikatawa da hannunsa, ka kuma kawo hujjoji qwarara tare da inda ka same su."
Wannan abu ya qara dagawa sibana hankali, wato dai lamarin mafarkin sa akwai wani sirri acikinsa. Sai dai abin da ke bashi tsoro shine tayaya zai iya gaskata mafarkin? Idan dai sibana bai manta ba, a shekarar data gabata, sarki ya hallaka kimanin mutane talatin wadanda suka zo da zummar amsa wannan hatsabibiyar tambaya tashi. Daman shardin tambayar kenan, duk wanda baiciba, ajalinsa yazo kenan. Idan mutum yazo da amsa, sarki zai amsa, sai kuma yace kawo hujjoji da kuma inda kasamo wannan amsa. Tofa ana ake yinta. Saboda mafiyawan mutane shaci fadi kurum sukeyi, tunda alokacin kan mutane bai waye da ilimin saukakkun littattafai ba, Allah dinma da yawa wai-wai dinsa kurum akeji.
( #Sadiq Tukur Gwarzo)
A zahiri, Sibana baiyi niyyar tunkarar Sarki Andaruz da wannan kasada ba. Sarki Andaruz fa jarumin gaske ne, yana da girman jiki, da kwarjini, gashi da qarfin fada aji. Sarakuna ma shakkar sa yake ji, don haka duk abinda yake so ko basa so, ala tilas akeyi masa. Amma kasancewar tunanika da qunci sun yiwa Sibana yawa, sai ya tsinci kansa yana mai cire son rayuwar duniya a ransa, yayi niyyar magance quncin dake ransa ta hanyar kai kansa ga halaka, wataqila zai samu sukuni idan aka hallakashi. Mafitar daya daukarwa kansa itace, zaibi umarnin da aka bashi a mafarki, in yaso sarki ya kashe shi ya huta da zullumi gami da quncin rayuwar daya ke fama dashi.
Kamar yadda aka buqata kuwa, fadar Sarki Alkandaruz tayi cikar kwari. Daman qasaitacciyar fada ce mai cike da gine-gine dogaye. Sarki yana can saman wata husumiya akan karagarsa. A qasan sa kuma manyan waziransa ne da wasu sarakuna wadanda aka gayyato domin shaida daurin auren Sarki da Gimbiya. Kasancewar Sarki yana matuqar qaunar gimbiya sulbaniya yasanya shi cikin annushuwa a wannan rana da zai aureta. Dariya kawai yakeyi, kyauta yakeyiwa bayi sai kace ruwan sama, gashi can akaraga yasha fararen tufafi masu tsada masu dauke da ado na jan jauhari da lu'u-lu'u.
(#Sadiq Tukur Gwarzo)
Kamar yadda aka tsara, za'ayi shela ne har sau uku. Idan an samu wanda yazo ya baiwa sarki amsar tambayarsa, to sai a gabatar dashi a gaban sarki. Idan kuwa ba'a samu ba, shikenan sai a daura auren sarki da gimbiya daga nan kuma ashiga sahun shagulgulan biki. Don haka mai shela ya fara shela. Yayi kira da murya kakkarfa, yayi kirari ga sarki, ya yabi gimbiya, sannan ya nemi duk wanda yazo da amsar tambaya ya matso, yana mai koda kyaututtukan da sarki yayiwa duk wanda ya dace tanaji.. Sarki zai baka babban wazirinsa, zai baka damar tattara harajin duk masarautun dake qarqashin ikon sa, zai aura masa aure da mata dari, zai bashi katafaren gida.. Dadai sauransu.
Mai shela ya qara yin shela akaro na biyu, amma wurin nan tsit kakeji. Talakawa duk sun shiga taitayinsu, kunsan ance wargi wuri yaka samu. Qwaqqwaran motsi ma bakaji, kai kace cewa akayi duk wanda ya motsa abakacin rayuwarsa ne. A karo na uku ma mai shela ya qara yin shela wanda bai rufe baki ba sai ga Sibana kwaram-kwaram yana sanye da tufafi yagaggu, ga kayan hauka nan rakwacan sanye ajikin sa. Ya nufi husumiyar Sarki kai tsaye, kwachachaf-kwac
hachaf kawai kaceji kai kace shine maigirma Sarkin mahaukata na duk duniya.
Dakarun sarki sukayi kansa asukwane saboda ko ina sune dauke da takubba gayawa jini na wuce, wasu kuma riqe da kibau, harda masu majaujawa. Suka sha gabansa, babban su ya daka masa tsawa yace kai mahaukaci, a fadar Sarkin sarakuna kake ka natsu. Sibana ya daga kansa yana mai dubansa ba tare da tsoro a tare dashi ba yace "Ni ba mahaukaci bane, kuma amsa nazo nabaiwa sarki. Kayi sani cewa Karshen tababa da zubda jinin jahilai yazo, kuma lokacin da gaskiya zatayi halinta ya tabbata. Don haka ka sanar da Sarki cewa duk abinda yakeso ya sani lokacin sa yazo, zan bashi amsa ba kuma naneman abiya da da wata kyauta amma fa sai idan har zai iya cika sharuddai na guda uku dazan ambata".
Sarki ya qyaqyace da dariya, ya buga qafa qasa cikin annushuwa da qeta da yaji abinda wannan mahaukaci yazo dashi. Yace "ku matso dashi gabana, yazo ya fadi wadannan sharudda, mu kuma munyi alqawarin zamu cika su. Amma fa idan har ya kasa bada amsa, to da sannu zansa ayi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsa". Sibana ya tsaya a gaban Sarki bayan dakaru sun gabatar dashi, sannan ya fara magana da cewa "ya kai Maigirma sarki wanda sarautarsa ta fadada, ikonsa ya shiga duniya, kai ne sarki mafi qarfin iko a duniya. Kasani cewa bana neman wata kyauta abisa amsar tambayarka dazan bayar. Sharudda kurum nakeso kacika. Na farko, zamuyi musanyen kaya dani-dakai. Na biyu zaka dawo nan inda nake, nikuma zan zauna a inda kake. Na uku kuma dakarunka zasuyi biyayya agareni. Idan har ka amince, to ina maka albishir da samun cikakkiyar biyan buqatarka agareni"
(#Sadiq Tukur Gwarzo)
Ko kadan Sarki bai dauki wadannan sharudda abisa wasu abubuwa masu sharadi ba, don haka nan take ya amince. Abinda yake hangowa kawai shine zai taya bera bari ne, wato zai qure qaryar wannan mahaukaci inyaso sai ya gallaza maza da azaba mafi muni, tayadda al'ummarsa zata qara jin tsoronsa. Da yake kuma Sarki ne wanda yake sa gabansa aduk inda yakeso, sai ya kasance babu daga cikin wazirinsa wanda yace maza kanzil akan cika wadannan sharudda.
Sibana ya zauna akan karagar sarki. A halin yanzu shine Sarki, domin kuwa duk dakarun sarki umarninsa suke jira ba umarnin Sarki Ankaldaruz ba. Sibana ya dubi taron jama'a yace "yaku jama'ar Andaluz dame nayi kama yanzu??? Mutane suka dauka gaba daya da cewa "da sarkiiiii". Ya qara cewa "wannan fa damai yayi kama?" Yana mai nuni da sarki Alkandaruz? Mutane suka qara cewa "da mahaukaci". Sai ya kalli Sarki Alkandaruz yace " wannan shine aikin da Allah mai iko ya aiwatar da hannunsa yanzu-yanzu. Sarki ya zamo mahaukaci, mahaukaci ya zamo Sabon Sarki." (#Sadiq Tukur Gwarzo)
Sarki Alkandaruz yayi tsaki, ransa ya baci saboda abin kamar yazo masa da qasqanci. Sannan ya dubi Sibana yace "to yi sauri ka cire kayannan ka dawo nan, wadannan kayan sun. Isheni da tsami. Sannan kuma idan ka kasa bani hujjar maganar ka da inda ka samo amsar na rantse sai na lahira ya fika jin dadi". Da fadin haka sai yayi kan karagar da nufin ya hankade sibana da qarfin tsiya. Ai kuwa nan take sibana ya dakawa dakaru tsawa, yace ku kama shi kuyi maza ku kai mini shi kurkuku. Ai duk wanda yake son zurfafa bincike acikin lamarin Allah hauka da qasqanci ne makomar sa" Aikuwa ala dole, suka amshi umarnin sabon sarki, tsohon sarki tun yana ashariya, har ya dawo yana magiya, amma ina, bakin alqalami ya bushe. Anan take ya fara fahimtar kuskurensa. (#Sadiq Tukur Gwarzo)
Sabon Sarki yayi jawabi mai ratsa jiki ga al'umma, yayi musu nasiha da gaskiya, adalci gami da zama lafiya. Daga nan kuma aka dauka aurensu da gimbiya Sulbaniya..
Wannan shine matashiyar wannan labari..
Darussan dake shirin GASKIYA DACI GARETA na wannan lokaci sune;
*Ya kamata mutane mu qara jin tsoron Allah, haqiqa ikon da Allah yake dashi yafi gaban a misalta.
* Hakika Allah shine mai yadda yaso, kuma ina aywatar da ikon sa cikin hikima a kowanne lokaci.
* duk baiwar da Allah yayi maka, kada kayi izgila. Kada kabari karfin iko ya yaudare ka har ka shiga hurumin Allah Ta'ala, domin haqiqa Allah bazai kyale ba.
* Duk kuncin da kake ciki, ka miqa lamuranka ga Allah Ta'ala. Idan lokacin da hukuncinsa yayi, babu makawa sai ya auku.
* ya 'yanuwa, haqiqa muna zaluntar kawunanmu a wannan zamani ya yadda muke qasqanta darajar ilimi da ma'abota ilimi, muke kuma ganin dukiya da muqami sune qololuwa a rayuwa. To dai dayake ance Gaskiya daci gareta, ya kamata mu sanar da kanmu cewa wannan tunani na halaka ne. Ya kamata mu sanar da kawunan mu gaskiya tun kafin wani ya sanart mana.. Shi Ilimi ai yafi dukiya, Manyan malamai duk sun sanar da haka, don haka shi yafi buqatuwa mu nema sama da duk wata daukaka ko matsayi.
Ku tuna dai, wani masani yana cewa a waqe "Duk daukakar da ba'a sameta ta hanyar ilimi ba, qarshenta qasqanci ne. Idan shugaba ya zamo mai ilimi, ilimin na zamar masa riga qasaitatta da kuma fitila mai jagoranci."
Zamuci gaba da yardar Allah.
SHIRIN GASKIYA DACI GARETA na biyu
LABARIN SARKI SIBANA DA GIMBIYARSA SULBANIYA
Tare da Sadiq Tukur Gwarzo
Da yake Allah shine mai yadda yaso a lokacin da yaso, a dare daya Sibana ya zamo sarki mai cikakken iko kuma qasaitacce. Shikuma azzalumin sarki ya zamo mazaunin gidan Jarun. Abinka da mai Ilimi, sarautar Sarki Sibana sai ta sauya. Ya kawo tsare-tsare masu kyau na adalci, ya haramta cin hanci da almundahna, ya kuma yi umarni da rage dumbin harajin da talakawa ke biya don sauqaqewa gare su. Wannan yasa nan da nan ya samu farin jini. Lungu da saqo sai waqoqi ake raira masa na yabo, gami da zambo ga tsohon sarki.
A daren farko da Sarki sibana ya shiga dakin amarya gimbiya subaniya, sai yake ganin abubuwan kamar a mafarki. Shi kansa yana mamakin wannan juyi da Allah yayi masa. Dakin nata an qawata shi da ado na alatu, ga fitilu masu kyawun gaske reras. Kamshi kuwa sai tashi yake yi, ga sautin wasu yammata kuyangi masu rera waqoqi yana tashi kadan-kadan, yabonsa kurum sukeyi tare da amaryasa, nan fa wani farin ciki ya qara cika masa zuciya, tuni ya fara mancewa da wahalar duniya, domin a yanzu jinsa yakeyi kamar tunda aka halicce shi shine Sarkin duniya.
Duk inda yasanya kafarsa, laushi yakeji kamar zai nutse. Ya hangota zaune bisa wata darduma, tana sanye da jajayen kaya masu ado da zinare, walwali da sheqi kawai takeyi.
Gimbiya Sulbaniya ta yaye mayafin daya rufe mata fuska, gami da dago kanta sama kadan. Ta dubi Sarki sibana, shima ya kalle ta, sannan ta duqar da kanta qasa tana mai cewa " Marhaban dakai Sarki daya tamkar da dubu,
sarkin da adalcinsa zai game duniya, sunan sa zai ratsa samaniya,
izzar sa zata wanzu har qarshen duniya,
An halicce ni don zamowa baiwa a gareka.
Maraba dakai haske maganin duhu.
Ina da buqata a gurin ka ya kai jarumin maza.."
( #SadiqTukurGwarzo )
Sarki sibana ya zura mata ido. Ganinta yake kamar aljana. Kyawun ta ya wuce a misalta, kallon kwayar idanunta kadai ya isa ya mantar da mutum wahalhalun duniya. Haka ma kallon daukacin fuskar tata . Kalmominta sun dauke shi daga wannan duniyar. A halin yanzu jinsa yake kamar anyi masa hisabi yana cikin aljanna. Sarki sibana ya nisa daga yanayin da yake ciki, dakyar ya samu kansa. Sannan yace "nayi miki alqari kome kike nema agurina zan miki matuqar ina iyawa"
Daga nan gimbiya sulbaniya ta fara bashi labarin ta kamar haka. "Ya kai wannan sarki mafi karimci daga sarakunan duniya, kayi sani cewa Sunana sulbaniya, mahaifina sarki Rama shike sarautar masarautar Ramayana dake kasar hindu. Ya kasance yana da fada aji, da karfin mulki. A yanzu haka ma, mutanen kasarmu na ganinsa kamar wani mahalicci, tunda har bauta masa akeyi. A lokacin da mahaifiyata ta dauki cikina, sai aka nemeta aka rasa. Nan fa hankalin mahaifina ya tashi. Da yake shima masanin tsafi ne, sai ya dugunzuma a cikin tsatuben sa, har saida ya gano inda take.
Ashe wani hatsabibin boka ne mai suna sundusur ya dauketa izuwa wani tsibiri mai suna Laaka, waje ne da ake kallo a matsayin mafi hatsari a duniya. Dalilinsa nayin hakan kuwa shine, yayi bincike a fagen tsafinsa sai yaga cewa za'a haifeni, zan kuma zamo mace kyakkyawa mai annuri, sannan kuma wani sirri zai kasance dani cewa dukkakan wanda ya aure ni, matuqar yana faranta min rai, babu wani abu dazai tunkara ba tare da yayi galaba akansa ba. Ya fahimci tauraruwa ta kakkarfa ce, hadimai na kuma suna da matuqar tasiri anan duniya.
Wannan lamari ya tayar da hankalin mahaifina matuqa gaya. Har ya rasa sukuni. Duniya tayi masa kunchi. Ya rasa menene mafita. Ana haka sai ya tara hakimansa da sarakunan yaqinsa, ya nemi shawararsu abisa zuwa tsibirin laakha domin dauko matarsa. A haqiqa, kasancewar kowannen su yasan hatsarin dake kunshe cikin wannan tafiya, babu wanda ya goyi bayan sa. Har mutane na ganin bai kamata ace akan rai guda daya tilo ba ayi asarar rayuka marasa adadi.
Daga nanfa kunchi ya qara tasarwa mahaifina. Kullum cikin hawaye yake da bege, kawai sai wata basira ta fado masa. Yace aransa, tunda ina da karfi a tasirin tsafi, kuma ta hanyar tsafi aka sace matata, to kuwa tilas nabi ta hanyar siddabaru na kwato ta, koda kuwa hakan zaisa nayi asarar rayuwa tane ma baki daya. Daga nan ya kira wazirinsa ya mallaka masa jiran gari, sannan ya nufi daji abinsa.
(#SadiqTukurGwa
rzo)
Koda isar sa kungurmin daji, sai ya sami kan wani dutse ya hau, ya zauna yana mai harde kafafuwansa, ya janyo wani kuben tsafi qarami irin na yaqi, ya fara busawa. Ai kuwa nan take dabbobin daji suka fara amsa kira. A wannan lokaci, namun daji kala-kala sun samu halarta, birai da karnukan dawa sune manya 'yan gaba dai-gaba dai. Bayan runduna ta hadu, kawai sai ya nausa cikin daji yayin da sukuma dabbobi suke biye dashi. Duk inda suka ratsa sai dai kaga bishiyoyi na zubewa aqas, qura na turnuqewa sama, iska kuma qaqqarfa na kadawa. A haka har suka isa wawakeken ramin da za'a tsallake a isa tsibirin Laakha.
Shi daman wannan tsibiri, ana kallon cewa babu mutum ko dabba dake rayuwa acikin sa, sai dai gagarumai kuma hatsabiban maridan aljannu. Don haka ne Boka sundusur ya zabi ya gina gidansa anan, saboda yasan babu mai iya kai masa chaffa. Dadin dadawa, tsibirin yana kewaye ne da wani wawakeken rami, babu wanda yasan zurfin sa, kuma wuta ce ke fitowa daga qasan sa izuwa sama. Saboda haka ya zamo cewar koda tsuntsaye basa kai kawo a saman ramin, domin babu zato wutar ke fitowa, duk kuwa abinda ta samu ko ta shafa, take zaka ganshi yayi qurmus.
Mahaifina ya zurawa wannan rami ido yana nazari akan hanyar qetare shi. Daga bisani dai sai yayi shawarar cewa gada zai hada ta tsafi wadda zata rinqa tafiya a saman ramin har taje daya gavar, kuma zata rinqa gociya da zamiya ga wannan wuta. Wannan shine kadai mafita. Nan take ya umarci dabbobi dasu karyo itatuwa.
Haka kuwa akayi, yasa aka daddatsa wasu, aka nemo ganyayen da ake igiyoyi dasu, dashi da birrai suka shiga aikin gada. Sai da suka gama tsaf, sannan suka hau kanta suna mai fuskan tar ramin. Gada ta tashi sama, ta fara tafiya sannu a hankali akan wannan rami.
Basu jima da fara tafiya ba sai ga wani katafaren tsuntsu, ashe shima aman wutar yake yi, nan take suka fara gumurzu. Tsuntsu na kwararo wuta daga sama, rami na watso tashi daga qasa, ita kuma gadar tsafi nata faman zuzzullewa. Idan ta zulle, shashin wuta ya shafi wasu daga dabbobin nan sai dai kawai aga sun kama ci da wuta, kafin a jima sun zama toka. Wannan abu yayi matuqar dagawa magaifina rai. Har saida yayi nadamar fitowar sa, sai ma da ya gamsu cewa tilas rayuwar sa zata salwanta a saman ramin nan, sannan akayi sa'a wuta ta fito ta qasa, shikuma tsuntsun nan na sama yayo qasa-qasa gami da saito gadar da nufin qone gadar baki daya qurmus, kawai sai gadar da waske, ai kuwa nan take wutar ta chafki tsuntsun. Yayi wata qara gagaruma, kafin ajima ya qone qurmus.
(#SadiqTukurGwarzo)
Wannan yasa suka sami raguwar bala'in da suke ciki. Amma kuma saukar su kan tsibirin keda wuya wani sabon bala'in ya dawo. Domin irin wadannan tsuntsayen n sunfi dubu ke dakon su. Da hango saukar su kuwa sai suka tashi sama, suka shiga aman wuta babu qaqqautawa. Nan fa rundunar mahaifina ta tarwatse, gashi basu da wasu makamai na mayar da martani, dole dabbobi suka shiga gudun neman mafaka, wasu suka nufi qarqashin duwatsu, wasu kuma suka koma da baya kan gada.
Da dai mahaifina ya rasa abinyi, sai shima ya quduri niyyar jarraba irin nashi tsafin, amma ga mamakinsa, duk abinda ya qudurci yi sai yaqi yiwuwa, sai da dabarunsa suka qare qar-qaf, yayi gudu kamar zai halaka wajen tsira daga sharrin tsuntsayen nan, wasu dabbobin kuwa duk sun qone, sai da suka dawo 'yan qalilan. Kwatsam sai mahaifina yayi wata shawara. Yaga cewa tunda tsuntsayen nan wuta suke fesowa, to bari shima ya koma wutar, wataqila zai kubuta daga sharrin su. Ai kuwa sai kawai ya rikide izuwa curin wuta, sannan ya nufi kofar shiga fadar da gudu.
Nan fa tsuntsayen nan suka ce dawa aka gama mu ba da kai ba? Suka tashi haiqan akansa, wuta kurum suke fesowa, shi dai bai canza siffa ba a haka har ya shiga fadar boka sundusur, duk inda ya wuce sai dai kaga wuta naci ganga-ganga a fadar, suma kuma tsuntsayen suka himmatu a mayar da wuta, kafin jimawa sai ga sassan fadar yana ci da wuta.
***
Darussan mu na wannan lokaci sune:
1. Kayi imani da Allah a kowanne lokaci, kada kuma duniya ta rudeka. Allah na iya canza duniyar ka akoda yaushe.
2. Shugabanci yana da wuya. Dole sai ka rinqa bin maslahar al'umma. Kada don kana shugaba ka dora buqatar ka fiye data mabiyanka.
3. A kowanne lokaci ka fadawa kanka gaskiya. Duk lamarin da zaka shiga, ka lura da wahalhalunsa, kada ka bari dadi ko bakin ciki ya rudeka kayi abin ba tare da kasan rikicin da zai iya aukuwa ba.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo

ARKIN BIRNIN HUNAN DA ALJANNU

HIKAYAR SARKIN BIRNIN HUNAN DA ALJANNU
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Daga cikin tsoffin hikayoyin da suka shahara a birnin Sin daruruwan shekaru da suka gabata, wannan hikaya na sahun gaba.
Akace a wani zamani daya shude anyi wani babban birni mai suna Hunan. A wani lokaci kuma, sai ya kasance anyi wani attajirin sarki a garin wanda ya tara mamakon dukiya a baitul malinsa. Har ya kasance ya taskance sunduk'ai na zinariya kimanin dubu d'ari shidda acikin wannan taska. Wannan ne yasa yaga buk'atuwar samo mutum mai amana don dank'a masa gadin wannan taska.
Akan haka, sai ya baiwa wani amintaccen Bafadensa mukullin taskar. Ya shaida masa cewa ya dank'a tsaron dukiyar duk dake ciki a hannunsa. Baya son ko allura ta b'ata.
A kullum, wannan ma'aji yana baro gida da dare, yazo ya kwana da safe ya koma gida. Kullum haka kullum haka. Rannaan ya baro gida kenan sai hadari ya hadu a gari, kafin kace haka ruwa ya kece mai mamakon yawa. Tilas ma'ajin taskar sarki ya nemi mafaka a wata rumfa tsohuwa, da niyyar da zarar ruwa ya d'auke sai ya k'arasa wajen aikinsa.
Abu dai kamar wasa, a wannan dare sai da aka kwana ana ruwa. Hakan na nufin ma'aji a rumfar daya fake ya kwana sab'anin a taskar sarki. Aikuwa bayan d'aukewar ruwa ya runtuma izuwa taska. Sai dai ga mamakinsa, yana zuwa sai ya tarar da ita a washe. Babu ko allura.
Wannan abu yayi matuk'ar sanya shi jimami. Ya rasa inda zaiyi da kansa. Yayi dube-duben duk da zaiyi tare da tambayar makwabta, amma sam bai samu wani abu mai dadi ba. A k'arshe dai ya yanke shawarar tafiya don sanar da sarki wannan mummunan labari.
Da zuwan sa fada, ya fadi gaban sarki yayi gaisuwa. Sannan ya kwashe labari ya fad'awa sarki. Sarki yace sam bai gamsu ba, k'arewa ma sai yasa fadawa su tuhume shi, yace awurin sa wannan ai barkwanci ne. Abu dai kamar wasa, fadawa suka rink'a nakad'awa ma'aji azaba, amma bai canza maganar saba. Sarki yasa aka je taska aka gano yadda ma'aji ya fada hakanan take.
Da sarki yaga ana neman hallaka ma'aji ba tare da samun wata magana mai k'wari ba, sai yace a dakata. Yacewa ma'aji ya bashi lokaci, da zimmar yaje duk inda wannan dukiya take ya maido da ita, ko kuma a maimakon ransa.
Ma'aji ya taso daga wurin sarki a gajiye, tinkis-tinkis. Yana tafiya kamar wani mashayi sabida azabar da aka gana masa. Azuciyarsa kuwa yana ta sak'a yadda zaiyi da rayuwarsa. Kwatsam sai ga wani makoho ya bangaje shi. Ma'aji cikin fushi ya dubi makaho zai daka masa tsawa saboda bangajin da yayi masa, amma dubawar dazaiyi sai ya fahimci ai makaho ne, don haka baice uffan ba, ya cije baki kurum yayi gaba.
Makaho ya juyo yana doddogarawa da sandarsa, yana kai hannu dazimmar kamo tufafin wanda ya bangaza, yana cewa yi hakuri mallam, kune ke ganin mu ba mune ke ganin kuba.
Ma'aji yace to babu laifi, amma dai zaifi kyau ka rink'a yawo da d'an jagora, kasan halin mutanen yau da zafin zuciya, idan wani ka bangaza haka yana iya kwabd'eka da mari.
Makaho yace kwarrai kam. Mutanen yau sai hakuri. Sai dai na karanci wani abu a tattare dakai, don haka idan kanaso matso kusa na taimakeka.
Ma'aji yace me ka karanta? Kuma wanne irin taimako zakayi mini? Yana mai matsawa kusa da makaho.
Makaho ya dafa kafad'ar ma'aji a dai-dai sa'ar dayazo daf dashi sannan yace "ni daka ganni nan, makaho ne mai karantar abinda ke zukatan mutane. Kuma a yanzu na fahimci cewa matsalar kud'i ce ta dugunzuma ka.."
Ma'aji yace tabbas haka nan ne. Daga nan ya zayyana masa labarin sa duka.
Makaho yace to biyo ni idan kana Iyawa, da sannu zaka gani da idonka.
Daganan suka fara tafiya. Ma'aji na gaba makaho na biye, amma makaho ke fadin inda za'abi. Shine ke cewa ayi gabas, yamma, kudu ko arewa. A haka har suka bar gari, suka shiga kungurmin daji cikin manya-manyan duwatsu. Suka hau kan wata hanya da take a tsakankanin duwarwatsu, basu jima ba sai ga wani katafaren birni a gabansu.
Nan ma dai suka shiga cikin garin, ga mutane nata harkokinsu babu mai tankawa wani, gidajen garin kuwa na alfarma ne dogaye gwanin ban sha'awa.
Suna cikin tafiya, sai makaho yace wa ma'aji ya tsaya. Sannan makaho yayi nuni da sandarsa izuwa kofar wani babban gida na alfarma, yace "ka kwankwasa wannan kofa, ka nemi taimakon mutanen gidan akan matsalar ka, da yardar Mai sama zaka dace da buk'atar ka." Daga nan bai k'ara cewa uffan ga ma'aji ba, ya wuce gaba yabar shi anan.
Ba tare da bata lokaci ba, ma'aji ya matsa kusa da kofar gidan ya fara kwankwasa ta sannu a hankali. Ba'ajima ba kuwa sai yaji ana kici-kicin bude kofa.
Wani mutumi fari dogo ne yafito daga gidan, yana sanye da tufafi kalar tufafin da fadawan sarkin Hunan ke Sanyawa. Ma'aji ya kwashe duk abinda ke tafe dashi ya fadawa wannan mutumi. Mutumi kuwa yace kwarrai kazo inda za'a taimakeka, amma sai idan zaka iya jira na wasu yan kwanaki a cikin wannan gida.
Ma'aji yace to babu matsala. Shikenan kuwa sai suka dunguma izuwa cikin gidan....
Zamu cigaba gobe insha Allahu

HINDU

HIKAYAR WASU SARAKUNAN HINDU
Tare da Sadiq Tukur Gwarzo
A wani zamani mai tsawo daya shude, lokacin da ake cewa mutane na magana da dabbobi, anyi wasu sarakuna biyu manya a kasar hindu, kowannen su na mulkin garin sa daban da dayan, sannan dukkansu sun kasance masu yawan kyauta, amma dayan su yafi daya kyauta.
Sarki na farko sunan sa Karna. A kullum yana rabon dinare dari ga mabukata. Har ma yasha alwashin cewa bazai taba cin abincin safe ba a kowacce safiya har sai ya kammala rabon dinare darin daya saba. Sai dai inda yake samun wadannan dinarai ya zamo abin tambaya da mamaki a wurin jama'a.
Na biyun su shine Vikram. Wannan sarki shahararre ne a wurin kyauta. Domin yana bada kyautar duk abin da aka tambayeshi tun daga kan gwala-gwalai, azurfa, gidaje, kuyangi da sauran su. Ance babu abinda ake tambayar sa ba tare da an samu ba, kuma wai har dabbobi na rokon sa abu.
Wata rana Sarki Vikram na shakatawa a lambunsa, sai ga wasu tsuntsaye mace da namiji sun dira a gabansa.
Namijin yace "Ya sarki mai kyauta, ka ceci rayuwar mu, yunwa zata kashemu".
Sarki yace "Abinci kuka rasa ko yaya? Idan kunaso zan rinka aiko muku da tsabar abinci a kullum".
Ta macen tsuntsun sai tace "Ay bazamu iya cin tsaba ba. Muna rayuwa ne can saman wani tsibiri, kuma 'ya'yan itatuwa ne wadanda ba'ai wa tabo ba kadai abinda muke iya ci"
Sarki yace " To babu matsala". Nan take yasa aka kawo musu zababbun 'ya'yan itatuwa masu kyau aka basu. Sannan aka ce kullum safiya suzo su amshi irin wadannan 'ya'yan itace masu kyau suci.
Hakan ne yayi ta faruwa. Kullum da safe tsuntsayen na samun abinda suke so kamar yadda aka alkawarta musu. Sai dai wata rana, ta-macen tsuntsuwar nan ta lura da cewa an kawo musu 'ya'yan itatuwa wadanda aka gatsa. Sai tace da namijin "kalli da kyau kagani.. Anyiwa wadannan 'ya'yan itatuwa tabo. Don haka sarki bazai iya ciyar damu ba, zaifi kyau mu tashi mu tafi wani wurin daban".
Da fadin haka sai gano su akayi sun shilla sama suna karkada fuka-fukin su tare da fadin "mungode maka Sarki Vikram, kaine mafi kyauta a sarakunan duniya".
Tsuntsayen basu gushe ba suna wannan yabo ga Sarki Vikram har sai da suka yi nesa sosai da garin izuwa wani babban tsibiri. Ashe a hanyar su ta wucewa sun gushe ta saman fadar Sarki Karna har kuma yaji abinda suke cewa, abinda ya sashi kishi, yake tambayar kansa tayaya za'ace akwai wani sarki da ya d'ara shi kyautayi a duniya?
Ai kuwa sai ya umarci wasu sadaukan sa da subi bayan wadannan tsuntsaye kuma su tabbata sun kawo masa su.
Kafin wani lokaci kuwa sai ga dakaru sun zo da tsuntsaye cikin keji ga Sarki Karna.
Sarki ya dube su cikin annushuwa yace " Naji kuna kiran wani sarki a matsayin wanda yafi kowanne kyauta, shin meye dalilin ku na fadar haka?"
Namijin Tsuntsu yace" Sarki Vikram ya kasance yana ciyar damu 'ya'yan itatuwa zababbu kullum da safe kuma baya daure wadanda basuyi laifi ba acikin keji".
sarki karna yace "Na kasance kullum da safe ina rabon dinare dari ga mabukata. Ashe ban fishi ba?" Sannan ya dubi dakarun sa yace "Ku kawo kwandon zababbun 'ya'yan itatuwa zan ciyar dasu yanzu".
Da aka kawo sai ya kalle su yace "Yanzu zan sa a ciyar daku da zababbun yayan itace, shin ban fishi kyauta ba?"
Sai ta macen tsuntsuwar tace "Ai shi sarki vikram da hannun sa yake ciyar damu".
Hakan yasa shima Sarki Karna yayi yinkurin ciyar dasu da hannun nasa, ya bude kejin zai mika musu tuffa. Sai dai kuma cikin hanzari ta macen tsuntsuwar tayi wuf ta fito daga kejin, sannan ta tashi sama. Bata zame ko ina ba sai gaban Sarki Vikram.
Da zuwanta ta fadi gaban sa tana afi, tayi masa bayanin abinda ya faru tare da rokon sa ya 'yanto mata mijin ta.
"Zan 'yan to miki mijin ki". Abinda sarki Vikram kurum ya fada mata kenan.
Kashe gari yayi shigar tsummokara, ya nufi birnin da Sarki karna ke mulki. Da zuwan sa ya wuce fada gaban sarki.
Ya fadi yayi gaisuwa, sannan yace " ya wannan sarki mafi kyauta a duniya, naji labarin karimcin ka da kyautatawar ka, don haka ina neman izinin ka don na zamo maka bara mai maka hidima."
Jin haka sai yasa sarki Karna yaji dadi a zuciyar sa. Sannan yace masa babu komai, " Duk abinda kaji a bakin mutane game dani gaskiya ne, kuma zaka shiga cikin masu dauko mini dinaran da nake rarrabawa kullum da safe".
Da gari ya waye kuwa Vikram da wasu bayin sarki suka kamo mazubin dinarai niki-niki. A kan idon sa Sarki karna ya raba guda dari ga mabukata.Shi da kansa vikram sai daya raya a ransa cewa Sarki karna ya fishi kyauta. Amma kumà sai yasha alwashin sanin inda Sarkin ke samo wadannan dinarai.
Tun daga nan Sai vikram ya ke ta leken asirin aiyukan Sarki Karna. Watarana da dare yayi, vikram ya wanzu leka kofar dakin sarki karna don yaga ko zai ga fitowar sa. Ai kuwa da gari ya dauko wayewa sai Vikram ya hango Sarki Karna ya fito daga dakin sa, yana waige-waigen kada wani ya gansa, sannan yabi wata hanya wadda zata fitar dashi daga cikin gidansa.
A hankali vikram ya rinka bin bayan sa yana labewa don kada ya juyo ya ganshi. Sai da suka fita daga gidan izuwa bayan gari, sannan Vikram ya hango Sarki karna ya nufi wata Bukka, kafin isar sa kuma sai ga wani tsoho irin masu kawwame kawunan su a wajen gari don bauta, ya nufo sarkin. Da haduwar su sai tsohon ya dukursa ya gaishe da sarki karna.
Sarki Karna ya tube kayansa daga shi sai gajeran wando, sannan ya dauki wata sanda ya nufi karkashin wata bishiya dake wurin. Ya rera wasu baitoci kamar haka:-
Ka_s_u_s_u_w_a_ d_a_ d_a_d_i_, a_m_m_a_ b_a_ k_a_m_a_r_ n_a_m_a_ b_a_.
Ka_b_a_ s_h_i_ r_a_y_u_w_a_, n_i_k_u_m_a_ z_a_n_y_i_ a_g_a_j_i_.
Da gamawar sa sai ya zunguro wata shigifa dake saman bishiyar. Nan take sai ga dinarai nata zubowa. Sanna ya karbo mazubi daga wurin tsoho ya zuba, yayi sallama da tsohon nan ya juyo izuwa gida yana dauke da tulin dinarai akansa. Anyi wannan duk akan idon Vikram. Da ganin haka, sai yace "yawwa, yanzu na gano yadda zan ceci Tsuntsu."
Kashe gari da sassafe vikram yayi sammako ya riga Sarki karna fitowa. Yazo wurin dattijo tare dayin duk abinda yaga sarki karna yayi. Tsoho bai iya gane shiba, abinda kurum ya iya tambaya shine sammakon da yayi, tunda yazo ba a lokacin daya saba zuwa ba. Vikram ya make murya ya ce masa uzuri ne ya fito dashi. Da Vikram ya gama yin duk abinda yaga sarki karna yayi, sai yace yau yana son tafiya da wannan shigifar gida, saboda kwana biyu wani uzuri zai hana shi zuwa wannan wuri. Tsoho yace to ba matsala. Sai kuwa vikram ya hau sama ya ciro shigifa yayi gaba da ita.
Anyi haka ba jimawa sai ga Sarki karna ya iso. Tsoho ya kamu da mamaki, ya kuma kwashe labarin abinda ya faru ya shaida masa. Nan take sai sarki karna ya cika da matsanancin bacin rai, lallai yasan cewa wanine yayi shigar sa ya tafi da wannan shigifa ta siddabaru.
Ya gama fadace-fadacen sa ga tsoho akan don me zai bari a tafi da shigifa, sannan ya koma gida. Kwana biyu sarki baya kyauta, kullum cikin bacin rai yake, har abinci ma baya iyaci.
Rannan kwatsam sai Vikram ya faki idon mutane ya shiga dakin Sarki karna. Yace masa "abokina, ka kwantar da hankalinka, shigifar ka na wuri na. Kuma zan dawo maka da ita matsawar zaka saki wannan tsuntsun da kake tsare dashi."
Sarki karna yayi tsallen murna, sannan yace ai a shirye nake na baka duk abinda kake so akan wannan shigifa. Amma yace yana rokon ya sanar masa da labarin sa.
Vikram ya labartawa karna ko shi waye da kuma labarin sa. Wannan abu yayi matukar kayatar da sarki karna. Shine ma har yace hakika tsuntsaye sunyi gaskiya. Ni ina iya yiwa talakawa kyauta don fidda su daga talauci, amma kai ka fini kyautatawa tunda kana iya sadaukar da kanka don 'yantar da tsuntsu."
Ai kuwa sai suka dunguma izuwa kejin da tsuntsu yake a tsare. Sarki karna ya bude kejin, tsuntsu yayi fir ya tashi sama inda ya hadu da matar sa wadda a kullum take rayuwa a boye a saman wata bishiya cikin bakin cikin rashin sa, tana mai fatan ganin ran da zai samu 'yanci.
Tsuntsayen suka wanzu cikin farin ciki suna waka ga sarki vikram, suna cewa " mungode, mungode, mungode wa Sarki vikram, wanda yafi dukkan sarakunan duniya kyautatawa"
Daga nan sai raha ta barke a tsakanin sarki Karna da sarki Vikram. Sarki karna ya tashi runduna don tayiwa sarki vikram rakiya izuwa birnin sa, sannan yasha alwashin shima idan ya samu lokaci zai kawowa Sarki vikram ziyara a birnin sa, zai kuma labarta masa labarin wannan shigifa mai ban mamaki wadda take aman dinare.

TARIHIN KASUWANCI A KANO

TARIHIN KASUWANCI A KANO
Tsakure daga littafin 'Kano cibiyar Kasuwanci ta Africa' wanda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo (Allah yajiqansa da Rahama ya wallafa).
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Maigirma Farfesa Sani Muhammad zaharaddin, babban limamin Kano ya faɗa a ta'alikin littafin cewar:-
Ana yiwa Kano kirari da "ka misulu alfin, Jalla Babbar hausa, Gari ba kano ba Dajin Allah! Yaro ko dame kazo an fika."
Haka kuma marigayi ɗan kishin kasa Sa'adu Zungur yana cewa a wakarsa Arewa Mulukiyya ko Jamhuriyya:
Ya! Sarki Alhaji Bayero,
Ga 'yan birni da kanawiyya
Tun Bagauda na Saran kano,
Suka fara fataucin dukiya.
TARIHIN ZUWAN LARABAWA KANO
A shekara ta 1453 miladiyya, a zamanin sarkin kano Yakubu ɗan Abɗullahi Barja, sarkin kano na goma sha shidda a mulkin kanawa, waɗansu larabawa mutanen kasar Gadamus masu fatauci suka zo daga Tarabulus (Libya), suka sauka a kano. Sune larabawan farko da suka fara zuwa kano.
Da saukar waɗannan fatake, sai sukaje wurin sarkin kano Mallam yakubu, a jujin 'yan Labu, a lokacin ba'a gina gidan sarautar kano na yanzu ba, suka ce da sarki a cikin harshen larabci su fatake ne, suna so su zauna a kano domin suyi ciniki.
A wannan lokaci kuwa, limamin kano Mallam Muhammadu Hashimu ne yake fassarawa sarkin kano abinda waɗannan fataken larabawa ke faɗa a matsayin tafinta. Daga nan sai sarikin kano yakubu yayi farin ciki kwarrai da gaske, sannan yace da shamakin kano ya kaisu sararin nan dake yamma da unguwar Garke watau Dandali, suyi gidaje su zauna acan.
Sabili da waɗannan mutane suna da jar fata, sai mutanen kano suka sa musu suna Turawa. Don haka koda larabawan suka zauna a wannan wuri, sai mutane suka sanyawa wurin Dandalin Turawa. Dalilin sunan dandalin turawa kenan yau kusan shekaru 553 kenan.
Tun daga wancan lokaci ne larabawa suka cigaba da zuwa kano fatauci. Kamar misali akwai Yamalawa mutanen Yamen, da larabawan Tunis duk sun riski kano, amma kowaɗanne akwai nau'in kasuwancinsu.
Su larabawan Libya mafi yawan abinda suke siyarwa kayan alatu ne irin na sarakai da kayan kamshi da kayan zaki.
Sai dai ya kamata a sani, da wahala ace ga lokacin da aka soma samar da kasuwanci a kano. A zamanin da, mutanen kano sunfi riko da noma fiye da wata harkar kasuwa, amma ana aiwatar da sana'o'i na gargajiya misalin rini, jima, kira da sak'a. Waɗannan su suka haifar da ainihin kasuwanci, domin mutum zaiyi abu ya siyar ga jama'a.
Koda yake, a wancan lokacin, ba'a fara amfani da kuɗi ba a kano, ana yin cinikin furfure ne, watu ban gishiri in baka manda.
Daga baya ne lokacin da fatake ƙlarabawa ko Asbinawa da Agalawa suka zo kano, kasuwanci ya fara kankama a kano.
Haka ma, sauyawar akalar kasuwancin kasar hausa daga izuwa kano kamar yadda littafin 'Kano civil war and the British Over Rule 1882-1940' na Muhammad F.A ya ruwaito ya taimakawa kano matuka gaya, domin an samu cewar fatake sun yiwa katsina tawaye ne, suka koma kano ɗungurungum da kasuwancinsu.
Zuwan turawa kano kuwa, da kuma yadda suka samar da farin kuɗi a shekara ta 1930 don yin musanje ya haɓaka kasuwanci sosai a kano. Domin a zamanin ne kanawa suka samu buɗewar ido ainun a harkar, har ya zamana suna yiwa kansu jagoranci, abinda ya sanya kano ta k'ara bunksa kuma kenan har ake mata kirari da Tumbin giwa ko dame kazo an fika.
Kai bama nan ba, har daga kasashen Kasabalanka ta Morocco da Yunana ta Girka fararen fata sunzo fatauci kano, bari kuma kuji yadda suka zo...
A karni na goma sha biyar, zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammdu Rumfa, wasu turawa fatake sunzo kano daga girka. Kasarsu acan kusa da Istanbul take, ana kiranta Yunana, a yankin kasashen Turawa.
Su waɗannan turawa sunzo kano ne domin fatauci, sun kai kimanin arbain, da rakuma kusan talatin da biyar, masu ɗauke da kayayyakin dukiyoyi masu yawa kamarsu alkyabbu, jabbobi, falmarori, kuftoci, jauhohi, hulunan dara, takalma, kilisai, takardu da kuma takubba.
Sai waɗannan fatake suka iso kofar fadar sarki, suka nemi iso sannan sukayi gaisuwa gareshi da larabci.
A cikin malamn da suke zaune, sai wani Malami mai suna Abdurrahman ya rinka fassara maganarsu da hausa.
Daga nan sai waɗannan fataken suka gayawa sarki Muhammadu Rumfa cewa su ba larabawa bane, Turawa ne mutanen Giris. Sun iya larabci ne kurum kuma fatauci ne ya kawosu kano. Nan take sai suka fito da kayayyakin da suke siyarwa.
Da yake a wannan zamanin, ba'a soma ciniki da kuɗi ba, sai sarkin na kano ya tambayesu cewa ku kuma me kuke da bukatar saye a wurinmu? Sai sukace muna bukatar bayi, fatu, kiraga, albasa da tafarnuwa. Daga nan sai sarki yace yana bukatar dukkanin kayayyakin nasu, sannan yasa a shirya musu kayayyakin da suke da bukata.
Ance an basu masauki a inda asbitin unguwar Marmara yake a yanzu, akayi musu ɗakuna dogaye da tsangayu masu faɗi da tsawo, aka yi musu hayin shirayi, sannan kowanensu aka bashi gado da tabarma.
Sarki ya tura musu bayi domin suyi musu hidima. A lokacin saida bayin suka haka musu tijiya domin samar musu da ruwa saboda rashinsa, shine har akace idan turawan suna bukatar ruwa sai suce Akwa, wai sunan ruwa kenan da yarensu, daga bisani sai aka sanyawa rijiyar suna 'Yar Akwa.
Waɗannan turawa da suka zo a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, sune suka fara kawo takardu da takobi. Suna kiran takardu "Yarta krata", takobi kuma "Takopis". Watakila daga nan sunayen suka samo asali domin da harshen hausa kansakali ake kiran takobi.
Da lokacin tashin fataken yayi, sai suka haɗa gagarumar kyauta suka baiwa sarki, sarki ya ɗauki nasa ya kuma rarrabawa hakimansa, sannan yasa aka basu bayi hamsin mata da maza, da dawaki masu yawa, gami da sauran kayayyakin da suka bukata tunda fari, sannan aka haɗa tawaga domin tayi musu rakiya.
Suka fita daga kasar kano, suka bi ta wani gari mai suna Dingas zuwa Damagaran, suka kalli hanyar Tunis, suka shiga cikin sahara har zuwa Wani gari mai nisan gaske dake cikin sahara a yankin Libya, sunansa Murzuk, daga nan suka dangana da birnin Turawa a bakin babban tekun bahar Rum, suka shiga manyan jiragen ruwa, suka koma kasar su ta girka. Waɗannan sune turawan farko da suka soma zuwa kano.

HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA WACCE BA MUSULMA BA :

HUKUNCIN WANDA YAYI ZINA DA WACCE BA MUSULMA BA :
TAMBAYA TA 2588
*******************
Assalamu Alaikum. Malam mun gode Allah saka da alheri da abunda kake mana.
Mallam nine nayi NYSC na a Jos plateau state Mallam sai na hadu da wata yer christan mallam sai shaidan ya shiga tsakaninmu har mukayi zina sai tazo tayi aure mallam da tayi aure sai muka sake saduwa har muka kwana agidana amma kafun na kwana da ita bayan aurentan sai abokina yace mun tunda ita christan ce ba komi zayyu na kwana da ita sai na sadu da ita da aurenta mallam yanzu mene hukunci na mallam.
mallam ina cikin matsala ayi hakuri agaya mun naji hukunci na nagode ALLAH saka da alheri.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam.
Hukuncinka daidai yake da na kowanne mazinaci. Da farko dai kaci amanar kanka Kuma kaci mutuncin addininka amatsayinka na Musulmi. Sannan kaci amanar hukumar Qasarka wacce ta turaka domin yin bautar Qasa acikin al'ummar wani yankin da ba naka ba, tunda ka aikata irin wannan laifin.
Zinar da ka aikata da ita kafin aurenta da bayan aurenta duk laifin yana nan akanka. Shi abokin naka da ya baka wannan gurguwar fatawar, shin mecece hujjarsa acikin shari'ar musulunci?. Kaima kasan bashi da hujjah. Ka biye ma fatawarsa ne bisa son rai. Kuma tabbas Allah zai tambayeku dakai dashi.
Ta hanyar aikata zina ka fitar da kanka daga layin muminan kirki awajen Allah. Domin kuwa ita zina saboda girman laifinta awajen Allah, yana ha'data waje guda ne tare da shirka da kisan kai. Sune laifuka uku mafiya girma a Musulunci.
Allah yana magana acikin Alqur'ani game da siffar bayinsa na kwarai, yace :
"SUNE WADANDA BASU KIRAN WANI ABIN BAUTA TARE DA ALLAH KUMA BASU KASHE WANI RAI WANDA ALLAH YA HARAMTA SAI DAI DA HAKKI, KUMA BASU YIN *ZINA.* WANDA YA AIKATA WANNAN ZAI HADU DA UQUBA (KO KUMA ZA'A JEFASHI ACIKIN WATA RIJIYA ACIKIN JAHANNAMA, MAI SUNA "ATHAM".
"ZA'A NINNINKA MASA AZABA ARANAR ALQIYAMAH, KUMA ZAI DAWWAMA ACIKINSA, ACIKIN HALIN WULAKANTUWA".
Malamai irin su Ikrimah sun ce acikin Jahannama akwai wasu ramuka guda biyu masu suna "Gayyu da Atham" acikinsu ake jefa mazinata da sauran masu biye wa sha'awa anan duniya.
Ibnu Abid dunya ya ruwaito wani hadisi ta hanyar Haitham bn Malik Atta'eey (Allah ya yarda dashi) yace Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "BAYAN SHIRKA BABU WANI ZUNUBI MAFI GIRMA AWAJEN ALLAH FIYE DA MANIYYIN DA MUTUM YA SANYA ACIKIN MAHAIFAR DA BATA HALATTA GARESHI BA".
Don Qarin bayani aduba tafseerin Ibnu Katheer, Suratul Furqan ayah ta 68-70.
Ga kuma hadisin da Bukhary da Muslim ta Tirmidhiy suka ruwaito ta hanyar Sahabbai daban daban, wanda Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace "MAZINACI BA ZAIYI ZINA ALHALI YANA MUMINI BA" (WATO YAYIN DA MAZINACI YAZO ZAI YI ZINA, ANA CIRE MASA IMANI NE DAGA ZUCIYARSA).
Idan laifin zina ya tabbata akan saurayi musulmi, ko kuma yayi furuci da kansa cewa yayi zina, to hukuncinsa shine bulala dari kamar yadda ayar cikin suratun Nur ta bayyana.
Don haka nake yi maka nasihar cewa kaji tsoron Allah ka tuba zuwa gareshi. Shi Allah mai karbar tuban bayinsa ne. Ka nisanci zina da duk abinda ya shafeta. Kaje kayi aure ka runtse idanuwanka daga kallon haram ko aikata haram. Domin akwai ranar da Allah zai tambayi kowacce ga'bar jikinka akan dukkan aikin da ka aikata da ita.
Allah yace "SAI DAI WANDA YA TUBA KUMA YAYI IMANI KUMA YA AIKATA AYYUKA NA KWARAI".
WALLAHU A'ALAM.
kayi sharing domin mafiyawan Matasanmu sun abka cikin wannan balai ko Allah zaisa kaima ta dalilin ka koda mutun dayane ya samu shiriya.

AVICENA

TARIHIN SHAHARARREN MASANI IMAM IBN SINA
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
Cikakken sunan sa shine Abu Ali Al-Husayn Abdullahi Ibn sina. Yana daya daga cikin qasurguman masana a wannan duniyar, ya kuma baiwa Ilimi kachokan gudunmuwa, wanda ya hadar da ilimin addinin islama, ilimin likitanci, ilimin falsafa, ilimin lissafi da dumbin makamantansu.
An haifeshi a watan Agusta na shekar 980AD a wani gari da ake kira Afshana, wanda keda kusanci da babban birnin daular Samanidiyya mai suna Bukhara. Sunan Mahaifiyarsa Setarah, an haifeta a garin bukhara, mahaifinsa kuwa sunan sa Abdullahi, wasu na cewa shine gwamnan afshana a wancan lokaci.
Ibn sina ya tashi cikin ilimi tun yana qanqani. Haqiqa an bayyana cewa gidansu Ibn Sina matattara ce tsakanin masu bada ilimi, da masu daukar darasi. Sannan kuma shi mutum ne mai kaifin hadda. Don haka akace ya samu nasarar haddace littafin Alkur'ani maigirma tun yana dan shekaru goma kachal a duniya.
Daga nan sai ya shiga haddace litattafai na sauran fannonin ilimi. Ya haddace hadisai masu dumbin yawa. Ya kuma haddace waqoqi na hikima irin wadanda larabawa ke rerawa babu adadi. Wasu ma sunce da zarar yaji abu yake haddace shi.
An samu a tarihi cewa, Imam Ibn sina ya fara daukar darasin zama likita tun yana dan shekaru goma sha uku a duniya. Sannan kuma ya kammala haddace tulin littattafan likitancin wancan zamani yana dan shekaru goma sha shidda da haihuwa, watau shekaru uku kenan da fara daukar darasin nasa. Ilimin daya samu a wannan lokacin yasa aka sahale masa fara duba marasa lafiya daban-daban. Kenan muna iya cewa, ibn sina na daya daga cikin likitoci masu quruciya a tarihin duniya.
A wannan lokacin ana fama da yaqe-yaqe. Sarkin bukhara mai suna Nuh Ibn Mansur na fama da maqiya kala-kala, kokarin sa shine ya qarawa wannan daular tasa qarfi da fadin qasa. Ance akwai wani lokaci da bashi da lafiya, sai ya shiga neman qwararren likita. A nan ne ya samu labarin qwarewar ibn sina, nan take kuwa ya aika akazo dashi domin yayi masa magani. Da akayi sa'a kuwa, Ibn sina ya bayar da magani kuma sarki ya samu waraka. Wannan abu saiya daukaka darajar Ibn sina a yankin baki daya.
Daga cikin tagomashin daya samu shine na zamowa babban likitan sarki Nuh ibn Mansur, wanda ance daga bisani Ibn sina ya rinqa samun kudaden da yake taimakon mahaifin sa ma a wurinsa. Sannan kuma an sahale masa shiga babbar Ma'ajiyar adana litattafai ta qasar Bukhara. Wanda hakan, dai-dai yake da bashi lasisin qara fadada ilimi ta hanyar karanta manyan littattafan ilimi. Koda yake ance babu jimawa dakin adana littattafan ya qone da wuta, abinda ya janyo wasu maqiyan Ibn sina suka zargeshi da qona wajen domin wai kada asan inda yake samo ilimansa.
To. Allah dai shi yasan gaibu. Amma a kwana a tashi, sai lamura suka sauyawa ibn sina. Na farko dai mahaifinsa kuma abin qaunarsa ya rasu, na biyu kuma sojojin turkiya sun cinye daular samanidiyya da yaqi. Wannan yasa Ibn sina barin gari tare da shiga fagafniya, yau yana wancan gari, gobe yana wani. Yana zaga garuruwa yana aiwatar da sana'ar sa ta likitanci, yana kuma karantar da dalibai ilimin falsafa dana warkar da marasa lafiya.
Ance a irin haka sai daya zagaya garuruwan Ganganji, khwarazm, Rayy, Hamadan da Isfahan. A garin hamadan ne akace sarkin garin mai suna shams al Dawlah ya nada shi bafadensa kuma likitan sa, amma daga bisani aka kai masa gulmar cewa ibn sina tsohon bafaden Nuh ibn mansur ne wanda yake maqiyi ne a gareshi, sai kawai ya koreshi daga garin.
Sai dai ance Ibn sina bai bar garin hamdan ba, asali ma boyewa yayi a gidan wani mai bada magunguna saboda a lokacin yana kan ganiyar rubutun littafin kitabusshifa da qanun fid dibbi, littattafan da har yau ake amfani dasu a fannin likitanci. Babu jimawa ibn sina ya aikawa sarkin isfahan takarda, yana neman izinin zama a garinsa, sarkin da yake abokin gava ne ga Sarki Shams ad daulah na hamdan. Amma ance cikin rashin sa'a sarkin hamdan ya samu wannan labari, ya kuma samu labarin maboyar ibn sina. Don haka ya bada umarnin a kameshi a daure a kurkuku.
Allah cikin ikonsa, ibn sina bai wanzu cikin kurkukun ba akace yayi bad-da-bami da shigar sufaye, ya gudu daga kurkukun, inda ya tsallaka zuwa garin Isfahan. A wannan garin ne kuma ya samu nutsuwa tare da karimci, harma ya cigaba da rubuce-rubucen sa.
Masana tarihi sun ce Iman ibn sina ya rubuta littattafai na ilimi kimanin guda 450 a tsawon rayuwarsa. Amma guda 240 ne kachal suka kubuta, ragowar sun salwanta. Daga cikin wadanda suka tsiran kuma, ance littattafai 150 sun qunshi ilimin likitanci ne, sauran 90 din kuwa suna dauke da iliman lissafi, dabara, kimiyyar sararin samaniya, luggar larabci, falsafa, kide-kide da sauransu.
Falsafar Ibn sina jajirtatta ce wajen nunawa duniya wanzuwa da buwayar Allah madaukakin sarki. Duk da dai bayan rasuwar sa, Imam Ghazali ya nazarci littattafan falsafar tasa, ya kuma samar da ilimin falsafar sa wanda yake sabanin na ibn sina. Ance ma ko alokacin rayuwar ibn sina, ya rinqa haduwa da sabanin fahimta daga manyan malaman musulunci na lokacin, tunda ance a wajajen shekara ta 1022, ibn sina ya rinqa amsar takardun tambayoyi na qalubale daga masanin lissafi da falsafa na musulunci mai suna Imam Al-Biruni.
Amma dai, a fannin likitanci, Allah ya hore masa ilimi. Wanda takai ga bashi da tamka aduk duniya a wancan lokaci. Ance yana da matuqar hikima wajen gane cuta da warkar da maralafiya. Shine ma aka taba ruwaito wata qissa tasa mai cewa "wata rana yariman farisa bashi da lafiya, cutar damuwa ta kamashi. Har ya fita daga hankalinsa, yana fadawa mutane cewa shi saniya ne, azo da wuqa a yankashi aci nama mai dadi. Yana kuka 'mooo, mooo, mooo' kamar na shanu. Sai sarkin farisa ya aikawa Ibn sina yazo yayi masa magani. Ance tun kafin yazo ya aiko a sanar da marar lafiyar cewa Ibn sina mahauci ne, zaizo kuma da wuqa ya yanka shi, don haka ya kwantar da hankalinsa. Ai kuwa yarima dajin haka sai murna, ya shiga zaquwar isowar Ibn sina.
A ranar da ibn sina ya qaraso, sai ya zare wuqa, ya wasata a qasa, sannan ya rinqa cewa 'ina saniyar take? Ga mai yankata ya qaraso' sai ya yarima ya rinqa gurnanin shanu 'mooo, moooo, mooo' da qarfi domin ya sanar da Ibn sina inda yake kwance.
Ibn sina yana zuwa wurin yariman, sai ya taba shi sannan yace ' kai! Ai kuwa wannan saniyar bata shirya a yankata ba. Idan tana son yanka, dole sai taci abinci. Tayi qiba, ta kuma sha magani'. Cikin zumudi yarima ya rinqa karbar abinci da magani, har daga bisani hankalinsa ya dawo, lafiyarsa kuma ta inganta. (Littafin The Art of Talking cure na Sadiq Tukur Gwarzo ya tattaro wadannan hikimomi ga jami'an lafiya).
A qarshen rayuwar Ibn Sina, ance dakarun Sarkin Isfahan sun samu nasarar karbe iko da garin Hamdan, don haka ibn sina yayi niyyar koma wa garin da zama, amma sai ya hadu da matsanancin ciwon ciki, daqyar ya qarasa hamdan. Wasu sunce guba aka zuba masa a abinci, wasu kuma sun tafi akan lalura ce ta ajali.
Koma dai ya abin yake, ibn Sina yayi hasashen mutuwarsa alokacin, don haka yaqi shan magani, ya koma ga Allah. Ance abokansa sun rinqa yi masa nasiha ta yabi a sannu yayi magani, amma sai ya nusar dasu ilimin sa na ruhi, gangar jiki da mutuwa. Saboda a iya abin daya sani, ya gamsu Da cewa idan jiki yayi rauni, tilas ruhi ke barin gangar jiki don komawa ga duniyar ruhina, abinda ke sanadiyar Rasuwar dan adam. Har ma yake ce musu "Nafi qaunar gajeriyar rayuwa mai fadi akan siririyar rayuwa mai tsayi"
A qarshe dai, Ibn Sina ya rarraba dukiyar sa ga matalauta, ya 'yantar da bayinsa, sannan ya shiga tilawar Alqur'ani dare da rana, yana saukewa duk bayan kwana uku, har lokacin rasuwarsa a watan Ramadan na shekarar 1037.
Ibn Sina shahararren masani ne, mai koyarwa don Allah. Rashin sa ya jefa duniya cikin duhu, donma Allah ya taimaka ya rubuta wasu daga cikin ilimansa. Alokacin rayuwarsa, ana masa laqabi da Bu Ali sina, Sharaf Al mulk, Hujjatul Haqq da kuma Sheikul Ra'iyss.
Ga kadan daga littattafan daya rubuta;
1. Mi'iyar Al'Aaaqd Ibn sina
2. Risala fi ibtal ahkamul Nujoom
3. Hikmat Al-mashriqiyya
4. Sirat al shiykh Ra'is
5. Al isharat wa Al- Tanbihat
6. Danishnama'I Ala'I
7. Risala fi Sirril qadar
8. Kitab Al najat
9. Hayy Ibn yaqdhan
Da sausansu.
Da fatan Allah ya gafarta masa. Amin

ABACHA

KO KUNSAN ATTAJIRI MAIGIDA MUHAMMADU ABACHA?

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Shine Muhammadu Abacha ɗan muhammadu Sani ɗan Muhammadu, an haife shi shekarar 1905 a garin Maiwa ta Kukawar jihar Borno.
A Maiwa yayi karatun alkurani, daga nan ya soma kasuwancin shanu tun yana matsahins, inda yake kawo shanu daga garin zuwa kano da wasu garuruwa, daga bisani ya komo kano da zama.
A gidan Bature Mai Amburzin ya soma sauka a kano, wanda yake auren 'yar uwarsa zara, daga bisani ya koma unguwar Sabon gari, a wani layi da har yau ake kira layin Abacha. sannan kuma babu jimawa sai ya sayi gidansa na kansa a layin Ibrahim Tawo.
Bisa gudummuwar Maigida Muhammadu Abacha kungiyar 'Yankasuwar Arewa (Nothern Traders Association) ta kafu, kuma shine shugabanta na farko.
Maigida Muhammadu Abacha ya samu damar zamowa zaɓaɓɓen wakili (councillor) a shekarar 1950. Ance ahi mai farin jamaa ne anan sabon gari saboda halayyarsa ta korki. Da taimakonsu kuma aka bunkasa kasuwannin dake birnin kano tare da gabatar da wasu manyan aiyuka.
A shekara ta 1963 ne Maigida Muhammadu Abacha ya kara zama zaɓaɓɓen wakili a majalisar arewa dake kaduna. Kasancewar sa ɗan kasuwa, ance yayi aiki tukuru wajen kwatowa yankasuwa yanci a gwamnatance, haka kuma bisa gudunmuwarsa attajirai irinsu Alhaji Dangote da Alhaji Maude Tobacco da wasunsu suka soma hurɗa kai tsaye da kamfanin Nigerian Tobacco Company.
Maigida Muhammadu abacha na ɗaya daga cikin attajiran da suka taimaka aka sabunta tare da faɗaɗa babban masallacin juma'a na kano a shekarar 1954.
Ance taimakon marasa karfi aikin sane, sannan mutum neshi wanda baya son zalunci.
A karshe Ya rasu ranar talata 6 ga watan mayun shekarar 1980. Anyi janaizar sa kuma tare da ɗumbin jama'a.
Daga cikin 'ya'yansane Tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya fito, amma baya dashi yana da 'ya'ya kimanin sha uku, misalinsu Alhaji Mustafa, Alhaji Nangana, Hajiya Titi, Hajiya Fanta, Alh Abdul da wasunsu.
Da fatan Allah ya gafarta masa amin.

ASALIN KALMAR HAUSA

ASALIN INDA KALMAR 'HAUSA' TA FITO.
(Tsakure daga Muk'alar Nazarin Tarihin Hausa)

Sadiq Tukur Gwarzo

Hakika, sanin inda kalmar hausa ta samo asali abin bukata ne a garemu, duba da yadda muke da kauna gami da soyuwar son jin tarihi mafi gaskiya na wannan harshe namu.
Idan wasu sunce asalin kalmar 'Bahaushe' wadda ake lakabawa wanda duk ya fito daga masu yara harshen Hausa, ta zone daga kalmar 'Baushe', ma'anarta kuma mafarauci, to sai muce ita kalmar hausa kuma daga ina ta samo tushiya?
Kalmar Hausa ance bakuwa ce, wai daga baya tazo. Ance ma masanin tarihi Leo Africanus ya tabbatar da cewa a zuwansa Katsina da Kano a karni na sha biyar, baiji ana faɗin sunan hausa ba, kuma da yaren gobiranci yaji ana magana.
Haka kuma manazartan littafin nan mai ɗauke da tarihin kano mai suna 'Kano chronicle' sun tabbatar da cewa tun daga zamanin Bagauda har zuwa kan Abdullahi Burja, ba'a amfani da kalmar hausa. Sai a wuraren karni na sha biyar, lokacin ɗansa Yakubu aka soma jinta
Tabbas, hakan na iya zama gaskiya, sai dai akwai-ja a maganar yaren gobiranci da akace Leo Africanus ya tarar ana yarawa a kadar hausa.
Domin masu bada tarihin Gobirawa sunce asali daga misira suke, yaki ya korosu, suka rinka sauka da tashi a wurare mabanbanta, sai a karni na sha biyar suka riski birnin Lalle da Gwararramu. Kunga kenan a wancan lokacin (karni na shabiyar) basu iso inda kasar hausa take ba a yanzu.
Sannan kuma a wancan lokacin, wasu littattafai sun bada tabbacin wanzuwar wasu kabilu a wannan yanki namu. Misali, kabilun Maguzawa, Katukawa, Gazargawa, Tokarawa, Damarguzawa da sauransu.
Hakan na iya nufin Kabilar hausa mai yara yaren hausa itama ta wanzu amma dai bada Hausa ake kiranta ba, kuma sai daga bisani ta bunkasa tare da haɗiye ɗaukacin kabilun dake makwabtaka da ita.
Amma dai ga binda wasu masana suka faɗa dangane da asalin kalmar hausa:-
- Mr C.R Niven (1971) cewa yayi: Hausa daga buzaye ta fito, domin sunan da ake kiran mutanen dake zaune a arewacin kogin kwara kenan.
- Farfesa Skinner (1968) cewa yayi :Hausa daga kalmar Aussa ne na mutanen songhai wadda ke nufin Arewa. Kuma yace akwai daɗaɗɗiyar alaka tsakaninsu ta yadda har hausawa sun aro kalmomi a wurinsu. A cewarsa ma kalmomin Bene da Soro duk nasu ne.
Marigayi Mal Aminu kano cewa yayi hausa daga Kalmar Habsha ne. Domin shi yana ɗaya daga masu cewa asalin hausawa mutanen habasha ne tun lokacin daya riski habashan yagano akwai kamance-ceniyar
al'adu a tsakaninsu da hausawa. A cewarsa 'Habsha' ne asalin sunan, sai aka koma Habsa, sannan daga baya ya dawo Hausa.
Sarkin Ningi Marigayi Alhaji Haruna cewa yayi an samo kalmar Hausa ne daga labarin Bayajidda sa'ar daya kashe macijiya shine sai tsohuwa Ayyana ta rinka ceea 'ai wani mutum ne ya kasheta wanda ya HAU-SA' maimakon tace yahau doki...
Shin menene Ra'ayinku game da Asalin Kalmar ta Hausa???

ZUWAN TURAWA 1

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.

SADIQ TUKUR GWARZO

GABATARWAR
Muhammad Sani Umar
Da
John Hunwick
A wani lokaci a shekarar 1902, wani matashi mai suna Abdullahi ya riski kano daga arewa, ana tsammanin daga Ghadamus yake. Bamu samu labarin komai dangane da dalilin zuwan saba, da kuma danginsa, amma dai wannan labarin daya rubuta na daga madogarar mu dangane da labarin nasa.
Domin acikin labarin ne ya bayyana kansa a matsayin ɗalibi, amma ba'a fuskanci a takamaimen fannin da yake ɗalibtar ba, domin babu wata alama dake nuna yazo kano ɗaukar karatu a gurin masana, amma mun samu labari cewa wasu shekaru da suka shuɗe yayi aikin tafinta ga kawunsa na wajen mahaifi dake zaune a kano, wanda hujjoji sun tabbatar da cewa balaraben Ghadamus ne da kasuwanci ya kawo shi kano.
Abdullahi Al Ghadamasi ya riski kano watanni 8 kafin turawan mulkin mallaka su riski kano, har su cita da yaki a shekarar 1903. Don haka muna iya cewa shi ganau ne ba jiyau ba akan yadda yakin ya kasance.
Haka kuma, bamu samu komai dangane da hakan ba sai a wajajen shekarar 1907, zuwa 1908 sanda Abdullahin ya amsa kiran C.L Temple na neman wanda zai taimaka masa a fannin tafinta masanin Arabi da Hausa. A wannan lokaci C.L Temple na kokarin tafiya hutu ne burtaniya, watakila bayan ya kammala ayyukansa a sokoto kenan a watan janairun 1908.
Koda yake, ance aikin Abdullahi da Temple baiyi tsawo sosai ba sabili da yadda akace an nusar da Temple cewar akwai rashin gaskiya/cushe a aiyukansa na fassara.
Babu Jimawa ne kuma akace Abdullahi Alghadamasi ya shiga aiki da H.R Palmer, wanda a lokacin babban aikinsa shine tattara haraji daga loko da sakunan kasar kano.
Kuma kamar yadda muka fahimta, Palmer yayi mu'amala dashi saɓanin yadda Temple yayi dashi ta hanya mai kyau harma yana yawan godiya gareshi. Kai, muna iya cewa ma babu shakka, Abdullahi ne matashin da Palmer yake nufi da 'matashin balarabe' a farkon littafinsa na sunayen sarakunan kano mai suna 'Kano chronicle' wanda yace ya ɗauka aiki, har kuma yana iya fahimtar larabcin Tripoli dana Ghadamus.
Sannan, Babu takamaimen dalilin daya sanya Abdullahi Alghadamasi ya rubuta wannan tarihi, amma tana ita yiwuwa Palmer ne ya karfafe shi yayi. Haka kuma bamu da takamaimen sanin halin da Abdullahi ya cigaba da kasancewa bayan Palmer ya tafi hutu Burtaniya. Koda yake, ance Palmer yayi nufin tafiya tare dashi Burtaniya ɗinma, amma yayin da suka riski Birnin Ikko, Sai Abdullahi ya karaya, har ya yanke shawarar bazai iya jure doguwar tafiya cikin teku ba.
Don haka, samun wannn tarihi muna iya cewa abu ne mai kyau a garemu, domin mahangan da tarihin ya kalla. Da fari dai, Abdullahi yana cikin kwaryar kano turawa suka zo, don haka ya gani kuma yaji abinda zai iya bada labari akansa.
Sannan kuma tarihin ya kalli kasar hausa daga fuskar turai, tunda yayi aiki da turawan harma turawan sun gyara masa wasu aiyukan nasa.
Yadda Turawa Suka Riski Kano.
Ali ɗan Abdullahi Alfallati (Aliyu Babba Zaki) ne sarkin kano na wannan lokaci, kuma yana kan mulki sai labarin yaki ya zowa wannan gari.
Ali, sarkin wannan gari yana sane da labarin yaki. Amma sai yayi shiru bai yayata ga jama'a ba.
A lokacin da tsoro ya cika masa zuciya, sai ya tattara amintattun sa, sannan yace musu "Kuyi sani yaku jama'a, nayi niyyar yin tafiya zuwa sokoto. Don haka waɗanda duk sukayi biyayya dani suna iya bina wannan tafiya"
Daga nan sai ya shiga tattara jagororin yakinsa, da manyan jarumansa da barori, ya sanar musu da shirinsa na tafiya sokoto domin ziyartar iyaye da kakanninsa. Don haka a iya watanni biyu suka kammala shiri.
Da lokacin tafiya yayi, sai sarki Ali ya kira yaronsa mai lakabin Sarkin Shanu, yace masa "Ya kai sarkin shanu, lokacin tafiya sokoto ziyartar iyaye da kakanni na yayi. Gashi kuma kai zan dankawa kasarnan a hannunka ciki da kewayenta da dukkanin hakimanta. Wannan mukamine dana sanya a hannunka, don haka kayi kokarin rike shi da amana da kuma gaskiya. Kuma na sanar da Ma'aji Usmanu ya tallafeka wajen tsare wannan birni, tare da larabawa mazauna mutanen Tripoli da Ghadamus.
Idan wani abu ya faru abirni, ko makiya suka zo daga ko ina, to ina umartarka kayi aiki da nutsuwa, kuma ka nemi shawarar larabawan nan wajen yanke hukunci.
Bayan nan kuma, sai ya sake kiran Ma'aji Usmanu yayi magana dashi da cewa "Kayi sani ina shirin tafiya sokoto ziyartar iyaye da kakannina. Kuma na sanya kasarnan a hannunka dakai da Sarkin Shanu. Idan wani abu ya auku a birni, ko ka samu labarin zuwan makiya daga ko ina, to kuyi aiki da nutsuwa tare da larabawan nan mazauna birnin nan. Kunga muna da iyali, bayi da tarin dukiya, don haka ku nemi shawarar su don samun sahihiyar mafita, lalle ne suƴ mutane ne masu ingantacciyar fahimta.
Saboda haka kada kayi watsi da ra'ayinsu. Ni yanzu zan tafi. Idan Allah Ubangiji ya tabbatar zan bar gari ranar 4 ga watan shawwal ( shekarar 1320 kenan, dai-dai da 3-1-1903.)
Ita kuwa kofar kansakali. Kada ku rufeta domin tanan zamu rinka sadar da manzanni a tsakanin mu.
Sarkin kuma ya sake shaidawa Sarkin shanu cewa "Kai wakili nane, don haka duk abinda ya faru bayan rabuwar mu ka sanar dani ta hanyar wasika, kuma kada ka bari aike ya tsaya a tsakaninmu daga gareka da ma'aji. Amma lamurorin sharia, sai kubar su a hannun Alkali, ku kuma kuji da abubuwan da suka shafi Sarauta.
Don haka, idan Allah ya dawo damu kano lafiya, muka sameku kunyi aiki da nagarta kun cika umarninmu, to hakika zan saka muku da abinda zai faranta muku zuciya. Ku sani Allah Ta'ala yace 'babu abu mafi kamantuwa da sakayya ga alheri sai alheri' (Q 55:60). Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri amin"

ZUWAN TURAWA 2

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.
Kashi na Biyu
SADIQ TUKUR GWARZO
Bayan anyi haka, sai sarki Kano Ali ya bar kano ranar 4 ga ga watan shawwal tare da tawagarsa, wadda ta kunshi dogaransa, dakarunsa da sauran barorinsa.
Kwana 26 bayan sun bar Kano sai labari ya riski kano cewar turawan yamma sun isa zariya harma sun kwaceta da yaki.
Da fari da suka shigo kano, sun riski wani kauye mai suna Bebeji ne. Sai kuwa suka kori mutanen garin suka kashe shugabansu da ake kira sarkin fulanin Bebeji.
Da labari ya riski sarkin shanu, sai nan take ya sanar wa da Ma'aji Usmanu cewar Turawa fa sun shigo kasar kano, harma sun cinye Bebeji da yaki.
Dajin haka, sai Ma'aji Usmanu ya tashi ɗan aike zuwa ga Larabawan nan mazauna kano, yace yana bukatar ganinsu.
Zuwansu keda wuya, sai ya shiga labarta musu halin da ake ciki na zuwan Turawan Yamma, sannan ya rufe da cewar wacce shawara zaku bamu bisa wannan lamari?
Larabawan nan sai suka ce ka sani ya kai Ma'aji, mu baki ne anan kasar, bamu da abin cewa anan. Kurum dai idan har suka rufar mana da yaki da niyyar kashemu tare da kwace dukiyoyin mu, to hakika muma zamu far musu da yaki daboda faɗin Annabi Muhammad S.A.W cewar duk wanda ya mutu yana kokarin kare dukiyarsa, to yayi mutuwar shahada. Haka kuma duk wanda ya mutu yana kokarin kare kansa daga halaka, shima yayi mutuwar shahada. Iya abinda zamu iya cea kenan.
Ma'aji Usmanu yace ku fahimce ni. Sarkin mu ya bar garin nan kuma ya umarcemu da cewa duk binda ya taso, muyi shawara daku, kuma kada mu tsallake ra'ayinku. Don haka kuji zancena, a yanzu muna zaune daku gari ɗaya, muna neman taimakon kune domin kare garinmu daga makiya.
Sai larabawan nan sukace wa Ma'aji Ka barmu muje gidajenmu tukunna.
Sai kuwa Maaji ya barsu suka tafi.
Da yammaci, sai dukkansu suka hallara kamar haɗuwa ta fari. Ma'aji ya kara nanata musu abinda ya faɗa da farko, sukuwa sai suka amsa masa da cewa "mun amince da duk abinda ubangiji yayi hukunci damu."
Sai Ma'aji yace "to idan Allah ya kaimu gobe muna raye lafiya, inason dukkanku da bayinku ku ɗauki makamai ku taru a bakin ganuwa. Nikuwa zaku sameni a bakin ganuwar Bebeji, don haka sai muga abinda Allah zaiyi."
Sai larabawa suka ce "munji abinda ka faɗa, Allah ya bamu nasara akansu amin."
Daga nan sai Ma'aji Usmanu ya tura da wasika izuwa sokoto, yana mai sanar da Sarkin Kano Alu Babba lamurorin da suka auku bayan barinsa birni.
Kashe gari, ranar talata (koda yake lissafin ranar ya nuna 4 ga shawwal + kwana 26, zai baka 1 gawatan zulka'ada na 1320, kuma ranar jumua ta kama) tun da sassafe wasu larabawan sukayi hawa da bayinsu suka tsaya a gefen ganuwa suna masu ɗauke da makamai.
Babu jimawa sai muka ga wasu mutane da suka fita izuwa Bebeji tare da Ma'aji sun shigo birni a sukwane kuma a gigice. Suna gudu kamar ransu zai fita, kowanne ya nufi gidansa suka shige abinsu.
Koda mutane suka ga haka, sai suka bisu a baya. Bayan ɗan lokaci wasu suka fito kofar gida, shine kuma sai mutane ke tambayarsu abinda ya faru. Shine sai suka ce hakika yau munga abinda zai fitar da zomo daga raminsa.
Mutane sukace bamu gane ba, me kuka gani kenan?
Mutanen nan "sukace munga kiristoci turawan yamma waɗanda zasu fitar damu daga garinmu. Suna ɗauke da madafu da ɗakaru masu yawan gaske. Lallai mun shaida waɗannan 'yan ta'adda suna nufowa ganuwar mu."
Kafin kace haka, sai muka fara jiyo kararrakin bindigogi, ana harba wata babbar bindiga da ake kira mai ruwa.
Harbinsu na farko suka karya kofar birni. Da suka harba na biyu kuwa sai da gidan sarkin kofa ya rushe. Harsashin yayi fata-fata dashi kansa sarkin kofar, ya faɗi matacce.
Koda larabawa suka ga haka, sai suka shiga cewa Ya Ubangiji Allah ka tsaremu daga sharrin wannan rana. Madalla da ubangijinmu mai tsarewa.
Daga nan fa sai suka rarrabu, kowannensu ya nufi gidansa ya shige, suka kulle kofofinsu, sannan suka haye bisa saman sorayen gidajen nasu.
Jim kaɗan da faruwar haka, sai turawa suka shigo birnin kano.
Suka shigo dasu da sojojinsu. Sannan kai tsaye suka nufi kofar fada. Suka shiga gidan ta kofar kudu. Jagoransu wani bature ne da ake kira Mai kwagiri.
Da shigarsu sai suka hangi wani mutum a tsaye da takobi zare a hannunsa. Su basu san kowanene ba, amma nan take baturen nan mai kwagiri ya harbeshi da bindigarsa, mutumin ya faɗi matacce. Kai kace tun jiya ya mutu. Ashe kuwa sarkin shanu ne wanda sarki Ali ya baiwa ajiyar gari.
Turawa fa suka rinka kutsawa cikin fadar nan tare da sojojinsu, da alamar akwai abinda suke nema amma basu same shiba. Domin babu abinda suka taras sai yara kananu da mata. A Gidan kuwa babu abinda kakeji sai koke-koke..
A wannan fada, turawa suka kafa dandalinsu.